Sashe 36
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya kalli Daddy yace, "Alhaji Ali, sai ka ɓace ɓat bayan ka tattara koma ka gudu." Daddy yayi murmushi yace, "kuma wallahi kana raina, daga baya ne na manta da komai." Abba yace, "Wai kuwa ina Zahra matar ka?." Daddy ya sauke numfashi ya ce, "daga baya na dawo ina neman ta amma ban same ta ba, na shiga damuwa sosai a kanta, dan wallahi nayi dana sanin abinda nayi mata matuƙa. na dawo da niyar na bata haƙuri na kuma mayar da ita ɗakin ta amma ban ganta ba. Har yau ina yawan tunanin ta ina kuma so na sake ganin ta."
Abba yace, "Yanzu wannan arzuƙin da ka tara har ya kai baka zaman nigeria duk da duniyar ta ka shi ko?."
Ya sauke numfashi yace, "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi."
Abba yayi murmushi yana girgiza kai yace, "ai abinda muka yi bamu kyauta mata ba daga ni har kai, haƙƙin ta sai ya bibiye mu ni da kai, dan mune silar barin ta cikin ahlin ta."
"Wallahi na sani, na sani kuma nayi nadamar tafiya na barta bayan nasan bata da kowa sai ni. Gaskiya ban kyauta ba nima na sani, saboda haka har Baby na sakawa sunan ta Zahra, duk sanda na kira sunan Zahra ina tunawa da ita nayi mata addu'a a zuciyata, in tana da rai ina so na ganta ko dan na nemi afuwar ta, in bata raye Allah ya jiƙan ta, ammaa na san Allah zai tsayar damu ni da ita yayi mana hisabi."
Abba ya kalle shi yace, "in akace tana da rai abin zai fi zuwa da sauƙi, ka nemi yafiyar ta tun kafin zuwan mu lahira."
"Inda hakan zai kasance wallahi zan ji daɗi sosai."
Abba yace, "Zahra tana nan da rai, yaran ka biyu da ka bari a wajan ta suna nan suna numfashi, ɗaya har tayi aure ma ta haihu, ɗayar tana nan ance itama an kusa bikin ta."
Gaban Daddy ya faɗi sosai, ya kalli Abba yace, "da gaske ka ke? Ka ganta ne kai?." Abba ya girgiza kai yace, "tabbas na ganta, na kuma san inda take, amma ita bata san na san inda take ba, kuma bata san ina da rai ba har yanzu" ya faɗi haka dan yaji me Daddy zai ce.
Daddy da hanzari yace, "to muje mu ganta mana, ina so na bata haƙuri akan abinda nayi mata wallahi. Nayi kuskure na kuma yi nadamar abinda na aikata, gwara mu je mu nemi afuwar ta kafin rai yayi halin sa."
Abba yace, "Da gaske ka ke kayi nadama? Ni dai har zuciyata nayi wallahi, Allah ne shaida ta."
Daddy yace, "Wallahi nima nayi, ai girma yazo yanzu, ko a da na faɗa maka na karɓi kuskurena balle yanzu. Duk abinda muka yi mata in aka yiwa yaran my haka ai bazan mu daɗi ba koda muna kabarin mu ne."
Abba ya sauke numfashi yana girgiza kai yace, "hakan babu daɗi ko kaɗan, Akwai ciwo a yiwa ɗan ka abinda ka yiwa ɗan wani, akwai radaɗi da azabar da baza ka gane abinda nake cewa ba sai ya faru dakai." Daddy ya ce, "muje mu ganta yanzu ba sai anjima ba, saboda halin rai nake gudu kar na faɗi na mutu bata yafe min ba, muje duk hukuncin da zata yanke min a shirye nake da na ɗaukr shi. Na cutar da ita ni kaina na sani."
Abba yayi shiru bai ce komai ba Daddyn ma yayi shiru suna tunain abinda ya faru a baya, jin abin suke a zuciyar su suna ji kamar a lokacin yake faruwa. Abba ya tashi tsaye yace, " indai ka shirya muje na raka ka inda Zahra take."
Daddy ya goge hawaye idanun sa yace, "gabana faɗuwa yake sosai, amma dole na tunkari Zahra domin neman ya yafiyar ta da yafiyar yaran da na bar mata, na cutar da iya cuta mai muni har bana son tuna abinda ya faru." Abba ya murmusa kawai bai ce komai ba Daddy ya miƙe tsaye suka fito.
Tare suka fito harabar gidan Huzaifa da Bebi suna tsaye suna tattauna batun Rumana, ganin sun fito ya saka suka ƙarasa wajan su, da mamaki suke bin su da kallo ganin duk yanayin su ya canja kamar ma kuka suka yi. Bebi ya ce, "Daddy lafiya? Me ya faru?." Daddy yace, "zamu je wani waje mu dawo, kar ku damu yanzu zamu dawo." Huzaifa yace, "To Daddy ba sai mu kai ku ba."
Daddy yace, "ku bari muje da kan mu." Abba yace, "babu komai Alhaji Ali, su kai mu ɗin." Ya kalli Abba yace, "taya zamu je dasu? Kar ka manta inda zamu je."
"Ina sane, sanin hakan ne ya saka nace muje dasu. Huzaifa ku shiga motar mu je."
Huzaifa ya shiga gaaba Bebi ya shiga mazaunin driver su kuma suna baya ya fita da motar. Sai bayan ya fita da motar sannan yace, "Abba ina zamu je?." Abba yace, "kai mu unguwar su Manal." Da sauri Bebi ya kalli Abba ta miror ya kalli Daddy ma nan take zuciyar sa ta fara bugawa zuciyar sa na zargin wani abun wanda bai kawo shi a zuciyar sa ba ko kusa.
