Sashe 32
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin Ammi ta shigo dan kukan ta har falon ana ji, ta tsaya tana kallon su Mama tace, "ki bursu ki faɗa min, akwai abinda yace miki ne?." Abu ɗaya take maimaitawa tana cewa, "Baya sona, wallahi baya sona ya daina sona, Shikenan na shiga uku na, in ban aure shi ba mutuwa zan yi. Mama ƙirjina zafi yake min, ƙirjina yana min zafi Mama, ƙirjina!."
Hankalin Mama da Ammin ya tashi şuna salati Mama tace, "ina kika ajjiye maganin ki? Ina maganin ki?." Bata jin abinda suke cewa ƙirjin ta kawai take nunawa tana kuka sosai daga zaune dan in ta kwanta ciwon yafi azaba. Mama ta kalli Ammi tace, "maza kira min Bebi yanzu Sumayya, Kira shi da gaggawa." Hannun Ammi na rawa take kiran wayar Bebi amma bai ɗauka ba.
"Rumana! Rumana!! Rumana!!!" Mama ta faɗ tana jijiiga ta amma ina Rumana ta jima da barin hankalin ta.
BDƘB3P17
Bebi kuwa bai san abinda yake faruwa ba, bai shiga gidan ba sai da yayi sallar i'sha ya shiga har falon da su Manal suke ya samu Maman Surayya ita da ƙaramar ƴarta ƙanwar Surayya suna ta hira da Manal. Zama yayi yana murmushi yace, "Mama kin dawo ashe?."
Da murmushi tace, "na dawo Adnan, ga auta ta yau ta maƙale min." Ya kalli wacce ta nuna masa ta gaishe shi ya amsa da fara'a ya kalli Manal ya sake kallonMama yace, "Mama zamu je asibiti da Manal za'a duba ɗinkin ta, yanzu zamu dawo in sha Allah." Mama tace, "Allah ya dawo daku lafiya." Ya amsa da amin ya tashi ya fita. Manal ta saka hijjabi akan kayan jikin ta ɗauki Ayan ta fita ta shiga motar suka tafi.
Asibitin su suka wuce tun kafin su hau sama suka wuce office ɗin likitan da zata duba ta suka shiga da sallama ta amsa tana cewa, "ga Maman Ayan." Manal tayi murmushi ta ƙarasa ciki ta karɓe shi tace, "Kaii ma sha Allah! Haka yayi girma yayi yawo?." Ta kalli Bebi tace, "an maka two zero fa, yaron nan da babar sa yake Kama wallahi."
"Shikenan na huta" ya faɗa da ɗan sakin fuska dan babbar likita ce kuma a shekaru ma babba ce shiyasa yake girmamata. ya kalli Manal yace, "bara naje office na dawo." Likitan tace, "ai kam ƴan gidan ku ma suna gidan nan, tun ɗazu naji ana neman wayar ka bata shiga, nima na kira ka ko zan same ta ban samu ba." Wayar ya ɗauko a aljihu ya duba yaga kiran Mama dana Ammi yace, "Subahanallahi! Amma dai lafiya ko?" ya faɗa yana fita da sauri.
Likitan tana ta tsokanar Manal ta duba ta bayan ta gama tace, "ai ɗinkin naki ma ya warke, kin yi ƙoƙarin kula dashi sosai. Ki cigaba da shiga ruwan zafi kina zama a ciki." Manal tayi murmushi tace, "na gode."
"Babu komai,Allah ya ƙara lafiya" ta amsa suka fito tare Ayan yana hannun likitan.
Inda su Maman suke suka nufa a nan taga Mama a zaune akan kujera da Ammi da kuma Kausar kowa da alama hankalin sa tashe yake. Manal ta ƙarasa ta zauna Kausar ta karɓi Ayan a hannun likitan ita kuma Manal ta kalli Mama tace, "Mummy waye babu lafiya?." Mama ta kalle ta tace, "Rumana ce, ina ta kiran ku dake dashi babu wanda ya ɗauka." Manal tace, "waya ta tunda na saka chargi na manta ma da ita wallahi, Allah ya bata lafiya." Ta amsa da amin suka yi shiru ba wanda ya kuma magana.
