← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 84

Sashe 49

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Huzaifa tayi tace, “Yaya Huzaifa ka gaida gida.” Ya amsa ta shiga ciki Bebi ya kalle shi har lokacin Ayan yana hannun sa yace, “da alama komai ya zama normal ko?.”
“Alhamdulillah, wallahi komai ya daidaita, sai aby ya koma raha ana farin ciki. Yanzu haka Mubeena tana gidan mu a can zata kwana, itama Manal ɗin wai na kira ka nace maka zata kwana.”

Yayi murmushi yace, “haka ake so, Allah ya sake daidaita tsakani.” Ya amsa da amin kafin ya shiga mota ya fita shi kuma ya shiga ciki.

A tsaye ya ganta a falo ya kalle ta yaga shi take kallo ya ƙaraaa ya ajjiye Ayan a kan kujera ya kalle ta yaga dai kallon sa take yi, ya ce, “kallon na meye ƴan mata?.” Murmushi tayi ta matso ta rungume shi ta kwantar da kanta a ƙirjin sa. Hannu biyu ya saka ya zagaya da hannun sa bayan ta ya riƙe ta yace, “akwai labari ne?.”

“Ka taya ni murna partner, maahifina da ƴan uwan Mama duka komai ya zama daidai. Farin ciki nake ji sosai a raina, nayi murna da bayyanar dangin Mamana, ko babu komai na san ƴan uwan Mamana a kusa dani.”

“Ina taya ki murna Manal ɗina, Allah ya baki ikon yi musu biyayya, Allah ya cigaba da saka ki farin ciki har abada.” Ta sake riƙe shi sosai tace, “amin Partner. Yanzu Mama kuka ya ƙare in sha Allah, damuwar Mama tazo ƙarshe, wannan dalilin yafi min komai daɗi wallahi.”

Ya ɗago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta ganin sai murmushi take yi yace, “ai in sha Allah rayuwa za’a yi mai daɗi wacce ba’a yi ta a baya ba, addu’a ai ba ƙarya bace ba Manal. Kuma na faɗa miki mahaifi mahaifi ne, dole ki ji farin ciki a zuciyar ki Manal.” Ta girgiza kai tace, “gaskiya ne wannan, na amince. Ka san me Yayan su Mama ya yiwa Baba da Maman Surayya alƙawari?.” Ya girgiza kai alamun A’a ta sauke numfashi tace, “Duk ya biya musu aikin hajji, kowa sai murna yake yi, wajan ya koma wajan farin ciki.”

Bebi yace, “ma sha Allah, amma ya kyauta sosai nima naji daɗi.” Mayar da ita jikin sa yayi ta sake kwanciya a ƙirjin sa ya lumshe idon sa, Manal tace, “Naji daɗi nima sosai.”
“Daman ba tare ku ke da Maman ba?.”
“Uhum tace sai gobe zata zo.”

“Allah ya nuna mana, ai kin ma ware kamar baki haihu ba kin yi kyau sosai, ta kular min dake yadda ya kamata jira kawai nake ta dawo min dake ɗakina. Allah Manal na gaji, nayi haƙurin rashin ki, na sake yi na kuma yi amma na kusa kasa jurewa abin yayi yawa. Kin warke tuni baki da wata matsala amma ko kwana inda nake bakya so, kin barni kamar maraya bayan ina dake. Gaskiya na gaji Manal, na gaji wallahi, ke kin san nayi ƙoƙari sosai” ya faɗa yana ɗago ta daga jikin sa yana kallon ta.

Manal tace, “to har yanzu fa bani da tsarki, nima na gaji na tsani wannan jinin wallahi, yaƙi tafiya ya barni.” Yayi murmushi yace, “kora shi zan yi dan da gaske ya fara cutar dani, na gaji ina missing ɗin ki sosai, baza ki gane abinda nake ji bane shiyasa.” Tace, “in ka faɗa min zan gane.”
“A’a baza ki gane ba, gwara nayi shiru.” Tayi dariya tace, “kayi min girki yunwa nake ji, baka taɓa yi min girki ba don Allah yau kayi min” ta faɗa tana kallon sa a shagwaɓe.

Ya kalle ta ya ce, “haka nace miki na iya girki?.”
“Indai kayi min, Allah yunwa nake ji, yaron nan sai ya dinga cinye mim abincin jikina.” Ya kalli Ayan da yake ta kalle-kalle dan idon sa biyu ya kalle ta yace, “muje dai na haɗa miki tea ba girki ba, akwai wheat bread ai nazo dashi.” Ta fara yi masa dara tana buga ƙafa tace, “ni Allah bana son tea abinci nake so kuma kai nake so ka dafa min.”

Yace, “Manal me zan dafa miki? Na gaji daga aiki na dawo fa baza ki tausaya min ba?. Muje dai na haɗa miki tea da kaina amma batun girkin nan ki barshi. Mu je har kwai sai na soya miki.” Manal ta bishi da kallo tace, “yanzu baza ka yi min ba?.” Bebi ya kalle ta yace, “ƙarya da ciwo, in nace zan miki ƙarya nake yi. Zo muje dai” yayi gaba yana jan hannun ta zuwa kitchen ɗin tace, “Allah inda a novel ne mijin novel sai yayi mata girki duk abinda take so, amma kai bak iya soyayya ba.”

Cak ya tsaya yana kallon ta yayi dariya kafin yayi tsaki ya ɗauki akwai guda biyu ya ɗora fan a kan wuta ya saka mai, ya fasa akwan a kai ba tare da ya saka maggi ko albasa ba yace, “yanzu zai yi sai ki ci.”

