Sashe 62
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kalle shi kallo irin na ban yarda da kai ba tace, “Shikenan matsayin da take dashi?.”
“Shikenan bayan wannan, zan girmamata matsayin yayar matata, sannan zan kalle ta matsayin ƙanwata wacce muka tashi kusan tare da ita.” Ta goge idanun ta tace, “har yanzu zuciyata rawa take yi.”
“Ta daina rawa a kaina, har zuciyata nake faɗa miki wannan maganar kin san bazan miki ƙarya ba.” Ta girgiza kai tace, “Meyasa baka faɗa min an ɗaura maka aure da ita ba? Meyasa ka ɓoye min?.”
Bebi yace, “yadda kika ji labarin haka naji wallahil azim ban sani ba, na san dai ta tafi Abuja kuma Mummy ta maimaita min maganar aurena da ita bayan wannan ban san da aurena a kanta.” Manal tace, “yanzu ko a tarihi sai ance mata biyu ka aura ko?.” Yayi murmushi yace, “mace ɗaya na aura kuma itace ke.” Ta kulle ido ta buɗe tace, “bayan ita babu wata kuma?.”
Yayi ƴar dariya yace, “akwai.” Kallon sa tayi ya ɗaga mata gira yace, “akwai Fatima na kuma Mummyn Ayan, ita kaɗai ce a zuciyata bayan ita babu ko wacce mace da nake kallo da fuskar soyayya.” Ta sauke ajiyar zuciya tace, “ba wani nan, bayan kwana biyar nayi baka neme ni ba.”
Bebi yace, “Allah ne kawai ya san irin tashin hankalin da na shiga, duk yadda zan faɗa miki baza ki gane ba, Allah ne kawai yasan yadda zuciyata take bugawa saboda rashin ki. Babban abin haushin ma muna tare da Huzaifa bai taɓa faɗa min kina can ba, har gidan nan yazo yana cewa shima zai nemo ki matsayin sa na yayan ki bai nuna min kina gidan sa ba. Ai ya ɗauki haƙƙina wallahi kuma zan rama abinda yayi min.”
Manal tayi dariya kaɗan tace, “Yayana ne.”
“Yayan naki fa, ya munafurce ni.” Ta girgiza kai tace, “Allah zan ce sai ka bashi haƙuri zan haƙura.” Yayi dariya ya ce, “girman ki ne, in hakan ki ke so sai ayi indai zaki huce.”dariya tayi ta kwanta a jikin sa yace, “Allah ya azabtar dani, na shiga tashin hankali sosai. Na rasa inda zan saka raina, nayi waya kin ƙi ɗauka na zaga inda nake tunanin zan same ki amma bakya nan. Kar ki sake nisa dani partner rashin ki illa ce a gare ni.”
“Ni kuma bani da kamar sa, Yayana ne da babu kamar sa.” Yayi murmushi yace, “ni kuma abokin adawata ne.”
Tayi murmushi ta riƙe shi tace, “Partner amma akwai wata maganar fa.” Ta ɗago daga jikin sa tana kallon sa tace, “a cikin zaman auren da muka yi da kai bamu shekara ɗaya ba amma ka mare ni sau biyu, na so ace ina cikin matan da zasu kafa tarihi a rayuwar auren su suce ce shekarar su hamsin da mijin su bai taɓa dukan su ba, ban samu shiga wannan layin ba duk da burina ne hakan. Don Allah Partner kar ka sake cewa zaka dake ni, ka kalli kunnena ka gani sai da na sha magani saboda marin da kayi min sai dai kunnen yayi ciwo. in dai ranka zai ɓaci ka ce zaka ɗaga hannu ka dake ni rayuwar mu zata dinga lalacewa, girman ka da matsayin ka zai dinga raguwa a idona har a kai ranar da ba’a a bana fatan zuwan ta…” kafin ta ƙarasa yace,
“Ranar da zan mare ki ki rama ko?.” Ta ɗaga masa kai alamun eh ya riƙe kunnen ta yake ciwo yana kallon cottin ɗin da take ciki yace, “ki yi haƙuri bazan sake ba in sha Allah, hakan ba halina bane raina ne ya ɓaci sosai, amma nayi miki alƙawarin duk ɓacin ran da zan shiga bazan sake marin ki ba. Roƙona a wajan ki duk lokacin raina yake a ɓace ki dinga ƙoƙarin ganin kin gujewa abinda zai sake ɓata min rai, ki dinga ƙoƙarin taimaka min wajan kawar da ɓacin ran in ba haka ba za’a iya samun matsala fiye da wacce tafi waccan.”
Ta ɗaga kai tace, “in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina. Kayi haƙuri da kalaman da na faɗa maka a ranar, na shiga tashin hankali ne kawai maganar na fitowa daga bakina ne ban san ina yi ba.”
“Komai ya wuce, kar ki damu daman laifina ne.” Tayi murmushi tana kallon hannayen sa da suke cikin nata ta kalli Ayan da yayi bacci ta kalle shi tace, “Mummy bata ji daɗin hukuncin da kayi ba ko? Meyasa ka zaɓe ni?, da gaske alfarmar Ayan ne ya saka ka zaɓe ni?.”
Kiran sallah ya jiyo ya kalle ta yace, “ana kiran sallah, zan je nayi sallah na dawo zan faɗa miki dalilin da ya saka na zaɓe ki, abu ɗaya nake so ki riƙe a zuciyar ki ni Adnan naki ne ke kaɗai in sha Allah. Bani da wacce nake so sai ke Manal, Allah ne ya saka min ke a zuciyata. Ko da Ayan ko babu Ayan zan zaɓe ki a cikin mata dubu, kece ɗaya tilo bayan ke babu wata” ya faɗa yana yi mata kiss a goshi ya tashi tsaye ya ƙarasa wajan ya yi masa kiss ya fita.
