Sashe 47
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun ta ta wanke tare da bakin ta, ta shiga kitchen ta ɗebo abinci tazo kusa da Mama ta zauna tana ci. Mama ta bita da kallo tace, “ya kamata ki fara shirin komawa gida kuma ko? Magriba tayi.” Manal ta amsa da to ta gama cin abincin ta koma ɗaki.
Bayan sallar i’sha Manal na tsaye tana cewa, “Mama kiran sa nake bai ɗauka ba.” Mama tace, “ya kamata dai ki wuce ki tafi, kar kuma ki sake fitowa sai kin kwana arba’in. Wannan jego na zamani sao shagwayi kike a unguwa ko kwana arba’in baki yi ba, yau kina nan kina can ko ɗan wankan jegon ma bakya yi. Sai wani na towel shima kuma dan iyayi wai babu ruwa mai zafi.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai.
Sallama aka yi aka shigo gidan duk suka amsa Manal ta fito tsakar gidan dan taga su waye. Idon ta akan Daddy ya fara sauka da Abban su Bebi ga yayyen Mama da suka zo suma gabaɗyan su dan suna da matuƙar yawa sosai. Manal tace, “Sannun ku da zuwa.” Mama ta fito tsakar gidan ta kalle su dukkan su sai tayi murmushi tace, “Sannun ku da zuwa, Mubeena zo ki shimfiɗa mana tabarma mu zauna a nan.”
Mubeena ta fito da babbar tabarma aka shimfiɗa a tsakar gidan kasancewar da haske sosai kuma yanayin garin na zafi ne. Mama ta kalle su tace, “bismillah.” Mamakin canjin ta kowa yake yi mazan suka zauna aka sake saka wata tabarmar matan kuma suka zauna suma.
“Barkan ku da dare” Mama ta faɗa tana kallon kowa da yake wajan. Yaya ta Alhaji Ahmad yace, “Barka dai Zahra, ya ƙarfin jikin ki?.” Tayi murmushi tace, “Jiki yayi sauƙi sosai ai Yaya, na samu lafiya.” Kallon ta yayi jin da sunan da ta kira shi, yaji sanyi har cikin zuciyar sa farin ciki ya mamaye ko ina a tare dashi yace, “Allah ya ƙara lafiya ƙanwata.”
Mama tayi murmushi tace, “Amin Yayana.” Ta kalli matan da suke zaune dukkan su Yayyen ta ne tace, “cikin ikon Allah babu wacce na manta sunan ta ko fuskar ta duk tashon wannan shekaru da aka kwashe bamu haɗu ba, kuma nima nayi mamaki da har kuka iya gano fuska ta akan fuskar Manal.”
Babar yayar su mace wacce suke cewa Yaya Bara’atu tace, “Kin taɓa ganin ɗam uwa ya manta da fuskar ɗan uwan sa? Ko kin taɓa ganin in da hanta da jini suka rabu?” Ta riƙe hannun Mama tace, “duk da lokacin da komai ya faru ni bana cikin gidan, ko nace kusan dukkan mu bama nan keda Halima ne da Hadiza kawai tunda ku ne ƙananu, amma ni ma na nuna miki rashin so da ƙauna ƙanwata. Wannan hali da muke nuna miki ba komai bane face haka muka tashi muka ga ana yi, dukkan mu bamu da laifi a kan turbar da aka ɗora mu kenan, amma don girman Allah….”
Mama tayi saurin tarar numfashin tace, “Haba Adda wannan maganar ta wuce har cikin zuciyata, na dawo cikin ƴan uwana da na rasa shekaru masu yawa da suka wuce. Ki ɗauka kamar ɓata nayi aka neme ni aka rasa yanzu kuma na bayyana, kar ki wani tunani a zuciyar ki ki ɗauka hakan ce ta faru.”
Kowa kallon ta yake yi cikin farin ciki da walwala tayi murmushi tace, “daman bani da kowa sai ku, ban taɓa sanin inda dangin Gwaggona suke ba, har ta bar duniya ban yi wani wayon da zan tambaye ta ina suke ba balle na san su. Ku kawai na sani, ku kawai nake kallo matsayin ƴan uwa kuma komai nawa. Lokacin da na rasa iyayena bani da kowa dai sai ku ɗin kawai, har yanzu har gobe ku ne ɗin ne kawai dani bayan ku bani da wasu.”
Adda Halima tazo ta riƙe hannun ta tace, “ana jima ina neman ki, nayi kukan rashin ki, naji ciwon rabuwar mu duk da bamu da shekaru a lokacin.” Mama ta kalle ta tana dariya kaɗan tace, “Adda Halima yanzu na dawo duk da shekaru sun tafi, babu lallai ma mu kai gobe a duniya, amma in Allah ya ara mana numfashi muna tare daga nan har Allah yayi ikon da akan kowa.” Halima ta rungume Mama cikin farin ciki tana kuka.
Mama ma hawaye take yi ta ɗago ta daga jikin ta tace, “Komai ya wuce, na yafewa duk wani wanda yayi min ba daidai ba” ta kalli Daddy da yake zaune yayi shiru kamar mara lafiya shi da Huzaifa ne kawai ko Bebi babu kuma Abban su Bebi yana nan. tace, “Har kai mahaifin su Manal, komai ya wuce na yafe maka, sannan ga yaran ka nan Nusaiba da Fatima kamar yadda ka sani, Fatima tayi aure harda yaro Nusaiba ma an saka ranar auren ta.”
