← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 84

Sashe 59

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bebi ransa ya sake ɓaci yace, “Kaga in ka sani ka faɗa min in baka sani ba ka daina min maganar banza da wofi, ƙanwar kace amma ai baka kaini son ta ba ko?, Baka kai ni sanin darajar ta ba, baka kai ni rayuwa da ita ba, kuma baza ka kai ni damuwa in ta shiga wani hali ba. Ka barni naji da abinda yake damuna ba da wannan maganar ta ba.” Hamza yace, “wannan maganar taku ba itace mafita ba, ku tsaya a nemo mafita mu tambayi inda ake tunanin zata iya zuwa. Ku yi haƙuri don Allah kowa ya nutsu a samo mafita.”

Bebi a fusace yace, “ba mafitar nake nema ba yana nema ya sake ɓata min rai, ya barni naji da abinda yake damuna mana, ai bazai kaini shiga damuwa ba in wani abin ya same ta ba. Yasan irin tashin hankalin da nake ciki a yanzu?, Har wajan Yayar maman su naje amma bata je can ba, hankalina ba a jikina yake ba meyasa ka kasa fahimta?.” Huzaifa yayi ƙaramin tsaki ya tashi tsaye yace, “tunda har na tabbatar da Manal jinina ce bazan bari wani abu ya same ta ba, ina da haƙƙin da zan nunawa mijin ta kuskuren sa in yayi sakaci da lafiyar ta. Yaje ya nemo ta matsayin sa ba mijin ta, matsayin a na yayan ta zan je na nemo ta nima. Zaman tattaunawar bashi da wani amfani dan ba mafita zai kawo ba” ya faɗa yana fita daga falon.

Hamza ya kalli Bebi yace, “ka kwantar da hankalin ka ka nutsu ka tuna ƴan uwan maman ta na wani garin ka kira su kaji ko taje can.” Bebi yace, “ba kowa nake da number sa ba a cikin su.”
“Ka san yadda zaka samu ka kira koda da niyar gaisuwa ne in tana can zaka fahimta, in bata can ma zaka gane. Amma maganar gaskiya kayi kurkuren Adnan.”

Bebi yace, “na sani Hamza, na karɓi kuskurena bazan kuma bari hakan ta kasance ba. Raina ne ya ɓaci sosai kuma ta dinga yi min maganar da bazan jure ba.” Hamza yace, “shiyasa nake faɗa maka tun a baya kenan ka dinga sarrafa ɓacin ranka, kar kace in ranka ya ɓaci na wani ma sai ya ɓaci, kaga yanzu hakan bashi da amfani.” Bebi yace, “na gane hakan, zan san inda take a daren nan in sha Allah.” Hamza yace, “Allah ya bayyana ta yasa tana cikin ƙoshin lafiya” ya faɗa yana fita ya bar Bebi cikin tunanin inda take.

BDƘB3P36

Hamza da ya fita a mota ya samu Huzaifa yana danna waya yana shiga yaja motar suka fita daga gidan ya kalle shi yace, “Huzaifa Bebi na cikin damuwa bai kamata ka yi masa haka ba.” Huzaifa yace, “ina sane nayi masa haka dan na nuna masa kuskuren sa na barin ta ta fita da daddare, tun farko mun faɗa masa ya sanar sa ita maganar Rumana yaƙi, duk akan ta ake wannan abun.”

“Daman bai faɗa mata ba?.”
“Bai faɗa mata ba wallahi, ita kuma yanzu damuwar ta wai da Rumana bata kasance jinin ta ba da yanzu sai dai a kawo ta matsayin matar sa. Kasan mata da kishi, a daren ya hau sama saboda fushi, itama ta hau sama saboda kishi dole a samu matsala.”

Hamza ya kalle shi yace, “kai ya akayi ka san da hakan?.”
“Saboda tana gidana, tun a daren taje gidana ban ma san ta kwana ba sai da safe” ya faɗa tana kallon Hamza. Hamza tayi dariya yace, “amma kai ɗan iska ne wallahi, kana ganin yadda ya haukace baza ka faɗa masa tana gidan ka ba?.”

Huzaifa yace, “wallahi bazan faɗa masa ba, Sai ya gane kuskuren sa na barin ta ta fito ita kaɗai ga jariri, sannan sai ya gane illar kasa saarrafa ɓacin ran sa akan komai. Duk da ba duka labarin ta bani ba amma akan Rumana aka yi faɗan, shine tayi fitowar ta ta tafi gidana.” Hamza yace, “gaskiya dai bai kyau ba, amma itama banga abin barin gida a nan ba.” Huzaifa yace, “mata ne fa, yanzu ƙaramin abu zai koma babba. Kuma abinda ya saka ban dawo masa da ita ba rashin neman ta da bai ba, kuma tunda fushi tayi sai ta huce ta sauka sai ta koma.”

Hamza yace, “gaskiya ne. Amma don Allah gobe ka sanar dashi in ba so ka ke a samu matsala ba, kai ka san irin son da yake mata zai iya shiga wani yanayi.” Huzaifa yayi tsaki yace, “na raina son da yake mata ai wallahi, babu wani so duk a baki ne. Kuma sai na nuna masa nima ƙanwata ce yadda yake kishin su Mimi ina kishin ta.” Hamza yayi dariya tace, “kana so ka wahalar dashi kawai, amma batun so kai ka san yana son ta, ka kalli yadda ya koma dai” yayi dariya ya cigaba da jan motar suka tafi.

