← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 99

Sashe 47

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fitowa toilet d'in k'amshin turarenta ne ya sa ya Kai dubansa ga wurin,ya ganta har ta fara barci, ta'be baki yayi tare da goge ruwan jikinsa singileti da gajeren wando ya saka ya fesa turare,hawa saman gadonsa ya yi ya zauna tare da d'aukar wayarsa, Sumayya ya kira bugu biyu ta d'aga tare cewa
"Baby da naji shiru baka kira ni ba na d'auka ko ka yi barci ne."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Ina zan iya barci banji muryarki ba,ai sai na kasa barci,ya su Mum da Dad suke?"
Murmushi ta yi tare da cewa
"Suna lafiya"
Nan dai suka cigaba fira har tsawon mintuna arba'in, Inteesar da ke barci ta yi wani juyi sai Hijabin da ke jikinta ya tattare ya koma gefe d'aya,lokacin da idanunsa ya sauka akanta ya yi arba da kyayyawun surar jikinta mai d'aukar hankali,rigar barcin da ke jikinta shara -shara suke hatta pant d'inta da bra d'inta ana hangowa.

Ido ya kafe ta dasu yana kallonta gaba d'aya tsigar jikinsa tashi suka yi cikin wani irin kasalalliyar murya a sark'e ya ya yi magana ya ce ma Sumayya
"Baby zan aje waya sai da safe."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran tare da aje wayar idanunsa na Kan Inteesar,wani irin azabbaben sha'awar ta ne ke fisgarsa,
Saukowa ya yi daga kan gadon,ya k'araso gare ta kwanciya yayi saman sofan shima duk da wajen ya matse su amma bai damu ba,hannunsa ya zura cikin rigarta yana shafar jikinta,mutsu mutsu ta fara yi sakamakon jin kamar ana shafa jikinta,kuma gashi tana jin iskar numfashinsa akan fuskarta,a hankali ta bud'e idanunta ganinsa ne yasa ta bud'e baki ta niyar ihu amma kafin tana bud'e baki kafin ta yi ihu ya ya kai bakinsa cikin bakinsa cikinta yana tsosan la'b'banta,ganin tak'i sakin la'b'banta ne ya sa ya saki la'b'banta ya Fara kissing d'inta a hankali zuwa wuyanta mutsu mutsun k'watar kanta take amma ta kasancewar rigar barcin mara hannu ce zame rigar ya yi zuwa k'asa,bra d'in ya 'balle ya Kai hannunsa a hankali ya shafa k'irjinta had'i da murza breast d'inta da d'an matsa su,laushi fatarta ne ya zautar da shi gaba d'aya ya fara rikicewa
Wani k'arfi ne ya zo mata ta hankad'eshi ta nufi k'ofar fita.
*WEEKEND BA ZANYI MAKU UPDATE BA*
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, Arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
Page4
Wani k'arfi ne yazo mata ta hanka'deshi ta nufi k'ofar
Cikin sand'a ta shiga d'akinta,maida k'ofar tayi ta rufe,a kasancewar hasken d'akin ba a kashe ya ke ba andai rage haaken ne yasa a hankali ta k'arasa wajen gadon,hayewa ta yi ta matsa can k'arshe a hankali ta ke komai da gudun kada Gwaggo ta farka,kwanciya tayi tare sa yin addu'ar barci.

Ta dad'e kwance barci bai d'auke tabba tana tunanin abubuwanda Muhdeen ya mata, tura baki ta yi tare da sanya hannu ta la'b'banta lokacin da ta tuna yanda ya dinga tsotsan la'b'banta kamar ya samu sweet, ta kuma sa hannunta duka biyu da rungume a k'irjinta lolacin da ta tuna sanda ya 'balle mata bra ya dinga shafa mata k'irjinta
Azuciyar ta dinga cewa Allah ya isarmun,bayan muguntar ma da alamaa ya k'ware a wajen iya iskanci,mugu kawai.

Ita kad'ai ta ke maganar zucinta har barci ya d'auke ta.

A 'bangarensa kuwa tunda ya ga ta fice a d'akin bai iya yuk'urin kamota ba,don gaba d'aya jikinsa ya saki kamar wanda bashida laka a jikinsa,gaba d'aya ya susuce daga ganin halittar yarinyar mai jan jankali,ko Sumayya dai da ya fara ganinta ba kaya a jikinta hankalinsa ba d'aga haka ba,ballantana ya susuce amma yarinyar nan gaba d'aya ta rikita shi,a halin yanzun ji yake ita kawai yake da buk'ata,gashi shiru baiga Gwaggo ta turo ta ba,don ya tabbatar da Gwaggo ta ganta ba abunda zai hana bata dawo masa da ita ba,amma tunda yaji ta ahiru yasan Gwaggo Bata ganta ba ta yi barci,dama tana da nauyin barci ita.

Ta shi yayi ya nufi toilet,ruwa ya sakar ma kansa bayan ya gama watsa ruwan ne ya guge jikinsa ya fito,jallabiya ya saka tare da kwanciya,ya dad'e kwance barci bai d'auke sa ba,da zaran ya rufe ido ba abuda ya ke ganin sai surar jikinta.

A haka dai barci ya d'auke sa,duk mararsa na d'an masa ciwo.

Can cikin dare ma haka ya dinga juyi ga wani irin feeling da ke bijiro masa,gaba d'aya yarinyar ta saka shi cikin wani hali,yana zamansa lafiya Gwaggo ta je ta turo masa ita gaba d'aya ta hanasa sukuni, sha'awar yarinyar kawai ke damunsa.

