← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 99

Sashe 45

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A falo suka zauna inda Inteesar ta nufi kitchen don kawowa Gwaggo abun ta'bawa Muhdeen kuma ya k'udiri niyyar cewa bazai ta'ba barin wata k'ofa da zaisa Gwaggo ta gane cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da Inteesar ba,zai dinga nuna mata k'auna da kulawa,zai janyo Inteesar a jikinsa yadda zata sake dashi ta daina jin tsoronsa don burinsa ya cika.

Inteesar ce ta kawowa Gwaggo ruwa da lemu a faranti,kallonta Gwaggo ta yi tare da cewa
"Sannu da k'ok'ari 'yar albarka Allah ya nuna mani 'ya'yanku."
Sallama suka ji daga bakin k'ofar shigowa, Muhdeen ne ya amsa tare da basu izinin shigowa, Jabeer ne da Salisu da Bilyaminu sai kuma Baahir.

"Jabiru kune a tafe?

Dariy ya yi tare da cewa
"Eh mune Gwaggo, dama kina nan ne?"
"Yanzun nan nazo kuma wata d'aya zan masu a gidan nan,duk da cewar shi Muhammadu bak'in ciki yake da zuwa na ban damu ba,duk tsiyarsa Bai isa ya koreni ba tunda 'yar albarka na maraba da ganina."
Inteesar dama tunda taji muryar maza zasu shigo ne tayi saurin ta nufi d'akinta,sai gata da hijabi har k'asa,Su Salisu ne suka gaida Gwaggo suka zazzauna a kujera, Muhdeen ya dinga mi'ka masu hannu d'aya bayan d'aya suna gaisawa,Bashir ne k'arshe lokacin da Muhdeen ke mik'a ma Bashir hannu baima san yana mik'o masa hannun ba,gaba d'aya ya shagala da kallon Inteesar ko k'yaftawa baya yi, Muhdeen ya kalle shi ya kalli Inteesar da bata ma San yana kallonta ba hankalinta na wurin Gwaggo da take tambayarta su Mufida,had'e fuska ya yi tare da kallon Inteesar cikin bada umarni ya ce,
"Inteesar ki shiga d'aki"
Da sauri ta kalle shi tana kokonton sunanta da ya kira,don tunda take bata ta'ba Jin ya Kira ta da sunanta ba sai dai ya ce ke wata rana ma mayya yake kiranta amma yau karon farko ta ji ya kirata da sunanta da mahaifinta ya saka mata,Bata gama tuna ni ba ta jiyo ya maimata cewa ta shiga d'aki,take ta juya ta koma d'akinta,kowa dake falon zuba masa ido ya yi shi kuma fuskar nan tasa a had'e,yana tuna lokacin bikinsa da Sumayya ranar da Bashir ya fara ganin Inteesar yana ta yaba kyawun surarta da har yana kiranta da zazzafar yarinya wai duk neman matan banza da yake bai ta'ba ganin macen da ta mallaki abunda ya ke so komai a jikin mace ba sai Inteesar.

"Bros ya zaka kori amarya ita fa muka zo gani,ko gaisawa ba muyi ba ana muna rowarta."
Dariya sukayi Salisu ta d'aura da cewa
"Nima abunda na gani kenan,lokacin da mukayi auren mu ai da yazo zama ya yi suka gaisa da amaren mu,amma kunga shi rowar ta ya ke."
"Muhammadu mutumce fa ita ba akuya ba ce da zaka rufe a d'aki,wannan ai zalinci ne wallahi bani so takura,haka kawai zaka takurawa 'yar mutane."
Bai ko kalleta ba ballantana tasa ran zai amsa mata,
"Bisimillah kuzo muci abinci"
Jabeer ya tintsire da dariya tuna ranar da suka zo cin girkin amarya Sumayya,Salisu da Bilyaminu ma ta ya shi dariyar sukayi don suma abunda suka tuna kenan.

"Nidai wallahi tsoron cin girkin gidanka nake ranar farko da mukazo cin girkin amarya ba Wanda ya iya had'iye ko cokali d'aya gaba d'aya saboda k'warewar Hajiya Sumayya a iya girki."
Gaba d'ayansu suka sake dariya,hakan ya sosa ran Muhdeen matuk'a don haka ya zauna ya fita batunsu ko kallonsu Bai sake ba.