Daddy farin ciki hana shi magana yayi, ya rasa abinda zai ce kana kallon sa ka san ya ruɗe saboda abinda yake nema ya samu. Ya kalli Alhaji Ahmad yana cewa, “Ku taya ni godiya ta yafe min, Ku taya ni yi mata Godiya, nayi mata abubuwan da yawa, bancancanci a yafe min ba, amma tace ta yafe min Ku taya ni gode mata.” Yayan ta ya kalle shi yana jin ciwon labarin da Daddy ya bashi akan abinda yayi mata, amma in ya tuna su ƴan uwan ta sune suka fara barin ta sai ya rasa bakin magana.
Mama tayi murmushi tace, “babu komai kar ka damu komai ya wuce, na yafe maka saboda Allah da kuma alfarmar Huzaifa..” Daddy yace, “Na gode sosai, Allah ya jiƙan Gwaggo da Baba, Allah ya gafartawa duk wanda kika rasa a rayuwar ki.” Mama ta amsa da amin kowa ma ya amsa addu’ar.
Alhaji Ahmad ya kalli Manal da take ta goge hawaye yace, “Ke ce Fatima?.” Manal ta kalle shi ta girgiza kai yace, “Fuskar ta sak kanwata Zahra, amma hasken na a Gwaggo ne.” Mama tayi murmushi ya sake kallon Manal yace, “ku zo kusa dani.”
Tasowa sukayi Ayan yana hannun Adda Halima daman suka ƙaraso suka zauna a kusa dashi ya riƙe hannun su yace, “Allah ya yi muku albarka, Allah ya raya ku ya bamu zuciya irin ta mahaifiyar ku.” Suka amsa da amin kafin ya kalle su yace, “mu nan duka iyayen ku ne, baku da ya fi mu a duk duniyar nan, duk abinda kuke so daga yau ku sanar dani, komai tsadar sa komai wahalar samun sa nayi alqawarin mallaka muku shi.” Mubeena tayi murmushi tace, “İn sha Allah.” Yaya Bello da Alhaji Abubakar ma kamar zasu cinye su, haka sauran mazan guda biyu da suke zaune.
Manal ta kalli Huzaifa da yake gefe ta kalli mahaifin sa sai ta tashi ta koma kusa dashi tace, “Daddy ka daina kuka, komai ya wuce bana so naga kana zubar da hawaye.” Da sauri ya kalli Manal sai yaga tana murmushi ya kalli Huzaifa da yake gefe shima yana murmushi ya sake kallon Manal yace, “da wanne suna kika kira ni?.” Manal ta sake yin murmushi tace, “Daddy nace.” Kawai sai ya sake fashewa da kuka, Manal ta riƙe hannun sa duka biyun tace, “Don Allah Daddy ka bar kuka yana karya min zuciya” ta faɗa muryar ta na rawa sosai alamun zata yi kuka.
“Eh Daddy, ka daina zubar da hawayen ka hakan yana sakawa muji babu daɗi” Mubeena ta faɗa tana dawowa kusa dashi. Farin ciki ya yiwa Daddy yawa ya rasa inda zai saka ransa saboda murna, ya rƙe su a jikin sa cikin zallan farin ciki yace, “na gode ƴaƴana, Allah ya yi muku albarka, na gode sosai, na gode, Allah ya faranta muku.” Manal tace, “Amin Daddy, ka daina yi mana godiya mu fa ƴaƴan da ka haifa ne.” Daddy ya sake kulle idon sa yana hawaye saboda farin cikin da yake zuwa zuciyar sa da gangar jikin sa.
Manal ta kalli Huzaifa da yake kallon ta yana murmushi tace, “Yaya Huzaifa ashe yayan da nake cewa ta jini ce ba ta kara ba.” Yayi murmushi yana kallon ta ya kasa cewa komai ganin abun yake kamar a mafarki.
Mama ta sauke ajiyar zuciya so take tayi maganar dukiyar yaran ta amma kuma sai bakin ta ya sarƙe ganin yadda yaran suke wajan sa kamar zasu ji babu daɗi in ta yiwa mahaifin su haka. Ɗuke kai tayi bata ce komai ba.
Alhaji Ahmad yace, “Yaushe zaku zo Abuja?.” Manal ta kalli Mama itama ta kalle ta tace, “meye zaki kalle ni? Zan hana ki ne?.” Manal sai tayi murmushi tace, “Duk sanda aka shirya zamu zo.”
“Ya kamata dai, sannan ina so ku je har Jalingo akwai dangi sosai a can duk su gan ku. Gidajen ƴan uwan mu duk za’a zaga a san ku.” Manal ta girgiza kai tace, “in sha Allah zamu zo.”
Adda Halima tace, “daman ni maƙociyata ce ke Manal, waje ɗaya muke zama in nazo Kano, dan haka yau sai kin shiga gidana.” Manal tayi murmushi tace, “To Mama.” Mama ta kalli Yayan ta tace, “a kaf duniya bani da wanda ya taimaka min kamar wannan bawan Allah, a lokcim da nake Zaria shine ya ɗauko ni ya taho dani Kano bai sanni ba ban san shi ba, ya kai ni wajan maahifiyar sa ta riƙe ni hannu biyu, Manal da Mubeena kuwa ta riƙe su kamar jikokin ta. Ita ce ta bashi shawarar aurena duk da lokacim yana da mata guda biyu, ya kuma amince ya karɓi shawarar hannu biyu.”