← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 84

Sashe 79

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi dariya tana sake kwanciya a jikin sa ya riƙe ta ta sosai yace, “Shikenan burin ki ya cika kin samu ciki ko?.” Ta ɗaga masa kai tana riƙe da wuyan sa taana murmushi. murmushin shima yake yi yana kallon ta yace, “to sai mu fara kula dashi kafin Allah ya kawo mana shi duniya, shekara biyar ɗin dai da kika furta sai ta kusa zaki haihu. Allah yasa wannan ba irin cikin Ayan bane a fannin sha sugar, Allah yasa wannan irin wancan ne akan son maƙale min.” Tayi dariya tana kwanaciya a jikin sa cikin farin ciki.

Sai kuma ta tashi tsaye ta ɗauki waya ta dawo jikin sa ta zauna tace, “bara na faɗawa Mama.” Ya girgiza kai bai hanata ba dan yasan sai ta faɗa mata. Manal ta kira Mama tana ɗauka kafin Maman tayi magana Manal tace, “Mama ina da cikiiiiii!.” Mama tayi tsaki tace, “Manal yaushe zaki hankali ne wai ke? Wannan itace sallamar taki?.” Manal a shagwaɓe tace, “to Mama ba ke kike min faɗa akan ban haihu ba, na dage kuma na samo cikin shine na kira na faɗa miki.”

Mama ta sake yin tsaki tace, “kin kyauta da kika dage kika samo ciki kin ji, Allah ya inganta mara kunya” ta faɗa tana kashe wayar. Dariyar da yake riƙewa ya fara yi yana kallon ta. Baki ta turo tace, “dariyar me ka ke min?.”
Yace, “wato ni ki ke jin kunya amma Mama duk abinda yazo bakin ki faɗa mata kike yi. Wato kin dage kin samo ciki ko? To faɗa min irin dagewar da kika yi har kika samo.”

Manal ta kalle shi tace, “Nifa ba da wani abun na faɗa ba, shiyasa tace min mara kunya ashe itama abinda kayi tunani take nufi” sai tayi dariya tace, “ko da yake ai dagewar nayi, har sharaɗi aka saka min fa kuma na haƙura nabi sharaɗin. Anya ma kuwa ba ranar bane?.”
“Ba a ranar bane me?.” Ta juya ido sai kuma ta rufe idon tana dariya. Ya ja hancin ta yace, “ai jin kunyar tawa duk ta ƙarya ce, tunda gashi kina cewa Mama kin dage kin yi ciki.”

Manal tayi dariya tace, “zan je school fa, bara na tashi.” Ya zauna da ita yace, “yau dai a ƙyale school ɗin nan mu zauna mu yiwa Babyn mu barka da zuwa. Kafin nan ki saka hujjabin ki muje asibiti mu tabbatar da kwanakin sa ko?.” Ta amsa da to ta tashi ta shiga ciki ta ɗauko hijjabi suka fita.

Da suka shiga asibitin basu tarar da Huzaifa ba sai da ya nufi office, tana bayan sa bayan an gama yi mata scaning suka haɗu da Huzaifa zai wuce. Manal ta kalle shi tace, “Yaya ina yini.” Huzaifa yace, “A’a Manal kin yiniLafiya?.”
“Lafiya lau Yaya, ina Anti da Amna?.”
“Lafiya lau, yau kece a asibitin namu?.” Bebi ya kalle shi yace, “ji mana, ya zaka dinga magana da mayar mutum bayan baka nemi izinin mijin ta ba?.”

Huzaifa yayi tsaki yace, “Manal gab nake da nunawa wannan mijin naki ikon da nake dashi a kan ki, na lura yana wasa dani yana kuma mantawa ni babban Yyan ki ne, amma zan tuna masa.” Manal tayi dariya tace, “ya dai kamata Yaya.”

“Ɗazu naje wajan Mama ai, naje an gwada sugar ta.” Manal tace, “ta faɗa min kaje ba.”
“Indai naje sai an faɗa miki?.” Tayi dariya kafin tayi magana sai result ɗin ta an kawowa. Bebi ya karɓa kalle ta yace, “ba sai mun shiga bama ga abinda muke jira” ya faɗa yana buɗe takardar ya kalli fuskar ta ya sake kallon takardar sai yayi dariya bai ce komai ba ya ninke ya saka a aljihu.

Ya kalli Huzaifa yace, “meye ka ke kallona ne?.” Huzaifa yace, “kai da wanne ido ka san ina kallon ka?.”
“Ka dai taya mu murna mun kusa samun new baby ko partner?” Ya faɗa yana riƙo ta yana kallon ta. Mintsinin sa tayi a hannu, Huzaifa ya harare shi yace, “ina taya ƙanwata murna, Allah ya inganta mana.”

“Ƙanwar ka kawai ka sani kenan? Da yake ita ta…” da sauri tace, “partner wai meye haka? yaya Huzaifa ne fa, bana so irin haka ka daina don Allah.” Huzaifa yayi dariya yace, “kaga inda ake girmama Huzaifa, kar ki damu Manal indai wannan ne ai ya saba” ya faɗa yana wucewa shima ya ja hannun ta suka fito.

Sai da suka je gida take cewa, “Meyasa ka ke wannan maganar a gaban Yayana?.” Bebi yace, “ke takura min yake shiyasa nayi maganin sa, shi ai bai ɗauke ki ƙanwa ba.” Ya ɗauko takardar yana duba yace, “kin san date ɗin cikin nan yayi daidai da ranar Sunday ɗin nan.” Manal tace, “to daman an samu banza kuma ina so ba dole ba.” Murmushi yayi ya girgiza kai yace, “Au abun haka ne?, Shikenan zamu gani.” Dariya itama tayi ta tashi ta shiga ɗakin ta.