"Koda yake Sumayya daban Inteesar ma daban ,don Sumayya bata iya girki ba ba yana nufin cewa Inteesar bata iya ba,bari mu tashi dai bakinmu ya gaya Mana."
Gwaggo ta zubawa Jabeer idanu tana cewa
"Jabiru Wai kana nufin wannan yarinyar bata iya girki ba?"
Dariya ya yi don dama ya it's tsokana
"Ai Gwaggo idan ana sallah ba'a magana wato ranar da tayi muna girki wallahi gaba d'aya kamar an wanke kai,ni wani d'aci naji na ma kasa tantance want irin test abincin keyi gashi bai dahu ba,dukanmu ba Wanda ya iya cin ko cokali d'aya,na ce wannan girkin na masoya ne."
Ta'be baki Gwaggo ta yi tare da cewa
"Idan mace bata iya girki ba ki ai ba mace bace,dama sai da na guje masa auren ta amma bai saurare ni ba."
"Ya isa hakanan kun zauna Kuna ta cin mutuncin mata ta akan me?"
Mi'kewa Jabeer ya yi tare da nufar dinning area.

"To ina amarya ta zo ta zuba mana muji ya nata k'warewar take."
"Ba zata zo ba kowa ya zubawa kansa ya ci tunda ba cikinta zaku zuba ba."
Daga nan ya juya ya nufi d'akin Inteesar,tura k'ofar ya yi inda ya samu tana waya a cikin zancen nata ne ya ji tana cewa
"Haba Usman ka daina fad'in haka Usman wallahi nima ina cikin damuwa na yi missing d'inka sosai."
Gaban Muhdeen ne ta fad'i cikin tashin hankali ya furta
"What?"
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kase auren wawa.

Page4
"Haba Usman ka daina fad'in haka, Usman wallahi nima ina cikin damuwa, na yi missing d'inka sosai."
Gaban Muhdeen ne ya fad'i cikin tashin hankali ya furta
"What?"
A firgice Inteesar ta juyo ta kalleshi gabanta na tsananta fad'uwa,cikin sanyi da nutsuwa fuskarsa ba yabo ba fallasa,ya k'araso gabanta yayin da ya mik'a mata hannu alamun ta bashi wayar,katse kiran tayi kafin ta bashi wayar kar'ba yayi tare da cewa
"Waye shi?"
Shiru ta yi ba tare da tayi magana ba,ya sake tambayarta da cewa
"Na ce waye Usman?"
Shiru ta yi masa ta kasa cewa komai,zuba mata ido ya yi yana kallonta.

"Soyayya kike da wani k'ato da igiyar aure na akanki?saboda baki San darajar aure da martabarsa ba ko?."
Sanin cewa Gwaggo na cikin gidan kuma matuk'ar Gwaggo na gidan bai isa ya ce zai mata wani abu ba ko ya yi yun'kurin cutar da ita,hakan yasa ta samu k'warin guiwar cigaba da magana.

"Usman masoyi na ne na hak'ika yana k'aunata da kuma burin aure na ya faranta mani rai don yana son farin ciki na."
Ji ya yi zuciyarsa na k'una da jin d'acin kalamanta.

"Shi baisan kina da aure bane ko kuma rashin sanin darajar aure ya sa ya ke waya da ke?"
"Eh baisan na yi aure ba."
"Uban me yasa baki sanar da shi cewar ke matar aure ba ce?"
Ba tare da ta kalle shi ko ta yi shakkarsa ba ta ce,
"Saboda ni ba matar auren ba ce, don wannan zaman da nake ban d'auke shi zaman aure ba,kai da bakinka ka fad'a mani cewar da zarar matarka ta dawo gidan nan ni kuma zaka rabu da ni ba zaka zauna da ni ba,wannan dalilin yasa ban sanar da Usaman cewa ni matar aure ba ce a yanzun,domin zaman jiran matarka ta dawo nake, idan ta dawo ka rabu da ni kamar yadda ka ce sai na je na auri Usman."
Gaba d'aya ransa ya gama 'baci da kalamanta,fita ya yi da wayar a hannunsa Kai tsaye ya nufi d'akinsa ransa a 'bace Gwaggo da ke zaune a falo taga ya fito ransa a 'bace yasa ta gane akwai abunda ya faru,su Jabeer da suke a dinning area basu ganshi ba.

Yana shiga d'akin ya bud'e size durowa ya saka wayar, zuciyarsa na tafarfasa,zama ya yi akan gadon tare da magana shi kad'ai kamar yana fad'awa wani.

"To ni mene ne nawa ne na 'bacin rai haka?to wai ma kishinta nake ko me?idan ina kishinta hakan na nufin sonta na fara? tunda ance kishi ke saka soyayya,kai ina bazai yiwu ba me zaisa naso ta? to wai shin ma ina ruwa na ne da zansawa kaina damuwa?"
Tsuki ya ja tare da ficewa daga d'akin ya nufi dinning area.
Chapter 45 · 0% Book details