← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 99

Sashe 8

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kinsan yadda Mummy take k'aunar yarinyar Nan kuwa?To bari kiji zata iya 'batawa dani akan yarinyar nan,don ba k'aramin son ta takeyi ba wallahi,ke ba ma ita ba hatta Dady da Mufida suna matakar son ta nida Asiya ce kawai bamu k'aunarta don ma yanzun Asiya bata k'asar tana can kasar Turkey tana karatu."
Shiru tayi tana sauraron sa kafin daga bisani tace,
"To ya akayi tazo gidan?"
Muhdeen ya ce
"Mummy ce zata fita unguwa Direbanta yad'an kad'e ta, mummy ta bita gidan su a bayan layin mu daga nan dai ta janyo yariyar a jikin ta,da taso iyayen yarinyar su bata ita taci gaba da zama a hannunta gaba d'aya,so sai iyayen suka ce a'a ita kad'ai Allah ya basu bazasu iya rabuwa da ita ba.amma fa kwana ne kad'ai batayi a gidan amma nan take ko wane lokaci."
Juyawa yayi yana kallonta kafin ya maida hankain sa Kan tukyin da yakeyi sannan ya ce,
"Wai me yasa kika damu da sanin ko wace ce it's?"
Girgiza Kai tayi tare da cewa ,
"Bakomai ,kawai dai na tambayar ne dan naganta kuma bansan ta cikin 'yan gidan kuba."
Daga ita har shi ba wanda ya cewa kowa komai har suka karasa gidan su Sumayya sallam su kayi inda ya shaida Mata gobe zai shigo.sannan yaja motar
yabar gidan
Ranar monaday da misalin karfe tara na safe Yana zaune a office din sa yana duba mara sa lapiya, yayin da yake ma wani dattijo tambayoyi yana bashi amsa shi kuma yana rubutu a file d'in da ke gaban sa ne jabeer ne ya turo kofar office din ya shigo,don dama shi kadai ne yake shigo masa office Kai tsaye.zama yayi Kan sofa din dake cikin office din ya zauna,bayan ya sallami dattijon tare da sanar dashi inda zaije ya mik'a file din.

Karasowa yayi ya zauna kusa da Jabir tare da mik'awa Jabeer hannu
Murmushi jabeer yayi ya ce
"Angon Sumayya mai jiran gado, har ka Fara kamshin angonci tun yanzun."
Kallon shi Muhdeen yayi tare da cewa
"Ai kallon ka kawai nakeyi duk yadda muke dakai banida aminin da ya wuce ka kuma dan uwa a gare Ni dan wan mahaifina amma ace tunda sumayya suka dawo garin nan baka taba zuwa kun gaisa ba har tambayar ka tayi."
Rik'e baki Jabber yayi yana dariya yace afuwan aboki yau zamuje tare inasha Allah.
yauwa na manta ban fad'a maka ba wannan rigimammitar tsohuwar na kira ta jiya tana ta zagin ka ashe dama baka kiranta ka gaishe ta?tana matsayin mahaifiyar Dadyn ka?"
Tabe baki baki Muhdeen yayi tare da cewa
"Mahifiyar Dady kace ai ba mahifiya ta ba,matar da duk mutum yayi waya da ita sai ta 'bata masa Rai shiyasa na daina Kiran ta."
Dariya yayi tare da cewa
"Ai ciwon Kai Kam yaxun zaka Fara don tace jibi tace zata so,kuma kasan idan tazo gidan Dadyn ka take sauka."
Had'e fuska yayi tare da cewa
"Dama duk cikin jikokin ta tafi saka mani ido wallahi."
Jabeer ne yace
"Ko kuma tafi kowa kaunar ka ba don wallahi tafi sonka fiye da kowa a cikin jikokin ta."
Fira suka 'dana taba kafin ya tashi ya koma office din sa.

Bayan kwana biyu kuwa sai
Gwaggo ta baro garin Kontagora ta iso garin Minna tun ana bikin Muhdeen da Sumayya saura wata biyu tazo.murna a wurin Mummy da Mufida ba'a magana.

Waya ta d'auka ta Kira mu6hdeen tace kada ya dawo gidan nan ba tare da yazo mata da amaryar da zai aura yau d'innan idan ba haka ba ko ruwa bazata bari yasha a gidan nan ba.

Sanin rigimamar Gwaggo ne yasa baida wani zabi dole ya Kira Sumayya yace ta shirya zaizo ya dauke ta ta gaishe da kakar sa da tazo.

Misalin karfe biyar na yamma Mummy ce zaune a falo yayin da Mufida ke zaune Kan carpet,Gwaggo ta shiga ta watsa ruwa.

INTEESAR ce ta turo k'ofar karamin gate din gidan ta shigo gaisawa tayi da Mallam Ibrahim mai gadi sannan ta shige cikin gidan.

Bakin ta d'auke da sallama ta shiga falon durk'usawa tayi har k'asa ta gaida Mummy sannan ta kalli Mufida ta ce,
"Yauwa Mufida Ina Gwaggon take?kinsan ban ta'ba ganin ta ba,wallahi na k'osa na ganta ba."
Mummy ce tayi murmushi tare da cewa,
"Karki damu Inteesar yanzun zata fito Zaki ganta"
Dai-dai lokacin ne Muhdeen ya shigo da sallama sumayya na biye dashi a baya suka karaso yayin da Muhdeen ya zauna a k'asan carpet ganin Mummy akan kujera, s6umayya ta zauna kan 1 seater dake facing din mummy gaida mummy tayi ba yabo ba fallasa ta amsa Mata,
Mufida ta nufi d'akin da Gwaggon take sauka ta sanar da ita cewa Muhdeen ya shigo da matar da zai aura.