Har ƙofar gidan su Manal Abba ya suka je sannan yace su tsaya, Bebi ya kalli Huzaifa shima ya kalle shi kafin su ji Abba yace, "a wannan gidan take rayuwa." Tare suka kalli inda Abba ya nuna, Huzaifa bai san labarin ba amma Bebi shi nan take ya gano ƙarshen zancen dan har ga Allah da ake maganar abokin Abba ne bai kawo hakan a zuciyar sa ba. Bakin sa na rawa yace, "Abba, kenan Daddy shine....." kasa ƙarasa maganar yayi Abba ya buɗe motar ya fita shima Daddy ya fita.
Suna fitowar daga motar suka tsaya a kofar gida, Bebi ya kasa fitowar daga motar ya ƙame ƙam a ciki ya kasa motsin kirki, shi kam Huzaifa bai gane inda maganar ta dosa ba tunanin sa me suka zo yi a gidan su Manal?.
Da wannan tunanin ya fito daga motar shima Bebi ya fito da sanyin jiki ya ƙarasa inda suke Abba ya kalle shi yace, "Adnan kayi mana sallama da mutanen gidan." Waya Bebi ya ɗauka jiki a snayaye ya kira number Mubeena akayi sa'a ta ɗauka, sai da suka gaisa sannan yace, "in kina gida ki sanar da Mama zamu shigo yanzu, tare muke da baƙi." Ta amsa ya kashe wayar ba jimawa ta kira shi ya ɗauka jin abinda tace sai ya kashe ya kalli Abba ya ce, "Abba mu je."
Da sallama suka shiga cikin gidan aka amsa daga cikin falon suka ƙarasa ciki tsoro da fargaba ya gama mamaye su, yayi da mamaki da bugawar zuciya ke tattare da Adnan. Da Abba suka haɗa ido kafin ta ɗauke ido ga kalli wanda yake gefen sa shima kuma ita yake kallo cikin matuƙar mamaki.
BDƘB3P20
Kallon sa Mama take yi kafin ta ɗauke kai ta sake kallon sa a lokacin ya cire glasses ɗin idanun sa shima yana kallon ta da matuƙat mamaki. Kallon Abba yayi a lokacin da suka shiga falon Abba ya ɗaga masa kai alamun itace dai ya sake kallon Mama da lokaci ɗaya fuskar ta ta sauya. Baba ne kawai suka gaisa dasu amma banda Mama da ta miƙe tsaye daga inda take.
Baba ne ya kalle yace, “Fatima ina zaki je? Kina ganin ga baƙi sun zo wajan ki?.” Mama ta kalli Baba tace, “wannan ba baƙin da zan zauna nayi magana dasu bane, basu da wannan daraja da mutunci a idona da zan saurare su.”
“Me kike cewa haka? Wannan wacce irin magana ce?” Baba ya faɗa yana kallon ta.
Mama tace, “Bani da wannan lokacin” ta faɗa tana shiga ɗaki duk suka bita da kallo. Baba ya tashi ya bita ɗakin da ta shiga yace, “Haba Zahra meye haka? Wannan wanne irin hali kika ɗauko wanda a baya baki dashi?. Baƙi su zo ganin ki ki dinga faɗa musu wannan maganar? Kar ki manta akwai mahaifin Adnan a cikin su da shi kansa Adnan ɗin, kuma shi sirikin ki ne mijin ƴar da kika haifa.”
“Ba shiyasa nace zan raba auren ba ka hana ni? Ba shiyasa nace Manal ta bar auren sa ba ka dage akan sai ta koma masa ba. Bazan taɓa ganin mutuncin sa ba har abada, da ya tashi sake zuwa sai yazo min da wanda na tsana bana son ganin sa har duniya ta tashi, bana ƙaunar sake kallon sa bana son tunawa da komai. Da ka barni na raba auren Manal da Adnan na tatatta ta mun bar garin nan ta yadda babu wanda zai san inda nake balle ya sake zuwa wajena, saboda Manal kawai nake zaune a garin nan sai kuma kai, amma wallahil azim da yanzu bama garin nan na jima da barin sa na koma inda babu wanda zai san inda nake. Wanda ya sanni a baya bana so ya sake ganina.”
Baba yace, “waya shi wanda yazo miki dashi ɗin yanzu?.” Mama ta share hawaye ta tace, “kaje ka tambaye su, don Allah ka bani waje bana son magana.” Baba ya juyo ya fito yana kallon su da alama duk abinda ta faɗa sun ji. Abba ya kalli Baba yace, “wannan shine Aliyu.” Baba ya kalle shi ya girgiza kai yace, “na gano inda maganar ta nufa, kenan ta fahimci kaine na kuma gane ka shiyasa ta bar wajan nan.”
Mubeena da take zaune a wajan da mamaki tace, “Baba meye ya sake faruwa? Waye wannan ɗin?.” Baba ya kalle ta ya kalli Ali da yake kallon Mubeena, nan take idanun sa suka yi ja dan ko ba a faɗa masa ba ya san ƴar sa ce, ga kama da Aysha nan ƙarara a kan fuskar ta. Baba yace, “Mahaifin ki.” Da sauri ta kalli wanda aka kira mahaifin ta ta sake kallon Baba tace, “mahaifina Baba? Taya zai zama mahaifina bayan Mama tace mahaifin mu ya jima da barin duniya?.”