Manal ta kalli kwan tace, “kalli fa ko maggi babu, kuma baka saka albasa ba taya zan ci abu yana ƙarni?.” Ya wara ido yace, “au soya miki ɗin ma da nayi bai miki ba kenan?.”
“Bai min ba” ta faɗa tana kallon gefe ɗaya ya girgiza kai ya ce, “kin yi da ɗan halak.” ta murguɗa baki kafin tace, “na bar ɗana a falo” ta faɗa tana fita da sauri sai gata ta dawo dashi a hannun ta ya kalle ta ya ce, “Ke bakya jin kunyar cewa ɗanki ki ko a gaban Mama?.”

Manal tace, “to ba ɗan nawa bane?, ai ni na sha wahalar haihuwar sa ko?.” Yayi ƴardariya yace, “naki ne.” A lokacin ya cire ƙwan daga cikin fan ɗin ya saka mata a mini plate yace, “to gashi nan.” Taja kujera a kitchen ɗin ta zauna tace, “saura tea ɗin, kuma ka wanke fan ɗin kar ka bar min shi ya kwana.” Ya harare ta ya ce, “to sannu Mummy, ita ce zata bani wannan umarnin ba ke ba.”

Tayi dariya yace, “ƙyayi dariya ai.” Manal tace, “kai ko karar nan baka yi min, haifar maka ɗa nayi ya kamata ka dinga yin abinda nace.” Ya ajjiye mata tea ɗin yace, “yanzu kika ce min ɗan ki ne” ya faɗa yana buɗe fridge ya ajjiye mata bread ɗin. Manal tace, “eh ɗana ne, amma kaima ɗan ka ne.” Ya girgiza kai yace, “A’a naki ne ke kaɗai, na bar miki.”
“Ni kaɗai na haife shi?.”
“Eh mana, ba kin ce ke kaɗai kika shiga labour room ba?.”
“To waye yayi min cikin?.” Da sauri ya juyo yana kallon ta, sai ta rufe bakin ta da hannun ta tare da kulle ido. Yayi dariya yana girgiza kai yace, “Lallai Manal kin waye, ko ƴar kunyar nan da ki ke ji yanzu guduwa take yi. Wato waye yayi miki cikin ko? Eh tabbas ni nayi wannan. daman tun kafin a haifi Ayan ki ka ce min nayi miki ciki.”

Shiru tayi bata amsa masa ba ta fara shan tew ɗin yana ta tsokanar ta taƙi kula shi har ta gama ta koma ɗakin ta tana dariya, ta ajjiye Ayan tayi wanka ta saka kayan bacci, ta canjawa Ayan kaya tana gyara shi ya shigo yace, “Muje ko?” Ya faɗa yana ɗaukar baby bed ɗin da Ayan a ciki ya fita dole tabi bayan sa.

Bayan Kwana biyu.

Manal na shan baƙi masu zuwa gidan ta, kullum sai ƴan uwan Mama sun zo da yaran su ana gaisawa. Kullum cikin baƙi take in ba’a zo ba ita zata je, kwanakin ya zamar mata na farin ciki ta san wanda bata sani ba a ƴan uwan ta sosai. Har gidan su taje ta yini har dare tana can ana hira ta saba da kowa da kowa ta kuma sake kamar daman can a gidan ta tashi.

Mubeena da Mama sun je Abuja kwanan su biyu a can ana ganin gidan ƴan uwa Mama tace Manal Sai Ayan ya gama yin ƙwari taje daga baya. Zuwa Jalingo ne Manal ta dage sai taje, da Bebi ya hana harda kuka dole ya haƙura ya sallama ta da yaron sa suka tafi Taraba state. Kwanan biyu suka yi suka dawo cikin kewa ʼƴan uwa dan kowa yaji daɗin ganin Mama da yaran ta harda jika. Lokacin da suka dawo kuma Daddy yake son suje dangin sa da suke garin Zaria da cikin Kaduna, haka aka sake ɗaukar hanya bayan kwana biyu suka dawo kasancewar babu ƴan uwa a can sa na uba.

Manal dai tana ta shan yawo Ayan har ya fara mura da zazzaɓi mai zafi, ranar da suka dawo daga Zaria Bebi yace tayi haƙuri amma babu inda zata sake zuwa sai ɗan sa yayi ƙwari ya gaji da wannan yawon da take yi.

Maman Surayya tunda Manal suka fara yawon nan ta tattara ta koma gida, amma ta gama gyara Manal ta ko ina ta ta kuma tsuma ta yadda ya kamata. Washe farin da suka dawo daga Zarria Bebi ya saka ta a mota suka je har gidan Maman Surayya siyayyan kayan abinci, da kayan sakawa da kuɗi suka je aka yi mata godiya mai yawa aka kuma bata wannan kyauta. Taji daɗi sosai tayi murna mijin ta ma da ya dawo yaji daɗin yadda suka karrama Mama ya kuma yaba domin sun san alkhairi. Ita kanta Mama taji daɗim abinda suka yi mata dan yaba kyauta bahaushe yace tukwici.

A ranar bayan sun dawo daga gidan su Surayya Manal tayi wanka ta shirya Ayan ta tayar da shafa’I da wutir kenan Bebi ya shigo ɗakin. Kallon ta yake yi da mamakin yaushe ta fara sallah bai sani ba? har ta idar yana zaune ya kalle ta ya ce, “shine ko labari?.”Tayi dariya ƴar tace, “jiya ne fa.”
Chapter 49 · 0% Book details