← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 84

Sashe 81

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskar ta ya kalla yaga duk ta canja kamar mara lafiya yace, “Manal lafiya ki ke?.” Ta kalle shi ta sauke ajiyar zuciya tace, “Don Allah Yaya wacece Dr Zainab?.” Huzaifa ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “wacce Dr Zainab?.”
“Wacce taje asibitin ku jiya.”
“Jiya da daddare bana asibiti, amma daga ƙasar waje tazo?.” Manal tace, “ina tunanin hakan.” Huzaifa yace, “Dr Zainab babbar illikita ce a ƙasar Canada, tana zuwa asibitin mu in muka buƙaci hakan musamman a ɓangaren zuciya dan ƙwararriya ce sosai. itace tazo kenan?.”

“Eh tazo tun jiya, a nan gidan ma ta kwana.” Huzaifa ya girgiza kai dan ya san dole Manal tayi kishi da ita.
Zainab a gaban kowa nunawa take yi Adnan kamar wani saurayi ta ne saboda ita a wajan ta ba komai ba ne. Kuma a baya ta so shi ɗin kawai bai bata fuskar soyayya ba ne saboda lokacin yana tsaka da ƙaunar Rumana, sai dai zumunci da kuma abota akan aiki. Manal tace, “Kuma Yaya don Allah babu wani abu a tsakanin ta da Partner?.”

Yayi dariya yana kallon ta yace, “ban da abin ki Manal wanne abu ne a tsakanin su?, Kawai jinin su ya haɗu sosai tun ɓuna makaranta, kuma ta girme mana dan ba mate ɗin mu bace ko a makaranta. Muna level two ita a lokacin level four take. Kawai tana da kirki ne kuma jinin su ya haɗu da mijin ki.”

Manal ta taɓe baki ta sauke ajiyar zuciya idon ta ya ciko da hawaye, ganin hakan sai Huzaifa yace, “kar ki wani damu fa babu komai kin ji?.” Ta ɗaga masa kai ya tashi yace, “zan je asibiti yanzu.” Manal ta tashi tsaye itama tace, “to Yaya a gaida Anti, zan zo in sha Allah.” Ya amsa yayi mata sallama ya tafi.

Asibitin ya wuce ya samu Adnan a tsaye yana magana da wasu masu jinya ya kalle shi yace, “Bebi in ka gama..” ya faɗa yana yi masa nuni da hannu kafin ya wuce ciki. Sai da ya gama abinda yake yi sannan ya hau saman wajan Huzaifa ya same shi a tsaye shi da Hamza da Dr Yasir mijin Lubna da Dr Hadiza suna magana.

Ya tsaya yana kallon su bai ce komai ba, Yasir ya kalle shi yace, “Babban Yaya barka da zuwa.” Adnan yayi ƴar dariya yace, “shiyasa ka ke yin albarka saboda girmamawa yayan makat ka da ka ke yi.” Huzaifa yace, “shiyasa wani baya albarka saboda raina yayan matar sa da yayi.” Bebi ya harare shi yace, “me zaka ce min ka saka ni nazo na?.”

Hamza yace, “gaskiya baka kyautawa, ya Yasir zai dinga girmama ka kai kuma baka girmama Huzaifa?, gaskiya hakan bai daidai bane.”Kallon banza ya yiwa Huzaifa aka yi dariya Yasir da Hadiza suka fita suka bar su su kaɗai.

Huzaifa ya kalle shi yace, “Zainab ɗin ta wuce ne?.” Bebi yace, “ta tafi. tace min Abuja zata je, taso mu na raka ta kawai baza je ba.” Hamza yace, “ai shige maka ɗin da take yi yayi yawa, ta san kayi aure ma baza ta ƙyale ka ba. Har yanzu tana son ka, bata ƙi kace zak aure ta ba.”

Bebi bai bashi amsa Huzaifa yace, “ashe a gidan ka ta kwana.” Ya kalli Huzaifa ta ƙasan idanun sa yace, “a nan ta kwana, sai ya ya?.”
“Amma ka san bai kamata ka kaita gidan ka ba. na farko dai Zainab tana acting kamar kai da ita soyayya ku ke yi, duk da kowa ya san tana sonka amma nunawa take kaima son ta ka ke, na biyu kai ka san ba wani tarbiyya kirki ne da ita ba, ta girma amma kallon kanta take a yarinya mai ɗanyen jini. Kuma ka san ana zargin ta da lesbian tun a makaranta.”

Adnan ya kalle shi yace, “to ina ruwana ni?.
Magana ce akan aiki ya saka na gayyato ta tun daga Canada tazo ƙasar nan tayi theater saboda ni kawai, in ban sauke ta a gidana ba a gidan wa zata sauka?. Ina ruwana da zargin ta da ake yi?, Ni ban taɓa gani tana yi ba kaga bazan tabbatar da abinda ban sani ba.” Ya sauke ajiyar zuciya Hamza yace, “amma matar ka baza yaji da daɗi ba saboda wannan shegen iyayin Dr.”

Adnan yayi tsaki ya kalle Huzaifa bayan ya riƙe ƙugu yace, “Wai Manal ce tace maka na kai ta gidana?.”
“Tambayata tayi wacece ita nake faɗa mata. Da yake na biya ta gidan naka kafin nazo nan.” Yayi tsaki yace, “mata suna da matsala, yanzu meye aibu dan na kai ta gidana ta kwana don Allah?. Bafa da ɗaki ɗaya muka kwana da ita ba, amma ita tunanin ta kawai budurwa ta ce, ba’a mutunci sai soyayya. Ni na gayyato matar nan tun daga wata ƙasa kuma tazo, ai ta cancanci karramawa fiye da haka a wajena.”