A daren Bebi ya rasa yadda zai yi duk yadda yake tunani abin ya wuce haka, hankalin sa ya kai ƙarshe wajan tashi akan rashin Manal, a haka ya kwana da duk inda ya san zai nema ta yayi amma babu Manal babu labarin ta. Kai da ka kalle shi ka san yana cikin damuwa, a haka ya yanke shawarar zuwa Abuja kawai gidan Alhaji Ahmad ko tana can.

Da safe asibitin yaje da niyar ɗauko maganin Rumana da Mama ta tuna masa a waya, ya ɗauko maganin ya fito suka haɗu da Huzaifa ya kalle shi shima ya kalle shi Huzaifa yace, “ya ake ciki Bebi? Jiya nayi waya ko ina amma Manal bata ɓangaren Daddy, ka tambayi ɓangaren Maman su?.”

Bebi ya kulle ido ya buɗe yace, “zan je Abuja yanzu dan ma ban samu jirgin safe bane da yanzu ina can, za je gidan Yayan su Maman ko Allah zai saka tana can.”
“Anya zata iya tafiya Abuja? Kar ka manta da daddare fa ta fita, ni nafi tunanin anya bata gidan su?.”

“Na faɗa maka Maman su ma magana take son tayi da ita, ai kaga baza ta yi min wasa da hankali ba ko?.” Ya girgiza kai alamun haka ne yace, “kuma wallahi bata gidan mu, Gashi su Daddy suna nan balle nace ko sun tafi Qatar da ita.” Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “zan je Abuja in sha Allah.”

Huzaifa ya kalle shi ganin ya canja gabaɗaya sai ya bashi tausayi, yayi rauni sosai da ka ganshi ka san yayi laushi hakan ya saka ya ce, “duk kayi wani iri, kar kaje su ga kamar su fahimci akwai matsala. Gashi in kowa yasan bata nan za a ga kamar baka kula da ita. Ace ta bar gida tun kwana biyar baya baka neme ta ba sai yanzu.” Bebi yace, “ni kaɗai nasan abinda nake ji Huzaifa, tashin hankalina bazai kwatantu ba wallahi. Nima bana so kowa ya sani musamman Maman ta, in ta sani hankalin ta zai tashi sosai ga yanayin ciwon ta.”

Huzaifa yace, “in sha Allah komai zai zo ƙarshe kar ka damu, yanzu kafin ka siyi ticket ɗin Abuja ka zo muje inda nake tunanin zata iya zuwa saboda suna da ƴan mata a gida, gidan ƙanin Daddy ne ko zuwan farko ta sake sosai anyi hira da ita kamar ta saba, wataƙila ko zata je can. Kaje ka dawo sai mu je.”

Bebi yace, “ina za je na dawo? Muje yanzu kawai.” Huzaifa yace, “bara mu yi sallar azahar sai muje.”
“Kaji matsalar ka, muje can nayi sallar kawai.”

Huzaifa yace, “akwai abinda zan ƙarasa yanzu, kaje ka dawo.” Bebi yace, “me zaka yi? Don Allah kayi hanzari mu je kawai.”
“Ni fa nace maka zamu je, kaje ka dawo kawai.” Bai ce komai ba ya fita ya bishi da kallo yana dariya. Hamza da yake kallon su yace, “ka tausaya masa don Allah ka kai shi ga matar sa.”

Huzaifa yayi dariya yace, “can zamu je, ai yayi laushi sosai ya kamata ace ya ganta.” Hamza yayi dariya ya wuce ciki shima ya wuce.

Ba jimawa Bebi yazo lokacin Huzaifa ya fito harabar asibitin ya kalle shi yace, “muje.” Motar sa ya shiga shima ya shiga tasa Huzaifa yayi gaba Bebi na bin sa baya yana fatan Allah yasa Manal tana gidan.

Ganin sun nufar hanyar gidan Huzaifa abin ya bashi mamaki bai magana ba sai da yaga Huzaifa ya shiga gida yayi tsaki ya ɗauki waya ya kira shi yace, “wai meye haka? Ni da zamu je wani waje meye na zuwa gidan ka?.” Huzaifa yace, “Daddy ne a gidan yace mu zo da kai, ka fito ku shiga ciki” yana faɗa ya yanke wayar. Bebi mamaki yake yi jin yace daddy kawai ya saka ya fito ya shiga cikin gidan. A ƙofar falon ya tarar da Huzaifa suka shiga ciki babu kowa a falon Bebi ya kalle shi yace, “Ina Daddyn? Ni ban yarda ma da batun Daddy yana nan ba kana yi min yawo da hakali ne kawai dan kaga ni nake nema a wajan ka.”

Huzaifa yayi dariya kaɗan zai yi magana kenan Manal ta fito daga ɗakin da take tana cewa, “Ayan yunwa nake ji duk kukan ka sai naci abinci.” Kallon wajan tayi inda suke taga Bebi yana kallon ta daga tsaye ta kalli Huzaifa da yake tsaye shima yana kallon ta.

Ganin kallon da take musu sai Huziafa yace, “zo ki zauna Manal.” Ta kalle shi tace, “Yaya Huzaifa ba haka muka yi da kai ba.”
“Na sani, dole ce ta saka ni na karya alqawarin ki. Ki zo ki zauna.”

Bebi kallon ta yake yi kafin ya kalli Huzaifa ya ce, “Amma kaci amanata, daman duk wannan yawon da nake yi ina neman ta tana gidan nan?.” Huzaifa yayi dariya yace, “tana gidan Yayan ta. Manal ki shiga ki ɗauko duk wani abin da kika sani na naki ne ki bi mijin ku koma gida.”
Chapter 59 · 0% Book details