← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 99

Sashe 33

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da kike cewa ke matar aure ce ni zaki fad'awa aure?to ki tantabara ce ke ni ba damuwa ta ba ce."
Murd'e hannayanta yayi da d'an k'arfi tare da cewa
" ni kika gama zagi ko? wato nine bak'in mugu ko?"
Kai ta girgiza masa idanunta na zubda hawaye ta ce,
"I'm sorry"
Gajeren murmushi ya yi yana cewa
"Sorry for your self"
Yana rik'e da hannayenta wayarsa ta Fara ruri zaro wayar yayi daga cikin aljihunsa,d'agawa yayi tare da cewa.

"Jabeer ya akayi ne?"
Jabeer yana shirin bud'e baki yayi magana kenan sai yaji muryar Inteesar ta cikin wayarsa tana kuka tana cewa
"Dan Allah yaya Muhdeen kayi hak'uri ka barni haka nan wallahi da zafi,ka tausaya mun haka."
ta saki k'ara lokacin da ya k'ara matse hannayenta.Jabeer kusa daga can cikin wayarsa yake Jin maganar Inteesar.Dariya ya kece dashi sosai har ya zauna daga tsayen da yake, shi a tunaninsa muhdeen sex yake da Inteesar da ya ji tana cewa akwai zafi ya barta hakanan ya ji k'aran da ta saki hakan yasa yakewa Muhdeen dariya.sai da ya tsagaita da dariyar kafin ya fara magana.

"Lallai namiji bashida kunya wato duk zagin yarinyar nan da kake kana cewa kucakar yarinya Allah ya kiyaye ka tsaneta yanzun ta tashi daga kucakar ne?ko kuma k'iyayya har ta juya ta koma soyayya ce?

Hhhhj to kadai bi 'yar mutane a sannu kasan sabon shiga sa..."
Tsuki Muhdeen yayi tare da katse kiran,hannun Inteesar ya saki tare da hankad'ata ta fad'a Kan gadon tana sakin kuka.

Mummy da Mufida ya samu a dinning room suna Breakfast,Sallamar Mummy yayi tare da sanar da ita anjima zai dawo yana son magana da Dady.Nan Mummy ta nemi yayi Breakfast kafin ya tafi amma ya nuna a office zaiyi Breakfast,hakan yasa ta barshi ya tafi hakanan.

Fitarsa kenan sai ga Gwaggo ta fito daga d'akinta,k'arasowa tayi tana fad'in
"ina cikin band'aki sai naji kamar muryar Muhammadu ya shigo d'akina shin ya tafi ko yana nan?"
Mummy ce ta bata amsa
"Yanzun ya fita amma ya ce anjima zai dawo."
Kallon Mufida Gwaggo ta yi tana cewa
"Ya banga 'yar albarka ba?"
Mik'ewa Mufida tayi
"Bari naje yanzun na kirata dama lokacin da naje kiranta na sameta ita da yaya ne a cikin d'akin,yanzu tunda ya fita bari na koma."
Da sallama ta shiga d'akin,jin muryar Mufida ne yasa Inteesar saurin goge hawayenta,d'agowa tayi ta kalli Mufida tana sakar mata murmushi,da mamaki Mufida ta kalli fuskarta.

"Lafiya kike kuwa naga idonki kamar kinyi kuka?"
"Bakomai banyi kuka ba,barcin da na tashi ne yasa idanu na sukayi haka."
Murmushi Mufida tayi tana fad'in
"Tare da ke fa muka tashi barci idonki baiyi haka ba sai yanzun?koda ya ke bazan matsa maki tashi muje muyi Breakfast."
"Yauwa Mufida bari na tambayeki mana ."
"Ina jinki"
"Me yasa aka sauke ni a d'akin nan ne?wallahi banso zama a d'akin nan ba ga mai d'akin ya dawo ya sameni a ciki nifa gasky zan koma d'akinki ko na Gwaggo."
Dariya Mufida yayi tana cewa
"To ai ba inda Zaki zauna bayan nan nan ne yafi dacewa dake."
Tunawa tayi da cewa Kila fa haryanzun ba wanda ya fad'awa Inteesar cewa Muhdeen ne mijinta.Hakan yasa bata sake magana taja hannun Inteesar suka nufi hanyar fita.

