← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 84

Sashe 21

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kam dariya yake bashi sosai ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa ya danne bai yi ba ta sake cewa, "ai naji haushi da ban yi amfani da dama ta na saka ka kuka ba." ya kalle ta yana dariya ya ce, "ke kuma so kike kiga nayi kuka?." Ta turo baki tace, "eh so nake, kuma so nake ka bani haƙuri."
"Gashi baki da sirri duk abinda aka faɗa miki sai kin faɗa min." Manal tace, "abu ne a zahiri gashi ina gani, inda ina amarya ne har goya ni ka ke yi" ta kalle shi tace, "da ina amarya komai nayi lallaɓa ni ka ke yi, amma yanzu" ta faɗa tana girgiza kai.

Ya ce, "yanzu ke ba amarya bace ba kenan?."
"Gaskiya ni ba amarya bace ba."
"I see" ya faɗa yana murmushi dan ta bashi nishaɗi kam sosai.

Ta kalle shi tace, "to na gama, yanzu zanje na canja kaya sai mu tafi ko?." Ƙare mata kallo yayi cikin kayan jikin ta, tunda dawo yake so ya mata magana a kai maganar ciwon ta ya ɗauke masa hankali ya ce, "kin kuma yi kyau fa." Ta yi murmushi harda ɗaga gira tace, "Allah?." Shima girar ya ɗaga mata tace, "na gode" ta faɗa tana murmushi, ya lura tana so tayi abu a baya shi kuma hakan ya zamar masa jiki.

Cake ɗin ya ɗauka yaci yana kallon ta tace, "Wai a ina kika iya abubuwa masu daɗi ne haka?."
"Don Allah yayi daɗi? Kaga ni ban ci ba saboda kawai sugar a ciki."
"Yayi sosai, hundred percent" ya faɗa yana mata jinjina.
Tayi murmushin murna ya ce, "amma kin ajjiye min nawa ko?."
"Ta ya zan yi ban ajjiye maka ba? Ai dole na ajjiye."

"Kin Kyauta, na san kina sona daman." Ta kalle shi Sai suka haɗa ido tayi murmushi shima haka tace, "da fa kalllo mara mutunci nake maka, tunda muka haɗu a asibiti naje wajan ka da katin Mama ka koro ni dan naje babu Mama."

Raina mata hankali yaso yi ya ce, "Au wai kece daman?." Ta harare shi tace?, "A'a aljana ta ce." Ya wara ido yace, "ni kike harara?." Tayi hanyar ƙofa tace, "ramawa nayi" ta faɗa tana fita a guje yayi dariya yana cewa, "malama ki daina gudu."

Bata fito ba sai da ta shirya cikin atampa mai kyau ɗinki riga da siket ta saka mayafi nai girma kamar yadda yake so, ta same shi har ya canja kaya zuwa manyan kaya. Ta kalle shi tace, "manyan kaya suna yi maka kyau, amma ina so naga ka saka ƙananun kaya." Yayi murmushi ya ce, "bakya so ki ganni ba kayan?." Ta ɗan kulle ido ta buɗe ya ɗaga mata gira yace, "uhum bakya so? Ko bana yi miki kyau babu kayan?."

Manal tace, "ni ina da kunya fa." Ya yi dariya sosai yana kallon ta ya ce, "ni kuma bani da kunya."
"Ni shaida ce."
"Kuma kin ga ni kina yi min kyau babu kaya, saboda...." Toshe kunne tayi tace, "Allah zan maka kuka."

Ya murmusa ya ce, "muje na ɗauki kayan kar ki ce min daman ai da ne nake ɗaukar miki kaya." Dariya tayi suka fito daga ɗakin ya ɗauki abinda tayi ya fita dasu ya saka a mota ya buɗe mata gaban motar ya kalle ta ya ce, "na wanke laifina?." Ta shiga ciki tana cewa, "ai dan kaji na faɗa ne, don Allah ka bani na tuƙa" ya harare ta baice komai ba ya ja motar suka fita daga gidan suka nufi gidan Hajiya.