“Ba matsala bace ba fa Adnan, dole ko wacece tayi kishi da Zainab. Kar ka manta Rumana da ba matar ka ba tayi kishi da Zainab a shekarun da suka wuce, to ina ga Manal kuma matar ka?.” Huzaifa ya kalli Hamza da yayi magana yace, “kuma ni ba ƙarar sa ta kawo min ba, tambaya ta take yi akan Zainab ni kuma na bata amsa.”

Bebi ya taɓe baki yace, “daga baya kenan, in ma ƙarar tawa ta kawo maka ai ba duka zaka yi ba ko?. Kuma ka faɗa mata bazan fasa ajjiye baƙuwa a gidana ba, ba Zainab ba; ko wacece in nayi ra’ayi zan kai ta gidan ta kwana. Na gayyato mata tun daga Canada tazo dan ta kwana a gidana a dinga yi min ƙananun magana?.”

Hamza yace, “Kai dai ka sani, amma tsakani da Allah dole tayi kishi da ita, dan a wajan Zainab dan ta rungumee ka a gaban Manal ba komai bane.” Yayi tsaki ya cigaba da aikin sa yana jin haushin Manal a zuciyar sa dan shi bai ga wani aibu ba da har zata faɗawa Huzaifa.

Koda ya koma gida fuskar sa a ɗaure ya koma
babu fuskar da zata yi masa magana sai ta share shi itama ta ajjiye masa abinci amma bai ce mata komai ba itama bata ce ba. Tana kwashe kayan abincin bayan ya gama ci yake cewa, “shine harda faɗawa Huzaifa wai nazo da ɓakuwar gidan nan, to me Huzaifa zai yi min? Duka na zai yi ko me?. Ko kina ganin faɗawa Huzaifa zai hanani saukar baƙuwa a gidana ne?.”

Kallon sa tayi bata ce komai ba ta kwashe ta bar masa wajan. A haka suka kwana bata ce masa komai ba shima haka sai dai duk abinda ta san yana so zata ajjiye masa amma magana bata haɗa su.

A haka aka kwana biyu tana yi masa wannan hukuncin da bai fahimta ba sai daga baya, ya jure shiru nata har ya gaji, in yayi mata magana daga eh sai a’a kawai, ta canja kamar ba ita ba ko dariya bata yi. Ko a falo suka haɗu zata bashi hanya ya wuce itama ta shiga inda zata je, in maganar ta zama dole sai dai tayi masa text a waya amma ba ta fatar baki ba.

BDƘB3P51

A ranar alhamis yayi nufin zama da ita yaji meye matsalar, hakan ya saka shi ya dawo daga aiki da wuri duk da dare yayi ya same ta tana waya da Maman ta da take Jalingo taje ziyara. Bayan ta gama ne ta kalle shi fuska ba yabo babu fallasa tace, “sannu da zuwa.”

Ya amsa yana kallon ta kafin ya ce, “ki kawo min fruit ɗaki” ya faɗa yana shiga ɗakin. Manal ta miƙe ta kwantar da Ayda da tayi bacci a hannun ta ta shiga kitchen haɗa masa fruit salad ta kai masa ɗakin kamar yadda yace. A zaune ta ganshi yana danna laptop ta ƙarasa ta ajjiye masa a kan table ɗin da yake aikin.

Wucewa tazo yi ya riƙo hannun ta a tausashe yace, “zo ki zauna.” Bata yi musu ba ta zauna fuskar ta babu walwala ko kaɗan. Yabi fuskar ta da kallo kafin ya ce, “Duk akan na kawo Dr Zainab gidan nan ta kwana ki ke wannan fushin Manal?.” Shiru tayi bata yi magana ba ya ce, “Partner dake nake magana, duk akan Zainab abin ya zama haka?. Magana ma sai kin ga dama ki ke yi min?.”

Manal tayi ƙaramar ajiyar zuciya tace, “akan ne zan yi fushi kai da gidan ka?, Gidan ka ne kana da ikon kawo duk wacce ka ke so.” Kallon ta yayi yaga fuskar ta a haɗe babu alamun walwala da alama bata huce ba, ya ture laptop ɗin gaban yace, “to meyasa kike fushi har na kwana uku?. bakya yi min magana, bakya dariya, wani lokacin in na dawo da daddare ma sai na tarar kin yi bacci. Fushin na meye haka?.”

“Ba fushi nake ba fa.”
“To me ki ke yi?.”
“Kawai na janye jiki na ne saboda baga baƙuwar taka ta fini a wajan ka.” Yayi murmushi yace, “ya za’a yi baƙuwata ta fiki Manali?.”

Ta taɓe baki bata ce komai ba ya gyara zama ya ƙce, “tun daga ƙasa Canada tazo saboda na gayyato ta tazo mu yi wani aiki tare a asibitin mu, ta amsa gayyata tazo kinga dole na girmamata nayi mata abinda nan gaba in na sake nema zata zo. In ba dan ni ɗin ba ganin ta ma wahala yake yi, amma ta taso daga wata ƙasa tazo nan kawai dan ta fito da martabar asibitin mu, kinga ta cancanci na sauke ta a gidan nan ko?.”
Chapter 81 · 0% Book details