← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kalle shi shima ya ɗago ido ya kalle ta tace, “uhum an faɗa min, shiyasa ka ke min maganar sa jiya ashe?.”
“Kin san waye?.” Ta kalle shi ta girgiza kai tace, “bani da buƙatar sanin waye, domin ni har yanzu bani da mahaifi ba kuma zan yi ba.”

Bebi yace, “ai tunda kika zo duniya kina da mahaifi Manal” ya faɗa yana cin abinci.
“To in ma akwai ni na goge shi a rayuwata.”
“Bazai taba goguwa ba faɗa kawai ki ke, darajar mahaifi ya wuce ace an goge shi.”
“Nawa maahifin bashi da wannan darajar, hanyar inda daraja take ma bai sani ba.” Ya kalle ta jin abinda tace ya kalli abincin yana juya cokali a ciki yace, “Daddyn su Huzaifa shine mahaifin ki.”

Duk da maganar ta shige ta sosai da jin abinda yace amma sai ta taɓe baki tace, “Sai me dan ya kwance maahifina?.”
“Sai ki masa biyayya domin ki dace a wajan Allah.”
“Har abada” ta furta zata bar ɗakin ya ce, “ki zauna ki yi tunani, wannan abin da kike ba shine mafita a gare ki ba, mahaifi mahaifi ne duk lalacewar sa, duk abinda ya aikata laifi ne an sani amma matsayin ki na ƴar sa magana mara daɗi a kansa ba naki bane.”
Bata ce komai ba ta buɗe ƙofar kawai ta fita shima bai saurare ta ba yaci abincin ya bar kayan a wajan ya tashi ya shiga banɗaki.

Washe gari.

Karfe takwas na safe matar ta kira Adnan a waya a lokacin ma ahirim fita yake yi, ganin kiran sai ya duba ya ɗauka da sallama ta amsa tace, “baka gane mai magana ba? Nice wacce na baka number tq jiya nace zan haɗa ka da yayan mu.” Bebi yace, “na gane, ina kwana.”

“Lafiya lau, In kana nan shi Yayan na mu yazo a ina zamu haɗu sai muje?.”
“Ki faɗa min inda yake zan zo.”
“Muna nan Sultan road nasarawa gra.” Bebi ya ama da cewa, “in nazo zan kira sai a faɗa min gidan.” Ta amsa ya kashe wayar ya fito suka gaisa da Mama amma bai ga Manal ba. Yayi tunanin bacci take saboda safiya ce, Mama tana masa yi tayin abinci ganin harda kunu sai ya zuba kunun yasha zallan sa ya dauki key ya fita.

Sai da ya biya gida suka gaisa da Abba da yake kwance shi ba mara lafiya ba kuma shi ba mai lafiya ba, ya shiga wajan Mama ya ta farka suka gaisa ya fita dan baya son ma ganin Rumana. Har ya shiga mota da niyar zuwa sai kuma ya canja shawara ya kira ta, tana ɗauka yace, “Hajiya ki yi haƙuri bazan samu damar zuwa ba a halin yanzu, sai dai in zaku zo gida.” Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, “shikenan sai kun zo.” Kashe wayar yayi ya kunna motar ya nufi gidan sa.

Yana ajjiye motar ya shiga ciki ba jimawa tace gasu da yake ya bada damar a shigo aka buɗe musu gate suka shigo suka ajjiye mota sannan suka shiga falon gidan.

Manyan mutane dattawa guda biyu kana kallon su kasan sun manyanta da shekaru sannan kuma suna ji da kuɗi saboda yanayin shigar su, ga mata guda uku suma manya kana ganin su ka san sun girma suma. Adnan ya kalle su yace, “Bismillah.” Duk suka zauna kafin a gaisa gaisuwar mutuncin da girmamawa.

Bebi yace, “Ku yi haƙuri na saka kun zo gida.” Babban ciki yace, “kar ka damu, daman mu ya kamata ace mun zo ai. ni sunana Ahmad Muhammad Jalingo, wannan ƙanina ne Bello Muhammad Jalingo, ga ƙannena mata da Hajara, da Safiyya da kuma wacce ta kawo mu nan Halima. Ta tabbatar min da cewa tana ganin ka da wata wacce tayi kama da ahlin mu, don Allah ko tana da alaƙa damu? Saboda kawai ƙaramar mu da ta ɓace shekaru masu yawa, Sai muke tunani ko ita ko kuma jinin ta ce.”

Bebi ya sauke numfashi yana kallon su yace, “Wacece wacce ta ɓace ɗin a cikin ku?.” Alhaji Bello yace, “Sunann ta Zahra, kuma ba ɓacewa tayi ba aurar da ita akayi ga wani mai suna Aliyu da abokin sa ibrahim. Daga wannan lokacin bamu sake ganin ta shekara kusan ashirin da wani abun yanzu. Kullum cikin addu’ar son ganin ta muke yi amma shiru, mun fitar da rai da ita a tunanin mu bata duniya, Halima ce tazo tana cewa lallai taga mai kmaa da ita, to kuma kasan abinda ka ke nema ko ya akace an ga mai irin sa baza ka yi sanya zuwa ka gani ko za’a dace, shine muka zo muji ko wataƙila jinin mu ce.”

Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “Eh to kusan zan iya cewa itace, ba wai ita ƙanwar ta ku da kuke nema ba, ƴar ƙanwar ta ku.” Mamaki ya bayyana a fuskar su Alhaji Ahmad yace, “tana ina?.” Bebi ya kalle su yace, “zan kira ta ku gaisa, amma bana so wani ya nuna mata kun san wacece ita, zata fito ku gaisa matsayin baƙi ne kawai daga nan sai ta koma ko meye zamu tattauna shi bayan barin ta nan.”

“Hakan ma yayi mana, don Allah ka kira ta.” Bebi ya ɗauki waya ya kira Manal yace tazo falo su gaisa da baƙi. Ba jimawa ta fito da hijjabi har ƙasa ta tsuguna ta kalle su tace, “ina kwanan ku.” Duk kallon ta suke yi kowa yana kallon kowa, Manal ma kallon su yake yi dan ta gane matar nan da ta tare su a hanya amma bata nuna ba ta gane ba. Gaisawa suka yi kafiin ta juya ta koma ciki.

Alhaji Ahmad yace, “itace wallahi, wannan jinin Zahra ce, kama take Zahra sannan yanayin hasken ta sak na Gwaggon mu mahaifiyar Zahra ɗin kenan. Kuma mun san mahaifiyar Zahra ita kaɗai ta haifa.” Bebi yace, ƙwarai itace, sunan ta Fatima ƴar Zahra ƴar uwar ku da ku ke nema. Ita ɗin matata ce.”

“Alhaamdullahi! Alhamdullah! Allah na gode maka, Allah na gode maka, Allah na tuba ka yafe min, Allah ka yafe min. Allah na gode maka da ka nufa zan sake ganin Zahra a duniya, Allah na gode maka da ka nufa zan nemi yafiyar ta baki da baki ya Allah” ya kalli Bebi yace, “don girman Allah a ina zan ga mahaifiyar ta?.”

Bebi yace, “Tana nan lafiya lau cikin aminci, bayan Fatima wato Manal akwai yayar ta Nusaiba wacce ake kira da Mubeena. Suna zaune a nan unguwar tudun maliki a yanzu haka.” Alhaji Ahmad ya goge ƙwallar da tazo idanun sa yace, “zaka iya raka mu yanzu mu ganta?.”
“Eh to, gaskiya da zamu bari zuwa wani lokaci saboda akwai wani abun da yake faruwa a yanzu, zuwan ku….” Ya dakatar dashi yace, “ko meye zamu iya fuskatar sa, ka bamu address ɗim gidan zamu je mu ganta.”

Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “shikenan, zan sanar daku.” Bebi ya faɗa masu inda gidan su Manal yake, suka sake masa godiya shi har nauyi yake ji ganin suna yi masa godiya haka, manyan mutane dasu suna yin godiya kamar shine a sama dasu. Har bakin gate ya raka su suka tafi shima ya hau mota ya fita. Bebi daga gidan asibiti ya wuce ya fara abinda yake gaban sa.

Wajan ƙarfe sha biyu na ran sai ga kiran Abba duk inda yake ya dawo ya ɗauki Manal su je gidan su. Hankalin sa ya tashi sosai haka ya bar asibitin ya koma gida yace Manal tazo su je gida suka tafi har Maman dan hankalin Maman ya tashi bata san me ya faru ba.

Daddy a hanyar su ta zuwa gidan su Manal yake kallon Abba yace, “na takura da yawa ko? Na gaji ne bana so na sake kwana da haƙƙin ta a kaina, ko me zata yi min gwara tayi, zan haƙura zan kuma jure duk abinda zata faɗa indai zata yafe min. Jikina yana bani kamar bazan ƙara wasu kwanaki ba shiyasa nake son neman afuwar ta da ta yaran ta.”

Abba yace, “nima haka nake ji, ina buƙatar yafiyar ta baki da baki ko zan samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata, abubuwan sun yi min yawa, abinda nake ji a raina zan iya cewa yafi abinda ka ke ji wallahi.” A ƙofar gidan su Manal suka faka, aka yiwa Baba waya yan kasuwa ya dawo ya tarar basu shiga gidan ba sai da yazo yayi musu iso har cikin gidan. Dukkan su suka shiga a lokacin Mama tana zaune ita da Maman Surayya da Mubeena da Surayya da kuma Manal.

BDƘB3P26

Tunda suka yi sallama kowa ya tsaya cak yana kallon su saboda mamaki, kowa ya kalli Mama da ta kawar da kai gefe kamar bata gansu ba.  Baba ya kalli kowa da yake wajan, ganin hakan sai Maman Surayya da Surayya suka miƙe zasu tafi Baba ya dakatar dasu yace, "Ku yi zaman Balaraba, ku ai ahlin mu ne."

Baba ya kalli Mama zai yi magana ta riga shi tace, "amma mun gama maganar nan da kai ko? Meye zaka sake ɗauko min su ka kawo min bayan ba shiryawa hakan ba?. Meyasa zaka min haka don Allah?" Ta faɗa cikin rauni sosai, idanun ta suka ciwo da ƙwallah.
Chapter 43 · 0% Book details