Sashe 29
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu da zuwan Rumana gidan cikin dare Manal ta fara naƙuda, babu ɓata lokacin ya ɗauke ta suka tafi asibiti aka karɓe ta da gaggawa dan haihuwar tazo sosai. Allah ya taimake ta bata yi doguwar naƙuda ba tana shiga labour room ɗin Allah ya sauke ta lafiya ta haifi ɗan tanamiji, babu wanda ya faɗawa haihuwar saboda dare ne lokacin, sai bayan ta haihu lafiya lau ya jira akayi sallah gari ya waye sosai sannan ya kira Mummy ya faɗa mata ya faɗawa Mamy ma, ya dauƙi wayar Manal ɗin ya ɗauki number Mubeena ya faɗa mata.
Ɗakin da take hutawa ya koma ya tarar ta tashi daga baccin tana kwance ta riƙe kai da hannun ta ya ƙaraso yana kallon ta ya ce, "Sannu Partner, kan ki ne yake ciwo?." Kai ta ɗaga alamun eh ya ce, "ko jinin ki yayi ƙasa? Bara mu duba" ya faɗa yana fita ba jimawa ya dawo da abin auna jini ya gwada jinin ta anan yaga abinda yake tunani sai ya sake saka mata sabon ruwa.
Kallon ta yake bayan ya saka ruwan idon ta a lumshe kafin yayi magana tace, "bazan sake haihuwa ba yanzu, ni sai nan da shekara biyar." Dariya ce ta kama shi dan kuwa an sha raki kala-kala ko yace an sha ihu, duk da tayi ƙoƙari sosai ta daure abinda zata iya daurewa. Cikin son ya tsokanar ta ya ce, "ni da ina tunanin nan da shekara ɗaya kin dawo." Da sauri ta buɗe ido tace, "wallahi ba dai ni ba" ta faɗa zata masa kuka yace, "yi haƙuri kin ga ba lafiya ce dake ba."
Kallon gadon Bebin tayi ta gashi a kwance a ciki yana ta motsa hannu da alama ma idanun sa biyu, kallon Bebi tayi yace, "naso kin shayar dashi kafin mintina talatin da haihuwar ki, hakan zai ƙara masa lafiya ya kuma kare shi daga cututtuka manya da ƙanana. Amma hakan bai yu ba saboda ciwon kan nan, sannu partner, kin yi ƙoƙarin haifo mana shi, Allah ya miki albarka" ya faɗa yana shafa kanta ta tare da yin kiss a goshin.
Tayi murmushi ta amsa da amin tace, "ka ɗauko min shi." Ya ɗauko mata ya kawo mata shi ta ɗan tashi zaune tana riƙe dashi tana kallon sa. Fari ne shima sosai kamar ta, ta kalli Bebi tace, "da wa yake kama?."
"Dake mana, ai yadda kika sha wahalar nan dole ma yayi kama dake." Tayi murmushi tana kallon sa soyayar sa na ratsa zuciyar ta tana shiga ko ina na jinin ta, bata taɓa jin abinda yake shiga zuciyar ta lokaci ɗaya ba kamar sa.
Sunkuyowa yayi yana kallon ɗan shima kafin ya kalle ta yace, "Dake yake kama fa babu zancen wasa." Manal tace, "ni da Mamana naga suna kama." Yayi murmushi yace, "zaki hango ki ɗin ma tunda kin gano Mama." Buɗe ƙofar akayi tare da shigowa da sallama hakan ya saka shi miƙewa tsaye sosao yana kallon wanda suka shigo.
Huzaifa ne da Hamza baki har kunne suna murmushi Huzaifa ya ce, "ashe haka akayi shine ko labari? Gaskiya Bebi kaci amanar mu." Hamza yace, "Sannu Manal, Allah ya ƙara lafiya ya raya abinda aka samu."