Koda suka k'arasa dinning table kallo d'aya Gwaggo tayi mata taga idonta ya yi kama da na wacce ta yi kuka.Haka ma Mummy ta lura da hakan, Gwaggo ce ya fara magana.

"To 'yar albarka lafiya me ya sameki ne kikayi kuka?"
"Banyi kuka ba Gwaggona"
Mummy ce ta zuba mata ido
"Kada kiyi mana k'arya don ba d'abi'arki ba ce k'arya kada ki fara."
Shiru tayi tana nazari,don ita dama duk abunda zai janyowa wani 'bacin rai bata so,hakan yasa ta ce,
"Bakomai"
Kai Mummy ta girgiza
"Kodai da son ya shiga ya 'bata maki raine?idan ya maki abunda ba dai-dai ba ki fad'a mani a matsayina na mahifiyarsa zand'auki mataki aka sa."
Murmushin yak'e tayi
"Ba komai ya sani kuka ba kawai na tuno da Abbana da Umma ne yasa nake kuka"
Kai Gwaggo ta girgiza tana cew,
"Kiyi hak'uri kinji kowa haka akayi mata Umman taki mma haka Mata ."
Nan dai suka dinga Bata baki sai da suka dinga bata baki har ta hak'ura sukayi Breakfast suka gama.Bayan kammalawarsu ne Gwaggo ta ce Inteesar ta koma d'akin Muhdeen zata zo ta same ta,haka kuwa akayi Inteesar ta ka d'aki ba jimawa Gwaggo ta shigo hannunta d'auke da wani galam da kuma Babbar robar ruwa da wani abu a cikin robar.Inteesar na zaune saman sofa dake ckin bedroom d'i,gefenta Gwaggo ta zauna tare da ajiye su,kofin da ta d'aura saman Galam d'i ne ta d'auko robar k'arami ta bud'e tare da tsiyayo wani abu daga cikin gorar,mik'awa Inteesar tayi
"Kar'bi wannan yanzun ki shanye shi yanzunnan."
Kar'ba Inteesar tare da zubawa abun ido gashi kamar zuma Amma ga wani garin abu a ciki kamar garin magani a ciki.

"Gwaggo meye wannan kuma?"
"Zuma ce ta mata da tsumi,kar'bi kisha."
Kar'ba Inteesar tayi ta fara sha,dama ita akwaita da son zak'i to zak'in da taji ne yasa nan da nanan ta shanye shi tas.Kar'bar kofin Gwaggo tayi tare da zuba mata tsumin cikin kofin ta mik'a Mata, dai-dai lokacin da Mufida ta shigo d'akin,kafa baki Inteesar tayi ta fara sha sannan ta cire baki tana d'an yamutse fuska ta ce,
"Gwaggo naji wannan da d'an bauri bai yi zak'i kaman wancan ba,gaskiya ni ya isheni hakannan"
Ta k'arasa maganar tana mik'awa Mufida sauran tsumin kar'ba Mufida tayi zata shawa sai Gwaggo tayi saurin k'ar'ba ta mik'awa Inteesar tana cewa,
"Me yasa zaki bata?to ba irin nata bane,itama idan lokacin ta yazo zata sha ne amma ba yanzun ba."
"Yaushe ne lokacinta?"
"Lokacin da tayi aure kamar yadda kema kikayi."
"Gwaggo Wai kina nufin saboda nayi aure kika bani?"
"K'warai kuwa kayan mata ne gobe ma za'a kawo maki wasu,don Mummyn Mufida tasa akawo maki wasu."
Suna Jin haka sun san inda zancenaGwaggon ya dosa tura baki Inteesar tayi yayin da Mufida ke ta yi mata dariya.

"Nidai Gwaggo don Allah ku kyale ni wallahi bana so."
Fuska Gwaggo ta had'e
"Ke dalla gafara can ana nuna maki ga annabi kina rintse ido,akwai gatan da zamu nuna maki wanda ya wuce wannan ne?ko ba don shi jikana ba zanyi ba ko ba komai ni maiyi maki ne,Ballantana jikana nayiwa."
Ita dai Inteesar bata san inda maganar Gwaggo ya dosa ba,Don Bata gane nufinta ba.Turo k'ofar akayi had'i da sallama Mummy ce hannunta rik'e da food flask Aunty Abla na biye da ita a baya, Mummy ce ta mik'awa Gwaggo food flask d'in tana cewa,
"Kinga ma na d'auka sai gobe ne zata had'o da sauran kayayyakin ta kawo ashe ma Wai tunda an riga an dafa kazar shine ta fara kawo ta tare da sauran magungunan."
Aunty Abla ce ta gaida Gwaggo.

