← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 84

Sashe 68

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na sani ai. Amma na faɗa miki har yanzu ba kallon Yayan ki nake yi masa ba, kallon abokina Huzaifa nake masa ba wanda ku ke uba ɗaya dashi ba, zafin abin nake ji a raina amma kin kasa ganewa” Ya faɗa yana kallon ta fuskar sa a ɗaure.

Manal tayi murmushi tace, "to ni naga hakan ba komai bane, ko rungume ni yayi babu zunubin da Allah zai rubuta mana.”
“Oh haka ne ko? Yayi kyau.” Manal tayi dariya tace, “Ni kallon Yayana nake masa, kuma kaga muharramina ne harda shi a cikin wanda Allah ya lissafa su ga kwalliyata. Dan ya ganni da wannan shigar ba komai bane, ko mutuwa nayi zai iya yi min wankan gawa, kai ko ban mutun ba ko da raina in akwai lalura zai iya ganin tsaraici na.” Yayi ƙaramin tsaki baice mata komai ba yana runtse ido, ya san abinda tace gaskiya ne amma kishi bazai bar shi ya amince ba. Fata yake a xuciyar sa kar Allah ya kawo ranar da Huzaifa zai ga ko da gashin kanta ne balle tsaraici.

Tayi dariya ta matsa kusa dashi sosai tace, "haba my life partner, kishi ka ke da Yayana kenan?." Ya kalle ta yace, "eh wallahi! har yanzu bana kallon Huzaifa matsayin Yayan ki kallon abokina nake masa, ina mantawa dashi yayan ki ne indai ba maganar aka yi ba, shiyasa nake jin babu daɗi a zuciyata. Shi kuma da gangan yake yin wasu abubuwa duk dan naji haushi."

Tayi dariya ta ɗora kanta a kafadar ta tace, "mijina mai ƙauna ta a ko yaushe. Kayi haƙuri ka dinga kallon sa matsayin Yayana don Allah, ka daina jin haushi kaga daman abinda yake so kenan kuma gashi kaji haushin.” Ya kalle ta baice komai ba tayi masa kiss a kumatu tace, "ko kace nayi kyau duk kwalliyar nan saboda kai nayi " ta faɗa tana tashi tsaye ta tsaya a gaban sa.

Ƙin kallon ta yayi ta saka hannu ta ɗago da kansa sai ya kulle idon tace, "don Allah ka kalle ni." Bai buɗe idon ba ta dauke Ayan daga cinyar sa ta ajjiye shi a gefen ta maye gurbin Ayan ɗin a jikin sa ta riƙe wuyan sa tace, "baza kace nayi kyau ba?." Banza yayi mata bai ce komai ba amma a zuciyar sa ya yaba da kwalliyar ta sosai dan tayi kyau ɗin kawai haushi yake ji da Huzaifa yaga kwalliyar ta. Kallon fuskar sa take idon sa a kulle tana murmushi a hankali ta kai bakin ta kan nasa ta fara kissing

Buɗe ido yayi suka haɗa ido ya sake mayar da idon sa ya lumshe sai ta daina abinda take yi ta haɗa goshin sa da nata tace, "mijina mai kishi da yayana." Kallon ta yake yi shima yayi murmushi kaɗan baice komai ba.

Tashi tayi daga jikin sa lafin ta gama miƙewa ya dawo da ita jikin sa ya zagaya hannun sa bayan ta ya ɗora hancin sa wuyan ta yana shaƙar ƙhamshin ta mai daɗi da sanyi wanda baya cutar da halittar sa. Shiru yayi a haka baice komai ba tana jikin sa a zaune. Ayan ne ya fara kuka hakan ya saka shi ya buɗe ido itama shi take kallo ta kalli Ayan sai ta tashi daga jikin sa ta zauna a kusa dashi ta ɗauki Ayan ta ɗora shi a kan cinyar ta.

Tashi yayi ya bar falon ita kuma ta fara shayar dashi. Ya ɗan jima kafin ya dawo ya samu har ta cire shi daga nonon ya kalle ta ya ce, "dole ya dinga yawan kuka bakya tsayawa ki bashi yadda ya kamata, da kin fara sai ki cire kamar naki." Ta kalle shi tace, "to da na waye?."
"Saboda ki shayar dashi Allah ya yi shi a jikin ki ba don kwalliyar ko dan ado ba, ko dan.." ya faɗa yana kallon ta itama shi take kallo tace, "cigaba mana, ko don me?."

Samun kasan yayi da murmushi mai sauti harda shafa fuskar sa ya kalle ta kawai suka yi dariya a tare. Ya tsagaita dariyar ya ce, "wait! dariyar me kike yi?." Tace, "kaima dariyar me ka ke yi?."
"Ina da dalilin dariya ta."
"Nima ina dashi." Ya matso ya kalli Ayan ɗin ya ce, "har yayi bacci kenan, sai na anjima kuma in ya farka."

"Wannan a rubuce yake" ta faɗa tana tashi tsaye ya karɓe shi a hannun ta ya wuce ya kai shi ɗakin sa bai ce komai ba. Ɗakin ta ta shiga ta cire ɗankwali ta ajjiye kenan ya shigo ya kalle ta yace, "au kwalliyar da ban gani ba zaki cire?." Ta kalle shi cikin shagwaɓa tace, "to ba ka ƙi cewa nayi kyau ba."
"Ba Yayan ki kika nunawa kwalliyar ba?.” Tayi murmushi ya ce, “Allah Manal har yanzu zuciyata bata kallo Huzaifa matsayin yayan ki, abokina Huzaifa a haka nake kallon sa. Kishi nake yi dashi sosai, a duk sanda ku ka haɗu naga kina yi masa murmushi zuciyata bugawa take yi.”