Sai wajen k'arfe uku ne uku da rabi ne barci 'barawo ya yi awon gaba dashi,bayan ya samu sassauci,ba shi ya farka ba sai k'arfe biyar da rabi,ganin lokacin sallah ya yi ne yasa ya tashi cikin hanzari ya ya watso ruwa tare da d'auro alwala,sharp -sharp ya shirya cikin farin jallabiya ya nufi masallaci,ko ya k'arasa masallaci an idar da raka'a d'aya.

'Bangaren Inteesar kuwa Gwaggo ce ta farka k'arfe hud'u,ganin Inteesar ne kwance tana barci yasa ta saki salati tare da kai mata duka a kafad'arta,farkawa ta yi tare da tashi zaune,kallon Gwaggo ta yi tare da cewa
"Lokacin sallah ya yi ko?"
Dak'uwa Gwaggo ta yiwa Inteesar ta ware yatsunta duka biyar ta nunawa Inteesar tare da cewa
"Ungo naka nan,na ce ungo nan 'yar jakar uba,anya kuwa yarinyar nan kina son kanin annanbin rahama?"
Tura baki ta yi tare da cew
"To me kuma nayi Gwaggo?"
"Uban me yasa kika gudo daga turakar mijinki?"
"Gaskiya ni Gwaggo bazan sake zuwa d'akinsa ba."
Kallon mamaki Gwaggo ta yi mata tare da cewa
"Saboda uban me yasa ba Zaki sake zuwa ba?"
"Wallahi d'an iska jarababbe ne."
Duka Gwaggo takai mata a bakin ta wanda har sai da tayi saurin d'ora hannayenta akan bakin,don ta ji zafin dukan.

"Kul na sake jin wannan maganar daga bakinki ."
Kukan shagwa'ba ta saka tare da cewa
"To nifa ba 'yar iska bace,wallahi Gwaggo baki ga abunda ya dingayi ba,ya bi ya damu mutum da tsotse-tsotse sai sunshina ni yake yi kamar d'an akuya."
Salati Gwaggo ta yi tare da cewa
"La lah ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam, yau ni kulu na ga abunda ya isheni bai ishi Allah ba,to Bari kiji abunda kike Kira iskanci shi aka kawo ki kiyi,nace iskanacin kika zo yi,kuma badi kiji wallahi indai baki fita a idona ba sai nayi maganinki,baki zuwa Islamiyya ne?ko kuma ba'a fad'a maki hakkin miji akan matarsa ba?"
"An fad'a Mana."
"Oho an ma fad'a maku kin sani amma kike take sani?ki gwammaci ki kwana cikin tsinuwar mala'ikun Allah?"
duk tunanin Gwaggo ta d'auka cewa Inteesar da Muhdeen suna mu'amalar auratayya ne gajiya da rashin sabo ya sa Inteesar gudowa ta barshi,don haka ta cigaba da cewa
"Haka Zaki dinga hak'uri da yanayin mijinki,a haka zaki saba kema ki zama jaruma irinsa ki daina gudowa nan kada nima tsinuwar taking ta shafe ni."
Ba tare da ta ce komai ba ta mik'e jin zancen Gwaggo ba na k'are bane, kuma gashi har an tayar da sallah a masallaci,bata tsaya yin wanka ba ta d'auro alwala ta fito,kallonta Gwaggo tayi ta ce,
"Banga kinyi wankan janaba ba,ana sallah da najasa ne?"
Inteesar dai shiru ta yi bata ce komai ba, k'ok'arin d'aukar hijabinta kawai take,sai jin muryar Gwaggo ta sake ji tana cewa
"To ko a can d'akin nasa kika yi wankan tsark?"
Nanma bata ce komai ba,har zata tada sallah sannan ta juyo ta kalli Gwaggo ta ce
"Gwaggo ki tashi fa kiyi sallah lokaci na tafiya."
Daga nan ta tada sallah yayin da Gwaggo ta shiga toilet don d'oro alwala.

Koda ya dawo daga masallaci d'akinsa ya koma ya kwanta ya cigaba da barcinsa.

Bayan Inteesar ta gama azkar da karatun al qur'ani kamar yadda ta saba fara gyaran gidan ta yi sai dai ba kamar na wahalar da Muhdeen ya dinga sata ba,yanzun idan ta gyara falo da d'akinta da toilet sai kitchen,sai kuma falon Sumayya da d'akin Muhdeen,bayan ta kammala gyara ko Ina ne ya rage d'akin Muhdeen,tana ta tsoro da zullumin shiga d'akin tuna abunda ya mata a daren jiya gabanta ne ya shiga fad'uwa tana tsoron shiga har ta kai hannu da zummar bad'e k'ofar sai ta fasa ta juya ta nufi kitchen dan d'aura masu breakfast,
Ruwan shayi ta dafa da yaji kayan k'amshi sai Dankalin turawa da plantain ta soya da k'wai,bayan ta kammala ne ta jera su dinning table sannan ta nufi d'akinta ba kowa a d'akin don Gwaggo ta dawo falo tana kallon T.V, magana ta dingayi a zuciyarta ita kad'ai tana cewa
"Sai dai yau d'akinsa ya zauna hakanan ba gyara, don bazan shiga d'akin ba idan yana ciki,salon ya je yayi mani fyad'e ya cuceni tunda ba k'aunata yake ba,gara idan naje na auri mai sona nakai masa budurcina amma bazan ta'ba bari wani mugu ya rabani da shi lokaci guda ba."
Haka ta yi ta surutanta ita kad'ai,wanka ta shiga bayan ta fito ne ta shafa man shawanta Mai k'amshi na wajen Hajiya Bilkisu mai gyaran Amare,riga da siket ta saka na atamfa ya zauna mata cif a jikinta inda ya k'ara bayyana kyakkyawar surar jikinta da kyawun dirinta.
Chapter 47 · 0% Book details