← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 84

Sashe 70

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari ya tashi da mura da ta saka masa ciwon kai, bai fita ba yana gida a kwance dan sosai kansa yake ciwo. Manal tana zaune kusa dashi ta taɓa jikin sa tace, “Partner jikin ka yayi zafi, kaci abinci ka sha magani.” Bai iya yi mata magana ba yana kwance sai ta fita ba jimawa ta kawo masa kunu a kofi.

Zama tayi kusa dashi tace, “ga kunu ka tashi ka sha sai ka sha magani.” Daƙyar ya tashi zaune ta matsa kusa dashi sosai ta saka masa kofin a baki ya sha kaɗan yace, “ya ishe ni, bani pcm na sha.” Tashi tayi ta kawo masa ya sha ta sake taɓa wuyan sa taji da zafi sosai. Ƙin sakin hannun ta yayi ya riƙe shi a wuyan ta yana jin sanyin hannun ta.

Tashi tayi ta rage kayan ta ta ƙarasa kan gadon ta zare ƙaramar rigar jikin sa ta maye gurbin rigar a jikin sa. A hankali yake jin daɗi sanyin jikin ta yan shiga jikin sa a haka bacci ya ɗauke su.
Da ya farka yaji daɗi babu laifi Manal sai lalaɓa shi take shi kuma hakan daɗi yake masa. Kwana biyu yayi a kwance har da masu zuwa dubiya dan shima mai yi ne.

Ranar da ya ji sauƙi ya fita asibitin yaje ya gama abinda zai yi ya dawo gidan su. Abinda ya bashi mamaki mazan gidan nasu suna nan duk da kasancewar yamma ce. Yana ajjiye motar ya shiga wajan Mama ya samu bata nan babu kowa a ciki, fita yayi ya shiga wajan Mamy a nan ya same su gabaɗayan har da Farida da Mimi da alama meeting suke yi.

Ganin sa sai Yaya Isma’il yace, “A’a Adnan ashe ka warware?.” Adnan ya ƙarasa shiga ciki yace, “eh na samu sauƙi, tun safe ma bana nan. Wai taro ku ke yi yau ban sani ba? Ke Lubna meye ya saka ki kuka kuma?” Ya faɗa yana kallon ta.

Yaya Bilal yace, “zauna zaka ji duk abinda ya tara mu a nan.” Zama yayi a akan kujera kamar yadda suke yace, “Allah ya dai lafiya dan naga Lubna tana kuka.” Mamy tace, “magana ake akan auren Lubna.” Bebi yace, “har ta samu miji bani da labari? A ina yake?.”

Yaya Bilal yace, “Mujahid ne ya takura mana da sintiri da magiya da koke-koke, jiya har yayan sa ya turo min akan ayi haƙuri a bashi auren Lubna. Shine muka taru a nan dan mu yi shawara.” Adnan ya kalle su da mamaki yace, “To Yaya Bilal meye amfanin zama akan Mujahid don Allah? Me ake tattaunawa a kan sa?.” Yaya Bilal yace, “to Adnan Mujahid dai shine ya yiwa Lubna fyaɗe, kuma saboda wannan tabo ko nace tambarin ya saka aka fasa auren ta a wancan lokacin. Shine muke ganin tunda yayi nadama ya kuma gane kuskuren sa me zai hana baza mu bashi auren ta ba?.”

Wara idanu Adnan yayi cikin mamakin abinda ya ce, “a bashi auren ta kace fa Yaya? Auren Lubna ɗin za’a bawa Mujahid?.” Yaya Isma’il yace, “tattaunawa muke a kai bamu kai ga yanke hukuncin ba.”
“Ai wallahi ko a yanke hukuncin sai an dawo baya tunda na shigo, babu wanda zai aurawa Lubna Mujahid indai ina da rai.”

