← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 84

Sashe 5

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bily tace, "gaskiya wannan ba karamin abu bane ba, in ya kasance mahaifin ku keda Manal kenan fa babu aure tsakanin ta da Adnan fa, ga ciki ma take dashi. Subahanallahi wannan abin kunya har ina? Allah kar ka tabbatar mana da wannan lamari."

"Amin. Bazan zo a raba Manal da mijin ta ba, yana sonta tana son shi. Nima bazan zo ace mahaifina ne yaso mayar dani karuwa ba." Bily tace, "ki daina wannan maganar, in sha Allah babu abinda zai faru wannan maganar baza ta zama gaskiya ba."
"To waye mahaifin mu Bily? Ina dangin sa suke?."

Bily tace, "Allah masani, Amma tunda aka zo wannan gaɓar komai ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah, mu cigaba da addua kawai." Mubeena tace, "to Allah ya bamu abinda zamu iya. Ni yanzu ko ba mahaifin mu bane, ko ba wani namu bane, Manal ta koma wajan Adnan da wanne ido ma zan dinga kallo Adnan?. Kin san Allah wannan shine dalilin da ya saka tun asalin farko Adnan bai min ba, ashe dashi yake min kama shiyasa haka nan baya burge ni. Shi kuma mahaifin nasa ashe ƙarya yayi min ya faɗa min suna na ƙarya saboda kar na gane shi."

Ta sake kallon Bily tace, "Haba shiyasa lokacin da Mama bata da lafiya da ya ganni a asibitin su Adnan ɗin yace kar na sake zuwa, ashe ya san da ɗan sa a cikin asibitin, yana tsoron kar na san ɗan sa ko shi ya sanni. Yace min sunan sa Isah ashe Mu'azzam sunan sa. Ai in akace shine mahaifin mu sai nafi Manal shiga tashin hankali."

Bily tayi ajiyar zuciya tace, "ki yi addu'a kawai Allah ya sassauta mana wannan lamari." Ta amsa da amin kafin ta raka Mubeena ta wuce gida.

****** "Dr tun ɗazu nake neman ka na sanar da kai, i'm sorry cikin jikin ta ya fita sakamakon faɗuwar da tayi. Alhamdulillah ya zo da sauƙi har ta farka ma" wata nurse ta faɗa tana kallon sa da shigowar sa kenan asibitin. Ya sauke numfashi jin daɗi yace, "ya jikin ta?."
"Da sauƙi sosai." Bai ce komai ba ya shiga ɗakin da Maryam take ya same ta ita kaɗai ce kawai a ɗakin ya ja kujera ya zauna ya kalle ta yace, "ya jiki?." Bata amsa ba sai kuka da take yi ya sauke ajiyar zuciya yace, "wannan koke-koken duk ba naki bane a yanzu, ki yi facing abinda yake gaban ki don ganin kin warware matsalar. Ki kuma tuba ga wanda ya halicce ki domin mutuwa zata iya samun ki a ko wanne lokaci."

Maryam ta goge ido tana furta astagafirullah a zuciyar ta. Kallon ta yayi yace, "nutsu sosai mu yi magana." Ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta yace, "ga wayar Kamal a hannuna" ya faɗa yana nuna mata wayar, ya ɗauko hanun ta ɗaya da babu ruwa a jiki ya saka mata wayar yace, "ki shiga cikin wayar ki tabbatar kin goge komai, kar ki bar wani abu ko ɗaya a ciki, ki tabbatar kin goge domin kar ki sake aikata kuskure."

Kallon sa take cikin mamaki ya akayi ya samo wayar Kamal, bata da bakin tambayar sa ya ɗauke hannun sa daga kan hannun ta ta kalle shi tace, "da gaske wayar shi ce?."
"Zaki iya tabbatarwa." Da hannun ta ɗauka ta danna abinda ta san ya saka matsayin security na wayar sai kuwa gashi ta buɗe alamun bai canja ba. Numfashi ta sauke cikin farin ciki tace, "Bebi itace wallahi."

Bebi yace, "ki yi abinda zaki yi da gaggawa, za'a mayar masa da wayar bana so ya ɗora whatsapp ɗin sa ko facebook a wata wayar daban, ki yi hanzari har chart ɗin da kuka yi na yanzu da na da ki yi clearing." Hannu na tawa ta shiga whatsapp ɗin ta goge, ta shiga facebook ɗin sa ta tara ya goge duk wani post ɗin sa. wajan hotuna ta shiga amma bata ga komai akan abinda ya shafe ta, ta kalle shi tace, "Babu komai." Yayi shiru ya san za'ayi haka babu lallai ya ajjiye su a inda za'a yi saurin samun su, karɓar wayar yayi yana dube-dube a nan ya gano wata secret folder amma sai da face id zata buɗe.

Tashi yayi ya fita ba jimawa ya dawo shi da wani yaro da laptop a hannun yaron, ya zaunar dashi ya bashi wayar yace, "gashi ka duba min wata folder da aka ɓoye." Karɓa yayi ya jona wayar a laptop ɗin ya shiga danne-danne. Kusan mintina talatin yaron yana abu ɗaya kafin yace, "ga wata na gani mai suna Maryam." Adnan yace, "yauwa, bani" ya faɗa yana karɓa ya ɗora mata a kan cinya yace, "ki buɗe wannan mai sunan naki ki goge duk abinda yake ciki da gaggawa."

