← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 84

Sashe 9

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya ga abinda ya faru yayi murmushin takaici yace, "gashi kin kasa faɗa saboda Adnan ɗin, na tabbatar yana da girma a idon ki da kuma ƙima sosai. Ban taɓa tsayawa Adnan ya samu abinda yake so ba, a ko wanne lokacin shi yake nemarwa kan sa abinda yake so. A wannan lokacin nazo ne domin na nemi afuwar ki sannan ki yi haƙuri kar laifina ya shafe shi."

Mama tayi shiru bata ce komai ba Abba ya kuma cewa, "duk abinda kike tunani a wancan lokacin ba haka bane, babu yadda ban yi da Ali ba akan ki, na san ina da laifi amma a farko ban san da ƙudurin cutarwa a zuciyar sa ba, da na sani tun farko ba zan bashi goyan bayan aikatawa ba. Daga baya da na samu bayanin ƙudurin sa sai na biyewa son zuciya muka haɗa kai dashi. Babban kuskurena da nayi da na bar ki a wannan lokacin, ya kamata ace nayi wani abun ko dan saboda ƴaƴan ki da suke tare dake a lokacin amma san ban yi ba. Ki yi haƙuri komai ya wuce don Allah, haƙiƙa na ɗauki haƙƙin ki amma wallahi bani da laifi, ban ɗauki ko da ƙayar zarra a cikin abinda Ali ya ɗauka ba. Duk da nasan baza ki yarda ba, amma bazan rantse a kan ƙarya ba."

Mama ta sauke numfashi ko kusa bata son a tuna mata da mahaifin su Manal, ta kawar da kai gefe bata ce komai ba. Abba ya sake cewa, "ki yi haƙuri ki yafe min a karo na babu adadi." Mama ta kulle ido ta buɗe tace, "ni daman ba laifi aka yi min ba, in ma an yi min ya wuce ko dan saboda Adnan ɗin." Abba yayi murmushi cikin jin daɗi yace, "na gode sosai, Allah ya saka miki da alkhairi ya jiƙan iyayen ki."

Mama ta amsa da amin kafin tace, "kamar yadda kace baka taɓa tsayawa Adnan ya samu abinda yake so ba, wannan ne karo na farko da ka shige masa gaba dan ganin ya samu abinda yake so, Ni kuma a karo na farko zan hana Manal abinda take so. Babu abinda bana bata wanda take so koda shi kaɗai na mallaka a duniya ina sadaukar mata dashi. Amma a wannan lokacin zan juya sama ya koma ƙasa, zan hanata zama da Adnan ko tana so ko bata so. Saboda haka ra'ayina yake, yadda ban tashi da kowa a kusa dani ba, su ma haka nake so su tashi basu san kowa na su ba mu cigaba da rayuwa. Zata auri wani daban wanda bai sanni ba nima ban san shi ba, hakan shine mafita kuɓa shine kwanciyar hankali a wajena. In da ace na san zan haɗu da kai a da babu ƙaddarar da zata kaini zama a Kano, yadda na tashi nayi rayuwa babu wanda ya sanni haka nake so na koma ga Allah, hakan bazai faru ba sai Adnan ya fita daga rayuwar Fatima."

Tsoron ya bayyane a fuskar Adnan ya kalli Mama yaga gefe take kallo ya kalli Abba da yake kallon ƙasa ya kasa cewa komai. Baba ne yace, "Haba Zahra, meye ribar ki in kika raba aure da yake tsakanjn Manal da mijin ta? Laifin wani baya shafar wani ko a wajan Allah."

Da sauri Mama tace, "Bana son sake tuna wani abu da ya wuce ne, zaman shi da Manal tamkar dawo da hannun agogo baya ne, ka fita daga maganar nan kawai kar ma kace komai, haka za'ayi domin hakan nake so."
Abba yace, "baki yafe min ɗin ba kenan?." Bata ce komai ba dan bata son yin magana a gaban Adnan, da ace babu Adnan da sai tayi masa wankin babban bargo, sai ya tabbatar da wacce ya sani a baya ba itace yanzu ba.

Shiru Mama tayi bata kuma magana ba sai daga baya tace, "nace magana ta wuce a rufe wannan shafin bana son sake tunawa, maganar aure tsakanin Adnan da Manal ne babu. Sakin ta nake so yayi daga yanzu zuwa ko wanne lokaci, bana son zaman auren su ko da wasa."

Abba ya kalli Adnan da yake zaune ya kasa ko motsi kansa yan ƙasa, ya kalli ƴan uwan Adnan ɗin kafin yayi magana Baba yace, "kar ka damu, babu abinda zai faru in sha Allah." Tashi Mama tayi ta koma ɗaki bata sake magana ba, dole suka fito dashi dasu Baba zuwa waje Bab yana cewa, "ranta ne kawai a ɓace, amma da zarar ta wuce babu wani abin damuwa. Babu abinda zai raba auren Manal da Adnan in sha Allah."

Abba yace, "Allah ya amince, bana so laifin da nayi ya shafi Adnan bazai iya jure rashin matar sa ba."
"Babu komai in sha Allah" Baba ya kalli Bebi za yake tafiya kamar mara laka a jikin sa yace, "kar ka damu Adnan, ɓacin rai ne kawai yake damun ta, kasan in ka tuna da wani abun da ya faru a baya ka kan kasa sarrafa ɓacin ran ka. Shine yake bibiyar ta amma da zarar ta wuce shikenan komai zai wuce in sha Allah."
Adnan yayi godiyq sosai suka shiga mota suka bar ƙofar gidwn har lokacin shi bai gamsu da wannan zuwan basu ba.