Yaya Isma’il ya ce, “Ai ba cewa muka yi za’a aura mata shi ba, shawara muka zauna muna yi a kai, in ana ganin hakan zai yu ba sai ayi a wuce wajan ba.” Mamy ta kalle shi tace, “Kuma Bebi shine wanda ya yi mata fyaɗe, a ganina shine ya kamata ace ya aure ta tunda shine wanda ya fara sanin ta a matsayin ɗiya mace. Duk macen da hakan ta faru da ita ta kan rasa darajar ta a wajan mijin da zata aure, kaga in ya kasance shine mijin ta an huta da duk wani tashin hankali da zai ɓillo bayan auren ta.”

Maryam tace, “kuma kaga yace yayi nadama har yana bada haƙuri, a ganina nima a bashi auren ta kawai zai fi.” Tashi tsaye yayi yace, “shine dogoran ku?, saboda yazo gaban ku yana kuka yace yayi nadama shikenan kawai sai a bashi auren ta?. To Wallahi Allah bazai aure ta ba, ko da ace da gaske Mujahid yayi nadama bazan amince ya auri Lubna ba indai har na kasance yaya a wajan ta. Kar ku manta neman mata halin Mujahid ne, kuma ina so ku tuna wannan hali nasa shine dalilin da ya sa muka fara faɗa ni dashi, ai baku kaini sanin sa ba dan dukkan ku ta dalilina ku ka san shi. Kenan dan yace ya tuba akan Lubna shikenan sai mu ɗauke ta mu kaita gidan sa kamar wacce bata da gata?. Wallahi bazan amince a aura mata shi ba koda zan ga nadamar Mujahid na zuba a ƙasa bazan yarda ba. Zan tsaya tsayin dana wajan nema mata wanda zai riƙe ta hannu biyu, wanda zai aure ta da zuciya ɗaya ba tare da yayi tunanin wani abinda ta rasa ba, wanda zai so ta tsakani da Allah ba don wani abu nata ba.”

Ya kalli Lubna da take ta kuka yace, “Lubna kina tare ni ko kina dare dasu Yaya akan auren Mujahid?.” Tashi tayi ta dawo kusa dashi tace, “bana so, kar ka bari hakan ta faru, wallahi Yaya Adnan bana so.” Ya riƙe hannu ta ya ce, “Ku yi haƙuri! amma Lubna baza ta auri Mujahid ba, in ganin ta a gaban ku ne ya saka ku ke son aure mata shi zan ɗauke ta ta koma gidana ta cigaba da zama har ta samu mijin aure” ya faɗa yana jan hannun ta zasu fita.

Tsayawa yayi ya kalli Yaya Isma’il yace, “kayi haƙuri, ban yi dan ɓata muku rai ba, nayi haka ne kana kare martabar ta, na yi hakan ne dan na aurar da ita ga mijin da ya dace da ita. indai ina da rai bazan bari a kai jinina halaka ba” yana gama faɗa ya fita shida Lubna

BDƘB3P444

Kowa ya bishi da kallo bayan ya fita daga falon Farida tace, “Maganar Adnan fa gaskiya ce Yaya, nima bana goyan bayan haka domin tun asali ya kasance mazinaci ne. Meye ribar auren mazinaci?.” Mamy tayi ajiyar zuciya tace, “ƙwarai Adnan ya fi mu gaskiya, ta dalilin neman marasa lafiya da yake yi aka ƙwace lasisin sa na zama likita.” Mama tace, “nima ban ga amfanin aura masa ita ba wallahi, zina tabo ne da ita zata dinga bibiyar sa ne har ƴaƴan sa” ta faɗa a sanyaye da alama ta tuna Abba.