A hankali ta shiga tayi clicking sai kuwa ga hotunan ta da videos kamar hauka. Ganin yadda ta runtse ido ya tabbatar abinda suke nema ne yace, "ki buɗe ido ki goge." Da sauri ta buɗe tayi marking gabaɗayan su ta goge duka hannun ta har rawa yake yi. Ta kalle shi tace, "na goge." Ya ɗauke laptop ɗin ya bawa yaron yace, "A goge wannan folder ta yadda ko anyi backup baza ta dawo ba, sannan ko charting ɗin kan wayar a goge yadda bazai dawo ba." Yaron ya amsa yana cigaba da dannawa har ya gama yace, "an gama, na sauke komai." Bebi ya girgiza kai yace, "Na gode, koma office ka jira ni." Yaron ya fita shi kuma ya sake duba wayar yana sake dannawa dan so yake ya tabbatar babu koda hoton fuskar Maryam a wayar.

Kuka take yi sosai tana kallon sa yana aikin danna wayar tace, "na gode ɗan uwa, na gode Allah ya saka maka da alkhairi ya baka abinda ka ke." Ɗago ido yayi ya kalle ta bai yi murmushi ba yace, "amin. Nan gaba sai ki kiyaye turawa wani hotuna koda ya kasance mijin ki."
"Har abada Wallahi." Lubna ce ta shigo da sallama ya amsa yana kallon ta ta gaishe shi amsa yana fita.

Mubeena bayan ta koma gida a falo ta samu Mama tayi sallama ta amsa tana shiga ciki Mama tace, "shiga ɗaki ki gano min Manal tunda ta shiga bata fito ba." Mubeena ta shiga ta samu Manal a kwance ta ƙarasa ta zauna kusa da ita tace, "Manal lafiya?."

Jin muryar Mubeena sai ta tashi zaune da sauri ta riƙr hannun Mubeena tace, "Yaya na rasa abinda zan yi naji daɗi." Mubeena tace, "Kaii jikin ki yayi zafi sosai, me yake damun ki?." Manal tace, "komai ma damuna yake Yaya, na rasa inda zan saka raina, ji nake kamar na samu suka na dinga cakawa kaina har sai na mutu."

Mubeena tac, "to ki yi haƙuri, in sha Allah babu ƙaddarar da zata rabu ku da Adnan, kina son mijin ki shima yana son ki in sha Allah babu abinda zai faru. Na tabbatar duk inda yake shima yana nan cikin damuwa wataƙila tafi taki, ki yi haƙuri ki daina kuka kin ga zazzami ya rufe ki, babu abinda zai raba ku sai mutuwa."

"Kafin zuwan mutuwar ni na raba su" Mama ta faɗa tana shigowa ta kalle su ta kalli Manal da take kuka tace, "Manal kukan ki babu abinda zai miki magani sai dai ya ƙara miki ciwo, nice na haife ki kuma bazan yi abinda zan cutar dake ba ke kin sani. Tunda kika ji nace babu auren ki da Adnan ya kamata ki fahimce ni, ba da wata manufa na aikata hakan ba sai dan dole hakan ya faru. Adnan bazai zama mijin ki ba a yanzu ko nan gaba, wancan zaman ma da ku ka yi na anyi shi a rashin sani ne, amma yanzu komai bayyane dole ki rabu dashi!" Ta ƙarasa maganar cikin tsawa.

Manal bata ce komai ba tana jikin Mubeena tana jan numfashi cikin tsoro, Mama tace, "cikin da yake jikin ki da ina da iko sai na zubar dashi, kawai bana son aikata zunubi ne amma da baza ki haife shi ba wallahi."

Mubeena da mamaki tace, "kin bar mu a duhu Mama, Mun kasa gane inda kika nufa. Ki faɗa mana dalilin aikata hakan hankalin mu sai yafi kwnaciya, wannan tashin hankalin zai iya sakawa cikin ta ya zube gabaɗaya."
"Ai da zai zube ɗin haka nake so Mubeena, da ace cikin zai fita da nayi farin cikin da ban taɓa yin irin sa ba" ta kalli Manal tace, "malama ki taso kici abinci, tun safe babu abinda kika ci har azhar tayi, kizo kici abinci kafin ran ki ya ɓaci."

Manal jin Mama tana yin maganar cikin faɗa sai ta bar jikin Mubeena ta sakko daga kan gadon amma ta kasa tsayawa saboda ciwon kai. Baya tayi kamar zata faɗi Mubeena ta riƙr ta tace, "Sannu Mama, Mama ya kamata mu kai ta aisibiti jikin ta yayi zafi sosai."
"Damuwa ce da yunwa, zata warware da zarar taci abinci. Riƙo ta tazo taci abinci" Mama tana faɗa ta fita Mubeena ta fito da Manal ta zaunar da ita ta kawo mata tea da biredin su. Manal saboda Mama ta sha iya tea ɗin kawai, gashi yanzu bata iya sha saboda babu sugar daƙyar ta iya shanyewa ta kwanta a wajan tana sauke ajiyar zuciya.

***** Bebi bayan ya bar ɗakin da Maryam take office ya koma ya sallami yaron da yace ya jira shi ya zauna tare da kwantar da kansa akan table ya rasa abinda yake damun sa a zuciyar sa. Damuwar Manal ce ko ta Abba ko kuma ta Maryam?. Tun safe yake kiran Manal bata ɗauka hankalin sa ya gama tashi gashi ko text bata yi ba balle ya tabbatar tana lafiya.

"Bebi team work is ready, kai suke jira za'a yi wannan surgery ɗin da aka yi maganar sa jiya." Jin magana a kansa sai ya ɗago yaga Huzaifa ne da Hamza akansa a tsaye tace, "ayi replacing ɗina da wani, I can't do anything wallahi" ya faɗa yana mayar da kansa inda yake a ɗazu.
Chapter 5 · 0% Book details