BDƘB3P12

A kan hanyar su suka tsaya a wajan mai siyar da kayan marmari suka siyawa Mama da kuma Hajiya. Bayan sun siya suka ɗauki hanyar gidan Hajiya. Basu jima a can ba suka fito, a ƙofar gidan ne Manal tana tsaye Bebi ya fito ya kalle ta ya kalli wasu mutane guda biyu mace da namiji da suke kallon ta bai ce komai ba suka shiga mota.

Sai da ya fara tafiya sannan ya kalle ta yace, "su waye suke kallon ki daga tsallake?." Manal tace, "ban ma kula ba balle na na gansu." Bebi yace, "amma kamar sun san ki, kallon sani suke miki." Manal tace, "ban ma kula ba ni." Ya kalle ta yace, "ai baza ki kula ba daman, ni ai na kula."
"Tunda ka kula ai shikenan."
"Yayi kyau."

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ya kalle ta ganin tayi shiru tana kallon wani wajan sai ya riƙe hannun ta suka haɗa ido ya ce, "ya dai?." Ta sauke numfashi tace, "wani iri nake jina."
"Ko muje wajan Mama?." Manal ta girgiza kai tace, "faɗa zata yi min tace ba jiya na tafi ba, mu wuce kawai."

"Me yake damun ki?." Manal ta riƙe hannun sa da ya riƙe nata hannun tace, "babu komai, kawai bana jin daɗi ne." Sai kuma ta riƙe hannun sa sosai tana kallon cikin hannun na sa kamar mai son ganin wani abun a tafin hannun kafin tace, "yanzu kuwa kana ganin mahaifin mu yana da rai?." Ya kalle ta yace, "to ai baka sanin wanda yake da rai ko wanda ya bar duniya indai ba kaji labari baPartner." Manal ta ɗora hannun nasa a fuskar ta tace, "ni kam ina ji a jikina yana da rai, Ina so kuma na gan shi ko sau ɗaya ne."

Shafa fuskar ta yayi a hankali ya ce, "Allah ya cika miki burin ki." Ta amsa da amin kafin tace, "amma Mama bata so." Shiru yayi bai ce komai ba ganin yayi shiru sai ta canja maganar tace, "Hannun ka sanyi."
"Ke kuma naki babu sanyi, yadda hannun ki yake da ɗumi haka jikin ki yake." Tayi murmushi shima yayi murmushin bai sake cewa komai ba.

A cikin gidan su ya faka motar suka fito aka ɗauki abinda tazo dashi da kayan marmarin da suka siya suka shiga ciki. Abin mamakin kamar jiya duka yaran Mummy ɗin suna suna aikin hira, ganin Manal ta shiga sai Mimi tayi ihuu ta taso tana cewa, "kin gani ko Mama na faɗa miki ta koma, barka da zuwa sister!" Ta faɗa tana rungume ta. Manal tayi murmushi tace, "yau kin zo kenan?."

Mimi tace, "ai fushi nake, baku taɓa zuwa inda nake ba har yanzu." Mama da take gefe tace, "laifin ɗan uwan ki ne, kin san halin sa bazai je gidan ki ba, dana tambaye shi yaushe zai je sai cewa yayi kawai sai a ganshi a gidan ƙanwar sa?."

Manal ta ƙarasa ta zauna suka gaisa da Mama ta amsa da fara'a tace, "yanzu maganar ku muke yi, nace kai lafiya Adnan babu shi babu labarin sa tun jiya da yace min zai je gidan ku, Sai Farida tace ai wallahi Mummy tunda kika ji shi shiru an bashi matar sa, sashi kuwa an bashi ke ɗin. Ya jikin naki?."