"Ina kwana Gwaggo"
"Lafiya lau Abla ya Mai gidan da yara duka?"
"Lapiya qalau suke Gwaggo."
"To masha Allah,amma kazar ce kawai ta samu?"
"Eh Gwaggo sauran Wai sai gobe zata had'o su,kuma ina da shwara Gwaggo matar nan k'awata ce munyi magana da ita idan ba damuwa da ankai Inteesar ta zauna a gidanta na sati d'aya yadda zata gyara ta ciki da waje,wallahi idan kika yadda na tafi da Inteesar gidanta na tsawon sati d'aya kawai wallahi sai kinyi mamakin canzawa da zatayi don Wallahi sai ta burge ki."
Jim kad'an Gwaggo ta yi tare da kllon Mummy ta ce,
"Fatima ya kika gani game da shawar k'anwar taki?"
Murmushi Mummy tayi tare da cewa
"Gwaggo nima nayi wannan tunanin,nariga ta a zuci ne ita kuma ta rigani a baki,nasan Hajiya Bilkisu k'awar Abla ce tun suna yara,sana'ara ce gyran amare da zaifi idan muka bari suka tafi tare don wasu ma tun biki na wata d'aya saura suke Kai yaransu gidanta."
Gwaggo jinjina Kai tayi
"To shikenan tunda haka kuka ce na amince ta tafi da ita d'in,amma fa ina ganin sai anyi fama da yarinyar nan, yanzun nake bata tsumi da zumar mata take ce Mani wai bata so mubarta hakanan."
"Karki damu Gwaggo zata kula da ita yadda yadda kamata ba zata barta hakanan kawai ba,ki tana so ki bata so sai anyi mata,ni kuma kullun zan dinga lek'awa Ina duba su.

Ta k'arasa maganar tana zama gefen Inteesar tana cewa
"Tare zamu tafi kinji daughter"
jinjina Kai kawai Inteesar tayi don bata son tayi masu gardama ne yasa ta yin shiru,amma ita har ga Allah bata k'aunar zuwa wani gidan gyaran da za'a kaita.

Mummy ce ta kalli Gwaggo tana cewa
"Yanzun taci kazar su tafi don ta ce sauri take zatayi bak'i."
Gwaggo ce ta bud'e flask d'in da aka zuba kazar ta mik'awa Inteesar,ganin gari-garin magani a jikin kazar yasa Inteesar ture baki, Gwaggo ce tayi Mata magana
"Zaki tsaya kina tura baki ko kuma zakici kazar ne ku tafi ko kuma zaki tsaya kina turawa mutane baki ne."
A shagwa'be ta fara maganar
"Wallahi Gwaggo na k'oshi ba wajen da zan saka kazar nan."
Jin hakan yasa Aunty Abla cewa
"Kada ku damu ku rufe mani flask d'in mu tafi dash,ko tana so ko bata so zata cimye shi tas."
Aunty Abla ce ta kar'bi flaak d'in ta rufe tare da kallon Inteesar ta ce,
"Tashi ki saka hijabi kid'ebi kayan sawanki na sati d'aya mu tafi."
Ba musu duk da a ranta bata so hakan ba amma bata da za'bi hakan ta mik'e ta d'auki hijab d'inta ta saka mummy ce ta ce,
"Kid'auki akwatin kayan da Mufida ta kawo maki jiya dadaddare kije dasu gaba d'aya."
Mufida ce ta janyo akwatin kayan gaba d'ayansu suka fita har harabar gidan,but d'in motar Aunty Abla Mufida ta bud'e ta saka akwatin kayan sannan ta bud'ewa Inteesar murfin motar gefen Aunty Abla ta zauna,sallama sukayi da juna sannan Aunty Abla taja motar tare da yin horn mai gadi ya bud'e mata suka fice daga gidan.
Chapter 33 · 0% Book details