Suna fita Mama ta fito daga ɗakin ta ta shiga inda Manal take ta kalle su tace, "eh baku da alaƙa ta jini da Adnan, ba yayan ki bane haka ba kowa naki bane aure ne ya haɗa ku. Auren kuma ina so ya ƙare daga yanzu. Manal nasan kina son abinda nake so, ban kuma taɓa hana ki abinda kike so ba. Na san kina son mijin ki kina ƙaunar sa, ina so ki sadaukar min da wannan soyayyar indai na isa da ke matsayin uwa ki bar auren Adnan har abada. Bana son auren ki da shi kuma bana ra'ayin hakan" ta kalle ta tace, "zaki yi min ko baza ki min ba?."

Manal jikin ta har rawa yake yi ga rashin lafiya ga tashin hankali, hawaye kawai take yi wanda ta rasa dalilin zuwan sa. Mama ta zauna gefen ta tace, "bazan iya jure ganin ki da Adnan matsayin mata da miji ba, zaki iya sadaukar min da soyayar da kike masa ko baza ki iya ba?."
"Zan iya Mama, zan yi, Tunda bakya so na haƙura."

Mama ta riƙe ta a jikin ta tace, "bawai bana son zaman ki da shi bane, kawai bana son tuna duk wani abu da ya faru a baya. Kamar yadda na san kin ji babu alaƙar jini a tsakanin ku, nace miki mahaifin sa shine mahaifin ki ne kawai saboda ki saka a ran ki babu ke babu auren sa, zaman ki dashi zai saka abubuwan da bana son bayyanar su su bayyana, ni kuma ban shiryawa hakan ba, faruwar hakan zai iya cutar dani shiyasa nake so ki rabu dashi ne Manal!." Manal ta girgiza kai tana kuka tace, "tunda kina so Mama zan yi."

Mama ya rungume ta tana shafa bayan ta tace, "Allah zai baki wani wanda ya fi shi, zai baki wanda baki tunanin samun sa ba in sha Allah." Ta ɗora hannun ta a akan cikin Manal tace, "babu yadda zan yi da cikin jikin ki, Amma gaskiya..." sai kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Manal dai kuka take tana jikin Mama dan babu yadda zata yi da ita ne, Amma tana son mijin ta bata son rabuwa dashi, kuma gashi bata ga laifin sa ba balle ace za'a raba su ta dalilin laifin. Daman tashin hankalin ta ace ita dashi jini ɗaya ne gashi yanzu ta tabbata babu abinda ya haɗa su meyasa Mama take so ta raba su?.

Sakin ta Mama tayi ta tashi ta fita Mubeena tabi bayan ta tace, "Mama Manal tana son mijin ta, tana ƙaunar cigaba da zama dashi, meyasa kike son raba su don Allah?."
"Mubeena bana son wannan maganar ta riga da ta wuce."
"Mama in kika aikata hakan kamar...." Dakatar da ita tayi tace, "bana son sake jin bakin ki a akan wannan maganar Mubeena, ki ƙyale ni na san abinda nake yi ni ba mahaukaciya bace."

Mubeena tace, "To Mama, amma me ya haɗa mu da shi mahaifin Adnan? Waye shi a wajan mu?, Gabaɗaya wannan tunanin shine ya cure mana ya tsaya a ƙirjin mu, waye shi?." Mama ta harare ta tare da yin tsaki bata ce komai ba ta wuce ta bar ta a wajan a tsaye.

Bebi a haka suka koma gida babu wanda yayi magana har ɗaki suka raka Abba bayan ya zauna ya kalle shi yace, "Hankalin ka ya kwanta ko Adnan? Baku da alaƙa ta jini da matar ka, abinda ya saka nace maka itama ƴa tace saboda ƴar babban abokina ce na wancan lokacin."

Bebi ya girgiza kai bai ce komai ba saboda zuciyar ta sa babu daɗi ko kaɗan, Abba ya kuma cewa, "in ka nutsu zan baka labarin dalla-dalla." Bebi yace, "Abba a nutse nake ina so na sani." Abba ya sauke numfashi yace, "dakai da ƴan uwan ka da kowa ma na gidan in an yi sallar magriba zuwa i'sha zan sanar daku a inda na san maahifiyar matar ka. Zan sanar daku abinda ya haɗa mu da abinda ya saka ta ke faɗar wannan maganar a kai na."

Bebi yace, "Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin. In sha Allah matar ka baza ta kubce maka ba, zata dawo ku cigaba da zama matsayin ma'aurata, kar ka damu." Bebi ya girgiza kai cikin sanyi jiki Abba yace, "yadda ban tsaya maka a lokacin auren ka ba, zan tsaya maka a yanzu wajan ganin matar ka ta dawo gare ka in sha Allah. Kar ka damu, zan zamar maka mahaifin da ka jima kana buƙatar irin sa, ba ma kai kaɗai ba dukkan ku."

Bebi ya girgiza kai dan ya fahimci canjin mahaifin nasu tunda daga kan wannan sa'in sa ɗin da suka yi da Mama. Bebi yace, "Allah ya tabbatar da hakan Abba." Ya amsa da amin suka yi masa sallama suka fito. Wajan Mama ya shiga bai jima a ciki ba ya fito ya hau mota ya tafi.
Chapter 9 · 0% Book details