Yaya yayi murmushi yace, “ai magana ta wuce, tunda kowa ya fahimci abinda yake nufi daidai ne. Allah ya kawo mata miji na gari.” Kowa ya amsa da amin Mamy tace, “Ku kira shi ya dawo da Lubna babu abinda zai faru in sha Allah, babbar budurwa kamar ta ya kaiwa matar sa yace zata zauna?.” Maryam tayi dariya tace, “ki ƙyale shi Mamy, yanzu ko ance bazai dawo da ita ba, a bari tayi kwana biyu.” Farida tace, “gaskiya dai, gani zai yi kamar auren za a yi mata.”

Bebi kuwa yana fita shi da Lubna sai da ta ɗauko wayar ta da kayanta kala biyu ya saka ta a mota suka wuce gida. Da suka je gidan Manal bata falo ya kalle ta yace, “ki shiga ciki tana nan” ya faɗa yana shiga ɗakin sa ita kuma ta wuce wajan Manal.

A zaune ta samu Manal tana canjawa Ayan kaya ganin ta sai tayi dariya tace, “A’a sis barka da zuwa.” Lubna tayi dariya ta zauna tace, “Sis barka da dare, ya Baby Ayan” ta faɗa tana ɗaukar sa kafin tace, “gaskiya Ayan yana da kyau ma sha Allah” ta faɗa tana fara yi masa hoto.

Manal tace, “Ya Mamy da Mama? Suna nan Lafiya?.”
“Lafiya lau wallahi, ya zaman gidan nan?.”
“Bari kawai Sis, zaman shiru ai babu daɗi.” Lubna tace, “tare muke da Yaya fa, ya shiga ɗaki.” Manal ta miƙe tace, “Au ai ban sani ba, ina zuwa” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗakin sa.

Kaya yake sakawa da ta shiga ɗakin ta kalle shi tace, “Sannu da zuwa Partner, ya jikin?” Ta faɗa tana matsowa ta taɓa jikin sa ta riƙe fuskar sa tace, “jikin ka da zafi kaɗan, sannan fuskar ka ta nuna min alamun ran ka babu daɗi” ta rungume shi tace, “me ya faru?.” Ajiyar zuciya yayi rigar da zai saka tana hannun ya rike ƙugun ta ya ce, “Lubna zata zauna a nan na tashon wasu kwanaki, in naga kwanakin ma bai yi aiki ba zata dawo nan da zama gabaɗaya.”

Manal ta kalle shi tace, “da gaske ka ke?.” Ya kalle ta shima yace, “eh, bakya son zaman nata ne?.” Manal tayi dariya tace, “farin ciki nake da zuwan ta, ko babu komai zan daina zama shiru na samu ƙawar hira.” Ya ɗauke idon sa daga kanta yace, “aure dole zasu yi mata shiyasa na gudo da ita nan.” Manal tayi dariya ta koma ta kwanta a kan fatar ƙirjin sa tana shafa gashin da yake kwance a ƙirjin a hankali tace, “wai ka gudo da ita. Gaskiya su Lubna sun yi sa’ar samun Yaya kamar ka. Allah ya ja da ranka ya baka lafiyar cigaba da yin abinda ka ke yi.”

Kiss ya manna mata a kumatu yace, “Amin my dear Wife. Ina fatan zuwan ta ba zai takura miki ba?.” Mintsinin sa tayi a ƙirjin sa tace, “takura ko sakewa? Ai ni zuwan ta yayi min daɗi wallahi, Allah yasa ma ta dawo nan ɗin gabaɗaya da na huta.” Yayi murmushi yace, “Na gode.”

“Kai dai abin godiya baya yi maka wahala” ta faɗa tana raba jikin ta da nasa tana kallon sa. Ƙare nata kallo yake yi cikin shigar da tayi ta vowel mai kyau yace, “kin yi kyau amaryata.” Kallon sa yake sai ta tuna farkon haduwar su tayi dariya tace, “ka san me na tuna?.” Ya saka rigar sa yace, “me kika tuna?.”
“Ranar da na fara ganin ka.” Ya kalle ta yace, “ranar na sace zuciyar ki ko?.”
Chapter 70 · 0% Book details