Bebi da Manal rainon ciki aka fara cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, makaranta ma ya saka ta daina jan mota kai ta ake ya ɗauko ta, gurki ma yace ta rage yi zai dinga taho musu da abinda zasu ci wani lokacin. A wannan cikin taba bin dokar shan sugar sai dai bata son warin gas ko kaɗan, hakan ya saka aka kulle shi aka ajjiye ta koma amfani da electric gas.

Kwance tashi ba wahala a wajan Allah Manal ciki har ya girma kuma cikin ikon Allah lafiy lau tana bin dokar ƙin shan abu mai sugar sosai. An yi scanning an tabbatar mace ce a cikin Manal ta fara kiran ta da sunan Maman ta dan tace sunan Mama zata saka shi kuma ya amince mata.

Cikin ikon Allah Manal ta haihu lafiya amma ta sha baƙat wahala fiye da haihuwar Ayan,sai dai Babyn da tazo da jendus sai da kwana uku a nursery sannan aka sallame ta suka dawo gida. A gida Manal ta cigaba da jegon ta da taimakon Addah Halima da tazo wajan ta take kula da ita.

Ranar suna yarinya taci sunan Maman Manal tayi mata laƙabi da Ayda. Satim Mama Halima uku a wajan Manal ta koma gida bayan ta bata kulawa sosai yadda ya kamata, ganin ta warke ta dawo daidai ne ya saka ta tafiya kasancewar ba haihuwar fari bace ba.

Mutanen Abuja kowa yazo har Daddy da kansa yazo har gidan yayi mata barka ya kawo kaya da abubuwa masu yawa matsayin sa na mahaifin ta. Rumana, Mubeena dukkan su sun zo duk da ba a yi taron suna ba amma sun zo sun yi mata barka sun tafi.

Bayan sati biyar da haihuwar tana zaune a falo tana ta yiwa Ayan faɗa akan wai sai ya ɗauki Ayda. A lokacin Adnan ya shigo yana amsa waya a lokacin da take cewa, “Wallahi Ayan zan dake ka, ina yi maka magana ka sake yi?. Baza ka ɗauke ta ba kuma kayi min kuka sai na dake ka wallahi.” Kashe wayar yayi saboda kukan Ayan ya kuma nufk wajan sa ya zauna a kan cinyar sa yana kuka.

Tayi tsaki tace, “ya cika shagwaɓa da kuka mara dalili.” Kallon ta yake yi cikin mamaki wai itace take cewa wani yana kuka mara dalili. Bai mata magana ba ya fara rarrashin Ayan har ya daina kuka yayi bacci a jikin sa. Kwantar dashi yaje yayi a ɗaki ya dawo ya ɗauki Ayda a kan cinyar ta yana kallon ta, dan wannan karon dashi take kama ba da Manal ba.

Bata kula shi ba dan shima haushin sa take ji ya kuma sani neman shiri yake shiyasa take share shi. Ya ajjiye Ayda akan gadon ta ya kalli Manal yace, “Haba Fatima na kuma Mummyn Fatima, har yanzu baki gama fushin ba?.” Ta kalle shi ta ɗauke kai yayi murmushi yace, “to yanzu me kike so na yi miki? Ai na faɗa miki komai ya wuce amma kin ƙi.”

Manal tace, “haka kawai ka dinga yi min faɗa akan abinda ba laifina bane, na faɗa maka in ranka ya ɓaci ya daina shafa ta amma ka ƙi. Ban san waye ya ɓata maka rai ba, ban san a inda aka ɓata maka rai ba amma kazo ka dinga yi min faɗa akan abinda ban san anyi ba.”
“To ai nace miki ya wuce ko?.”
“Ni a wajena bai wuce ba” ya faɗa tana kawar da kanta.

Murmushi yayi ya riƙo ta ya matse ta a jikin sa yace, “to me kike so nayi miki ki daina fushin?.” Ta kalli idon sa ya hura mata iska cikin idon ta, lumshe idon ta kuma buɗewa yace, “kina girma kina sake kyau.” Ta turo baki tace, “daɗin baki kawai ka ke min, ina kyau a wajan mai yara biyu? Kaine dai ka ke kyau shiyasa ƴan mata suke bin ka.”

Yayi dariya ganin ta sakko yace, “yara biyu ne fa dani, ina ni ina soyayya Fatima ta?!” Ya faɗa yana kai hancin sa wuyan ta. Ta ɗan ja baya tana kallon sa shima yana kallon ta yace, “ya dai? Yau dai dole a tausayawa Adnan, na gaji da zaman jira. Tunda ki ka haihu shikenan ki ka raba kan ki dani.”

Ta kalle shi tace, “nidai tsoro nake ji kar na yi ciki da wuri, na sha wahala a haihuwar Ayda wallahi, gaskiya bazan haihu ba sai nan da shekara….” Yayi saurin dakatar da ita yace, “kar ki faɗa da baki mala’iku, kinga haka wancan kika faɗa sai da biyar ɗin ta tabbata.” Ta kawar da kai yyai dariya yace, “Kina da abin mamaki, kince baza ki haifi Ayda ba sai nan da shekara biyar amma kafin lokacin kika tayar da hankalin ki ke kin zama juya, Allah ya baki yanzu zaki sake cewa ke baza ki sake haihuwar ba sai nan da wasu shekaru?.”
Chapter 79 · 0% Book details