Da sauri Gwaggo ta nufi falon 'dan kwalinta a hannun ta take fad'in
"Ina kishiyar tawa take inga da mai tafini da ya tsallake ya tafi wurin ta"
Idon ta ne ya sauka akan Inteesar dake zaune a carpet Muhdeen na gefen ta 'dan nesa da ita.

Washe baki tayi tana fad'in
" masha Allah wannan had'in yayi ai daga ganin zaren ma kalan yadin ne,gata kyakkyawa kamar shi jikan nawa."
Dan Bata lura da Sumayya dake zaune Kan kujera ba.durkusawa tayi ta kamo ha'bar Inteesar tana cewa
"Kai kyakkywar kishiya ta dole nayi kishi dake."
Gaba d6aya falon tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah.Sumayya Kam ta cika da bak'in ciki tayi fam,idon ta ne yakai kan Sumayya dake Kan kujera wani kallo shek'ek'e take mata sannan ta nuna Sumayya tabce,
"Ina kuka samo wannan Mai zubin karuwai?"
Muhdeen ne ya ce
"Haba Gwaggon ki dinga tsayawa kina tabbatar da abu kafin ki fad'a mana,matar da zan aura kike cewa karuwa?"
Ware idanun ta tayi tare da nuna sumayya sannan tace,
"Kana nufin wannan zaka kawo a cikin zuri'ar mu? a matsayin uwar 'ya'yan ka?Haba Muhammadu to nikam bada yawu na ba."
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to ku gafarceni ba da niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.

Page1
Cikin daurewar fuska ya kalli Gwaggo ya ce,
"To ni ita na gani nake so, kuma bazan canza ra'ay ina akanta ba".

Hannu Gwaggo tasa ta rike baki cikin mamaki ta ce,
"Allah buwayi Gagara misali, oh ni yau naga abunda ya ishe ni, to bari ka ji ko Uban da ya haife ka bai isa idan nace a'a yace mun Eh ba, ballantana kai dansa".

Murmushi Mai cike da takaici Muhdeen yayi sannan ya kalli Gwaggo yace,
"To ai Dama Dady bazai tsallake maganar ki ba saboda ke kika haifesa, "Amma ni kama bak...

Tsawar da Mummy ta daka masa ne yasa ya fasa karasa abunda yayi niyyar fada.

Cikin bacin Rai Mummy tace,
"Kanka daya kuwa?

Gwaggon kake fadawa haka, wani irin rashin hankali ne wannan?"
Gwaggo ce tace
"Kyale shi Fatima idan bai ci mun mutunci ba ai bai isa ba".

Sai kuma ta fashe da kuka tana murzar idanu da d'an kwalinta tana fadin
"Yanzu D'an nan ni za ka yi wa cin mutunci a bainar jama'a?

Ni ka wulakanta ka nunawa duniya ban isa da kai ba?

Dan na hana ka bai kamata ka aure karuwa ba ko?"
Muhdeen ne a hasale ya bude baki zai yi magana, Mummy ce ta dakatar dashi ta hanyar masa gargadi da idanunta.

Shiru sukayi suna kallon Gwaggon, don inda sabo sun saba da Halin tsohuwar da rigimarta, shima Muhdeen din Abunda ya Kara 'bata masa rai shine kalmar karuwar da ta kira matar da zai aura dashi.

Ita kanta Sumayya hawayen da ya cika mata ido ne ya samu nasarar zubowa, ranta ya baci matuka tsanar tsohuwar ce tab a cikin zuciyarta.

Muhdeen ya je har gida ya dauko ta don tazo ta gaisar da kakarsa amma tazo gaida tsohuwar amma sakayyar da tayi mata kenan kalmar karuwa kawai take ta maimaitawa a cikin zuciyarta.

Mikewa tayi aguje ta nufi kofar fita, Muhdeen ne ya bi bayanta yana kwala mata kira,
"Sumayya!

Sumayya!!

Sumayya!!!"
Amma Ina ko kallonsa batayi ba ta ta ci gaba da gudu dai-dai takai bakin gate ne tana kokarin fita ya samu nasarar rike hannunta, kokarin kwatar hannun tayi ta kasa, hakan yasa ta fashe masa da kuka tana fadin
"Ka sake ni na tafi dama ka kawo ni nan ne dan a tozartani? kukanta ne ya tsananta, bai san lokacin da ya janyota jikinsa ya rungume ta yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, Don ya rasa abunda zai ce.

Dai-dai lokacin ne Gwaggo ta fito daga kofar falon tana fadin "ba dai bin ta yay...

Turus ta tsaya ganin Muhdeen rungume da Sumayya.

Salati ta saka tana tafa hannu cikin Al'ajabi tace
"Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun ni 'yar Sulaiman yau naga tashin hankali ganin ido na, lallai iskancin ku ya girma, rashin kunyar ku ta balaga, to wallahi ba a gidan d'ana zaku janyo masa masifa da bala'i da ransa ba, ban san yaushe Muhammadu ya lalace haka ba Amma zanyi maganin ka wannan yarinyar mai kai kamar na jemage ba matar aurenka ba ce".

Muhdeen ya janye ta daga jikin sa ganin tayi shiru ta daina kukar sai hawaye dake bin idanunta, dama ita bata raina abun kuka, hannunta ya rike suka nufi wurin mota da kansa ya bude mata motar ta shiga, Shima ya zagaya ya shiga ya tayar da motar Malam Ibrahim dake kallonsu ne ya wangale masa gate din ya fice.

Gwaggo dake sake da baki tana kallon ikon Allah tasa kai ta shiga falon yadda tabar su haka ta same su, zama tayi tana kallon Inteesar da tayi shiru tana tunani.
Chapter 8 · 0% Book details