Yana fita aka kira ta a waya ganin sunan Addah Halima ce sai ta ɗauka tana murmushi nan take sanar da ita gata ta zo gidan, da farin ciki Manal ta fito ta tarar ya buɗe musu falon sun shigo shi kuma ya fita. Adah Halima ta jima a gidan suna hira Manal tayi musu girki aka ci ana dariya da raha cikin zumuncu, bata bar gidan ba sai bayan sallar i’sha Manal tayi farin cikin zuwan ta sosai duk da sallama tayi nata tace washe gari zata wuce Lagos.
Bayan fitar su ya jima bai dawo ba har ta gama kwashe kayan da akayi amfani dasu ta gyara wajan tayi wanka ta shirya dan ta san ranar ta musamman ce a wajan sa shi da ita. Tana fitowa falon yana shigowa yace, “na jima ko?, Naje wajan Mama na kai mata maganin Ruman.”
Kallon da tayi masa ne ya saka yace, “Oh Sorry, Rumana zan ce” ya faɗa yana zama tayi dariya tace, “na kawo maka abinci ko ba yanzu ba?.”
“Bani yanzu.” Ta wuce ta kawo masa abincin ta zauna a gefen sa tana ci itama. Wayar sa ce tayi ƙara taga yayi saurin danna wayar ta ɗauke ta kalle shi tace, “wannan hanzari na danna power na meye? Waye yake maka waya haka?.”
Bebi yace, “daga asibiti ne bana so a takura min.” Ta jingina da kuskure tana kallon sa tace, “oh daga asibiti, Lallai kam.” Bai ce komai ba yana cin abinci ta kalli wayar tace, “ko yaushe wayar ka na kusa da kai kamar mara gaskiya, me ka ke ɓoyewa a ciki?.”
“Me zan ɓoye a ciki? Babu komai, wayar mutum sirri ce ai ko?.” Manal tace, “ni meyasa tawa bata zama sirrina ba?.” Yayi dariya kawai baice komai ba kafin ya kalle ta ganin shi take kallo yace, “babu komai a wayar fa, zaki iya ɗauka ki duba abinda kike so.” Manal tace, “a nasihar da aka yi min kafin nazo gidan nan ance min banda duba wayar ka, na kuma gamsu da nasihar, a yanayin yadda aka kira ka kashe da sauri ya nuna min akwai wani abun a ƙasa.”
“Tunanin ki budurwa ta ce?.”
“Ni dai ban ce ba, kawai nace akwai wani abun a ƙasa.”
Yayi murmushi bai ce komai ba ya cinye abincin ya tashi ya shiga ciki itama ta ɗauke abinda ya gama ci ya shiga ciki. Tana tsaye tana shaye abinda Maman Surayya ta bata tun ranar da zata gidan ya shigo yana kallon ta itama tana kallon sa, ta ajjiye abinda ta shanye ya shigo yana kallon ta yana lumshe ido ya buɗe ya sake kallon tq yace, “kin shirya amma ko?.”
Ya zo gab da ita yana kallon idon ta tace, “na shiryawa me?.”
“Kin shirya zama sabuwar amarya a yau? Dan no excuse, four to six rounds in sha Allah. Dan wannan kwanakin da aka ɗauka Allah sai na fanshe su a yau.”
Ta wara ido tace, “Six kamar wata machine?, A’a kar mu yi haka da kai ka san bazan jure ba.” Yayi dariya ya kai hancin sa wuyan ta yace, “ki shirya dole ma ki jure ko bakya so.” Cikin shagwaɓe a tace, “Allah ka san bazan iya ba, kaima faɗa ka ke amma kaima baza ka iya ba.” Yadda tayi shagwaɓa ya burge shi ya kuma shige shi sosai, ya jawo ta ta faɗa jikin sa da nata yana zame rigar ta daga sama yace, “kina kokwanto bazan iya ba?.”
Tana daga jikin sa tace, “uhum!.”
“Mu gwada?.”
“Ni dai a’a ban yarda ba” ta faɗq tana sake motsawa a jikin sa hakan ya sake saka shi a sabon yanayin.
Ɗagowa tayi ta kalle shi tace, “why did you choose me?.” Ta faɗa a lokacin da yake sauke rigar ta ƙasa. Fuskar ta ya riƙe yace, “Because” ya faɗa yana yi mata kiss a wuya yace, “Because you’re you” ya yi mata kiss a wuyan ta yace, “loving” ya sake yi mata kiss yace, “beautiful” ya dawo goshi ta yace, “smart” ya yi mata kiss a idanun ta yace, “brave” ya sake matsawa wani wajan yace, “unselfish” ya sake matsawa wani wajan yace, “your smell” ya faɗa tana kai hannun sa ko ina na jikin ta da kuma hancin sa. Ya kai bakin sa cikin nata ya yi kissing sannan yace, “your taste.”
Manal ta lula wata duniya a wannan lokacin salon da yake amfani dashi yana yi mata maganar ya saka ta a sabon yanayi wanda bata ɓata shiga irin sa ba, murya a sarƙe tace, “it’s feels so good when you touch me Partner.” Jin abinda tace sai ya ɗauke ta cak ya ajjiye a kan gadon ya bi bayan ta ba tare da wani dogon tunani ba.
BDƘB3P38
Manal ta jima tana bacci kukan Ayan ne ya tashe ta ta miƙe zaune daƙyat ta kalli inda yake jin kukan sa ta ganshi a hannun sa yana jijjiga shi yace, "na rasa yadda zan masa yayi shiru, ba dan naso ba kika tashi" ya faɗa yana ƙarasowa ya hau kan gadon ya zauna kusa da ita.