Manal tayi murmushi cikin jin kunya tace, "na ji sauƙi Mummy."
"Allah ya bada lafiya, ya raba lafiya." Ta amsa da amin cikin jin nauyin Maman. Kallon Farida tayi tace, "Yaya ina wuni." Yaya Farida tayi murmushi tace, "yi haƙuri Manal na zuba miki ido ina kallo ban yi magana ba, jiya jiyan nan ya gama cewa Mimi bleaching take yi, to ke kuma me ki ke yi kenan?. Wannan haske naki ma sha Allah, da ana ƙwacewa da yanzu na raba ki dashi."

Manal tayi dariya kawai bata ce komai ba Kausar tace, "Ai Anti baza ki ga hasken ta ba sai kin je gidan nan kin tarar da ita babu kaya, wallahi fatar ta kamar...." Kallon da yayi mata ya saka ta rufe baki tana dariya.

Farida tace, "ai a fuska ma an san tana da haske balle jikin ta." Mama tayi dariya tace, "ta bakin sa ki dinga haɗawa da tabarakallah kar ki disashe masa hasken mata." Suka yi dariya Manal ita kunya take ji sai ta sunkuyar da kai tana murmushi. Mama ta kalle shi tace, "ka fito da ita bayan bata da lafiya?."
"Mun je mun gaishe da Hajiya ne muka biyo nan." Kausar ta kalle shi tace, "Yaya me aka kawo mana?."

Hararar ta yayi ta tashi ta buɗe abinda aka shigo dashi ta miƙawa Mama ta karɓa tace, "harda hidima Manal keda babu lafiya?." Manal tayi murmushi tace, "babu komai Mummy." Bebi ya kalli Farida da Mimi yace, "wai me kuka dawo yi ne yau?, ba jiya ku ka zo ba?." Farida tace, "Abba ne babu lafiya muka zo duba shi."

Bebi yace, "Abba babu lafiya babu wanda ya faɗa min? Me ya same shi?" Ya faɗa yana tashi tsaye ya fita ba tare da an bashi amsa ba. Mama ta kalli Kausar tace, "raka ta wajan Abban su gaisa sai tazo taci abinci." Kausar ta tashi suka fita da Manal.

Farida ta kalli Mummy bayan fitar Manal tace, "wallahi Manal tana burge ni Mama, akwai kunya da hankali." Mama tace, "gaskiya babu laifi, har yanzu bata iya haɗa ido dani. Ba ke kaɗai ba Farida ni kaina farin ta ma burge ni yake, ba kamar yanzu da yake ya haɗu da ciki hasken nata ya daɗa bayyana."
Farida tace, "Dole ta dinga gigita miki ƙwanyar ɗa ai Mama, kallon ta kawai abun burgewa ne saboda hasken ta na musamman ne." Mama tayi dariya kawai bata ce komai ba dan Rumana ce tazo zuciyar ta.

Manal kuwa da suka shiga wajan Abba samu suka yi Bebi yana zaune a gefen sa yana duba maganin Abban, suka shiga da sallama kan Manal yana ƙasa dan bata so Abba ya shaida fuskar ta.

Abba ya amsa suka ƙarasa suka zauna a kan carpet Kausar tace, "Abba Manal ɗin Yaya Bebi ce." Abba sai ya tashi zaune sosai Manal tace, "Barka da dare Abba, ya ƙarfin jikin?."
"Lafiya lau Manal, jiki Alhamdulillah."
"Allah yasa kaffara ce." Ya amsa da amin.

Abba ya kalle ta cikin son jan ta da hira yace, "ya sunan ki na gaskiya?." Manal tace, "Fatima." Abba ya girgiza kai yace, "sunan Maman ki kika ci kenan?." Manal ta ɗaga kai alamun eh kanta na sunkuye. Abba yace, "Yayar ki fa? Meye sunan ta?."
"Sunan ta Nusaiba, amma Mubeena ake ce mata."
Chapter 21 · 0% Book details