"Amin Dr, na gode sosai." Huzaifa ya kalle ta yace, "Sannu Manal, Allah ya raya mana shi ya masa albarka." Tayi murmushi tace, "Amin Yaya Huzaifa na gode" ta faɗa ta bawa Bebi yaron ta koma ta kwanta saboda baccin da taji yana sake dawowa.
Bebi ya bawa Hamza shi suna ta yabawa ganin ta fara lumshe ido alamun bacci sai ya ce, "muje waje bacci zata yi, jinin ta yayi ƙasa." Ta buɗe ido tace, "Partner waje akwai sanyi kar yayi mura." Huzaifa yayi dariya ya ce, "da gaskiyar ki Manal in muka fita dashi mura zai yi." Bebi yayi dariya shima yace, "kar ki damu zan kular miki dashi." Jin hakan sai ta kulle ido suka fita daga ɗakin.
Zuwa wani lokaci kaɗan Mubeena da Maman Surayya da Surayyan sun zo, sune zaune a ɗakin da yaron a hannun su ana ta yaba shi, ma'aikatan asibitin suna ta zuwa ganin yaron ana taya su murna har lokacin Manal bacci take yi sosai.
Basu jima ba Mama da Mummy da Maryam ma suka zo asibitin suka zauna tafredasu Mama ɗin ana taɓa hira kaɗan-kaɗan. Manal sai sha ɗaya na safe ta buɗe ido, idanun ta na buɗewa kukan jaririn ne ya fara ratsa kunnen ta, ta tashi zaune tana kallon su Surayya tace, "Sannu Milky." Ta amsa tare da faɗin, "Mummy ina kwana." Mummy ta amsa tana yi mata barka suka gaisa da Mamy ma da Maman Surayya kafin Maman Surayya tace, "ai ki karɓe shi tun ɗazu yake kuka yunwa yaje ji. Surayya bata shi."
Gaban Manal ya faɗo lokacim da aka bata taron a hannu, wai yanzu a gaban şu zata kwaye riga ta bawa yaro nono duk suna gani? Ga Mummy ma a zaune a gaban ta zata ɗaga rigar ta sama ta bashi nono? Taɓ ashe bazai sha ba kuwa. Mummy tace, "ai Hajiya Balaraba sai kin koya mata, ina Manal zata iya shayar dashi yanzu?."
Maman Surayya ta tashi ta ƙarasa inda Manal take Manal tace, "Mama ni kunyar su Mummy nake bazan iya shayar dashi ba."
Mama tace, "to meye na kunya? Bana son shirme Manal ki bashi ya sha yunwa yake ji ko na aika kira mijin ki."
Zip ɗin ta buɗe daga baya amma ta kasa yin abinda ya kamata. Maman Surayya tace, , "baza ki ciro ki bashi bane ba wai yaro yana kuka?." Manal ta sauke numfashi ita bata san taya zata fara bane wallahi.
Manal harda ƙwalla ta tana so tayi amma ta kasa dan da gaske kunyar take ji ba wai da wasa ba. Ta kalli Mama tace, "don Allah Mama ki bani mayafin ki na yafa sai na bashi." Mama tace, "akan me zan bari ki rufe shi sai kin tosshe masa hanci?."
"Allah bazan toshe ba." Mama tayi tsaki ta kalli Surayya tace, "bani mayafinki, wai kunya take ji ita baza'a ga nonon ta ba."
Mummy tayi dariya Mamy ma haka Mummy tace, "da gaskiyar ta, mu sai mu bata waje ma tafi sakewa."
Mama Surayya tace, "don Allah ku yi zaman ku, shirme ne irin na Manal." Mummy tace, "A'a bara mu koma waje tafi samun nutsuwa." Mama tace, "to mu ma sai mu biyo ku in yaso sai a turo mijin ta sai ya taya ta tunda shi wataƙila baza ta ji kunyar sa ba."