Tayi murmushi ta zagaya da hannun ta ta riƙe kugun sa tace, "to yanzu so ka ke kace min har yanzu sharaɗin ka akan sa yana nan?."
"Da hakan zai faru da naji daɗi."
"Inaaa! kaima kasan wasa ka ke Partner. Sharaɗin ka akan Huzaifa ne, wannan kuma Yaya Huzaifa ne Yayana na jini."

Ya taɓe baki yace, "to naji ya zan yi?." Ya faɗa yana kallon ta. Ta taɓe baki tana ɗage gira sama. Sakin sa tayi ta taka zuwa wajan madubin ɗakin ya bita da kallo yace, "kin yi kyau sosai, kayan nan sun miki kyau." Tayi murmushi ta juyo ta kalle shi tace, "na gode mijina."
"Daman kin zama ƴar lukuta shiyasa komai ya fito a kayan, kin yi caras dake ƴan mata." Manal tace, "ni bana ganin ƙibar nan da kake faɗa."
"Ai kam kin yi ƙiba, har mamaki nake saboda nasan ciwon ku baya bari kina ƙiba amma ke gashi kin yi."
Tayi dariya kawai bata ce komai ba yace, "abincin ɗazu yayi daɗi sosai, in akwai saura a ajjiye min gobe naci."

Da sauri ta kalle shi ya wara idanu yace, "eh a ajjiye min zan ci." Tayi dariya tace, "kai da kanka zaka ci abincin da ya kwana kuma?, Ka manta baka maimaici ne?.”
"Gori za’a yi min kenan?."
"A'a ni na isa."
"To ayi abinda nace."
"Wallahi babu ko kaɗan."

Ya ɗan yi tsaki ya kalle ta tana dariya yace, "to tsayuwar me kike yi wai? Muje a faɗa min kallon da ake yi min yau na meye." Manal tace, "to jirani na cire kayan nan sun ishe ni."
"Ko kin saka wani suma cire su zaki ki, zo muje bana son iyayi" ya faɗa yana jan hannun ta suka fita daga ɗakin.

     Washe gari.

Bai fita ba sai sha ɗaya na safe shima dan yana da abin yi ne da babu abinda zai fitar dashi a wajan mtae sa zai zauna su kwashi roman soyayya. Asibiti yaje lokacin da yaje Huzaifa da Hamza babu kowa dan haka bai bi ta kansu ba aikin sa yake yi.

Yana zaune a cikin office bayan sallar azahar Huzaifa ya shigo yana cewa, "Mijin ƙanwata ashe kazo." Ɗago ido yayi ya kalle shi Huzaifa yayi dariya yace, "kana ji, Hamza baya jin daɗi yana kwance a gida in mun tashi sai mu biya mu duba shi ko?."

Bebi yace, "Allah ya nuna mana lokacin." Ya amsa da amin ya kalle shi yace, "baka zo da wuri ba shiyasa na ɗauka ma baza ka zo ba, har zan kira ka sai aka ce min kazo.”
"Ban yi niyar fitowar bane bama wallahi, kawai dole ce ta fito dani. Dr Fulani yana nan?a kwai file ɗin da nake so a kai masa."  Huzaifa yace, "tunda ya fita bai dawo ba gaskiya."
"Okay" ya masa a taƙaice yana ɗaukar wayar sa.

Knocking ɗin ƙofar aka yi Huzaifa ya amsa aka buɗe aka shigo. A tare suka kalli wanda ya shigo Huzaifa ya kalli Bebi shima ya kalle shi ya sake kallon wanda ya shigo har ya mayar da ƙofar ya rufe ya tako a hankali cikin office ɗin.

"Mujahid!" Huzaifa ya faɗa da mamaki yana kallon sa. Mujahid ya miƙa masa hannu alamun su gaisa, bai bashi hannun ba ganin hakan Mujahid sai ya janye hannun sa daga gaban Huzaifa ya miƙawa Bebi hannu, Bebi ya harari hannun nasa yace, "wato kaga ka aikatawa ƙanwata laifi na barka ka cigaba da yawo a duniya ban kai ka prison ba shine ka samu damar zuwa inda nake?."

Mujahid ya sauke ajiyar zuciya yace, "Adnan ya haƙurin rashin Abba da muka yi?. Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa.” A laɓɓan Bebi zaka san ya ce amin Mujahid yace, Adnan don Allah kayi haƙuri, na ssn na ɓata maka rai akan ƙudurina na banza da wofi, don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min abinda nayi maka. Nayi nadamar abinda na aikatawa Lubna wallahi, tunda na bat wajan ta bani da kwnaciyar hankali har yau, don Allah kayi haƙuri ka saurare ni."

"Haƙuri ka ɗin banza da wofi, kai har kana da zarrar da zaka zo gabana kana cewa nayi haƙuri? Ka manta abinda ka yiwa ƙanwata ne?."
"Ban manta ba, rashin mantawar shine ya kawo ni yanzu gare ka. Don Allah don Annabi ka yi haƙuri ka yafe min, nayi nadamar abinda na aikata mata, nadamar da na yi a zuciyata itace ta saka na kasa mantawa da ita har sak da nazo yanzu duk da ba na san ɗauki lokaci. Kayi haƙuri don Allah."

Adnan ya kalli Huzaifa da ya kasa magana ya sake kallon Mujahid kafin yayi magana yace, "Wallahi Lubna ce mace ta farko da nayi nadamar abinda nayi nata, itace mace ta farko da naji babu daɗi akan abinda na aikata mata. Itace nace ta farko da nake ji a zuciyata in bata yafe min ba kamar wani abun zai iya faruwa dani. Shiyasa nazo gare ka kafin naje gare ta, don Allah ka yafe min komai ya wuce."
Chapter 68 · 0% Book details