Mamy tayi dariya tace, "A'a dai ki yi haƙuri ki zauna" ta faɗa suna fita. Manal ta kalli Mama tace, "Mama yanzu fa har yaro ina dashi kice ina shirme?, haihuwa nayi fa kuma haihuwar da wahala." Jin yadda tayi maganar cikin shagwaɓa Maman Surayya tace, "Sai na bufe miki baki, dallah malama ki shayar dashi ko na ciro da kaina na bashi wallahi."
"Yi haƙuri" Manal ta faɗa tana yafa mayafin ta ciro guɗa ɗaya Mama ta nuna mata yadda zata yi tana cewa, "ki daure zaki ji zafi amma zaki daina."
Da to manal ta amsa da ya fara sha harda kuka wai zafi, Sai da taga Maman Surayya na yi mata faɗa sosai sannan ta daina kukan sai hawaye. Ya jima yana sha kafin ta karɓe shi Mubeena ta karɓa a hannun Maman tana yi masa hotuna dan yaron ya burge ta sosai.
Wajan su Mummy Mama ta fito ta bar Surayya da Mubeena a can ana ta zuwa sai dai a shiga wajan Manal ɗin.
Lokacin da Bebi ya shiga ita kaɗai ya samu a ɗakin duk suna waje a zaune har yaron yana wajan su, ya zauna a gefen ta ya ce, "ya ciwon kan? Ya naga kamar kin yi kuka meya faru?."
"Ba Mama bace ta dage sai na shayar dashi, kuma wallahi zafi nake ji." Yayi murmushi ya ce, "yanzu ɗan zafin da kika ji shine na kuka? Partner yanzu fa ke uwa ce ki tuna mana."
"Allah da zafi, ni kaɗai na san abinda naji."
"To shikenan yi haƙuri zaki daina ji in sha Allah." Ta ɗaga kai ya ce, "an masa test komai nasa lafiya lau yake." Tayi murmushi tana kallon sa ya
ce, "amma yadda kika dage wajan ƙauracewa zaƙi da cikin sa haka za'a sake maimaitawa Partner."
Manal tace, "zan yi ko dan shi" ta fada tana kwanciya a jikin sa tace, "yana hannun waye da ka shigo yanzu?."
"Yana hannun Surayya."
"Kar fa Surayya taje ta ƴar min dashi, wallahi ba wani iya riƙe shi tayi sosai ba." Ya kalle ta yaga harda turo baki ya ce, "ta ya zata ƴar dashi?."
"To ta san zafin haihuwar ne? Ni fa na shiga labour room ba ita ba." Yayi dariya sosai yace, "ƙwarai kuwa kece, amma duk da haka baza ta yar miki dashi ba." Tayi shiru yayi dariya ya rungume ta ya ce, "kina ji dashi ko? Nima ina jin sa har zuciyata kusa inda ki ke a zuciyata, ji nake kamar na karɓo shi na dinga kallon sa kawai. Ina son ki Manal kin mayar dani uba a yau."
Tayi murmushi ya sake ta yana kallon ta ya ce, "in kin warware zamu wuce gida." Manal tace, "gidan Mama?." Ƙwanƙwansa ƙofar akayi sai ya tashi daga kusa da Manal ya ce, "a shigo." Maman Surayya ce ta shigo tace, "zan ɗauki wayata ne." Yayi murmushi ya ce, "Mama ma gwara da kika shigo, zamu tafi gida da ita yanzu ya zaa yi?."
Mama tace, "au ba gida zata tafi ba kenan?." Ya girgiza kai ya ce, "Nafi so ta zauna a gidan ta gaskiya." Mama tace, "wannan ai ba damuwa, daman mun yi magana da Maman ta ka kan hakan, babu damuwa ni da kaina zan zo na zauna da ita." Ya ce, "kai amma naji daɗi soaai, Allah ya saka da alkhairi" ta amsa da amin ta fita ya kalli Manal yace, "ga Maman Surayya zata zauna dake."