Bebi ne ya fito daga ɗakin da take ya kalli Mama da take kallon sa ya ce, "Mummy ai babu damuwa bacci take yi, daman rashin shan magani ne kwana biyu ya saka hakan ya faru amma yanzu zata warware in sha Allah." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba yace, "lokacin da kike min waya wayar na silent ban ji ba gabaɗaya kuma ban yi amfani da wayar ba shiyasa, yanzu ma Dr ce take faɗa min kuna nan."
Mama tace, "babu komai, na nasan baka ji ba" ta faɗa tana kallon sa dan ta san bai ji ɗin bane. Ya kalli Ammi yace, "in sha Allah Ammi zata warware." Ammi ta amsa da Allah ya sa ya wuce zuwa office ya zauna dan a yanayin da Mama take yana barin asibitin faɗa zata yi masa.
Har tara na dare suna asibitin Manal tana office ɗin sa a lokacin saboda Ayan ya tashi yana kuka dole ta koma can saboda ta kula dashi. Bebi ya koma ɗakin da Rumana take ya kuma fitowa Mama tace, "bata farka ba?."
"Ai allurar bacci aka yi mata Mummy, kawai rashin bacci a damuwar ta gaskiya, amma da ta warware Shikenan in sha Allah."
"Allah ya sa."
"Amin."
"ka koma gida, Manal ta jima a nan na san ta gaji gata da ɗanyen jego. Duka abinda yake faruwa zan yi maka waya." Ya amsa da to yaje suka fito da Manal ta dawo ta yiwa su Mama sallama suka wuce gida.
A mota manal ta kalle shi kafin tayi magana ta riga ta ya ce, "Dr tace min kin warke sosai, ɗinkin yayi kyau." Manal tace, "eh haka tace min."
"Gaskiya Mama tayi ƙoƙarin kular min dake, Allah ya bata lada ya saka mata da aljanna."
"Amin ya Allah."
"Daman na ƙagu ki warke wannan jinin ya ɗauke ki dawo office, kinga yanzu kin warke saura jinin ya rage." Ta kalle shi suka haɗa ido kafin ya janye idon sa ya cigaba da tuƙa motar tace, "wanne office?." Bebi yace, "ai kin san wanda nake nufi." Manal ta turo baki tace, "to ai sai an kwana arba'in." Ya girgiza kai ya ce, "ba dai a gidan Adnan ba kuwa, ai indai kin gama jini bana jin zan ƙara miki kwaya ɗaya Manal, ni kaɗai nasan halin da nake ciki, tunda kin samu lafiya jini kawai zan jira ya tafi kwana arba'in wannan maganar hausawa ce."
Manal tace, "to nida bazan koma ba sai an ɗauki mataki akan yin ciki, dan na faɗa maka sai nan da shekara biyar zan haihu." Yayi dariya ya girgiza kai yace, "an gama ranki ya daɗe." Tayi murmushi tace, "ya jikin Rumana ɗin?."
"Da sauƙi, ciwon ta ne ya tashi, daman ai na faɗa miki tana da ciwon zuciya ko?."
Manal tace, "uhum ka faɗa min."
"Ciwon ne ya motsa amma zata dawo daidai in sha Allah."
"Allah sarki! Wataƙila wani abun ne ya tayar mata da hankali."
Bebi yace, "eh zata iya yuwa hakan, kin san ciwon ƙaramin ɓacin rai sai ya kai mutum ga kwanciyar asibiti." Manal ta kalle shi tace, "amma ni nafi tunanin ganin da tayi mana ɗazu ne ya saka ciwon ya tashi." Ya kalle ta kaɗan kafin ya ɗauke kai yace, "kawai dan ta gan mu sai ciwon ta ya tashi?." Manal tace, "eh mana, kishi ne kawai." Cikin dakiya da basarwa yace, "mijin tane ni da zata yi kishi?."
"Wanda take so ya zama dai."
Bebi yace, "Manal ki daina wannan maganar ba yadda kike tunani bane." Manal ta taɓe baki tace, "hmmm! Faɗa ka ke kaima amma wallahi akwai wani abu a ɓoye dake tsakanin ka da Rumana, baka so na sani ne kawai, Baka san gwara ka faɗa min ba da na gano da kaina." canja maganar yayi yace, "Mu shiga mu gaida Mama ko?."
Manal tace, "dare yayi sosai mun bar Maman Surayya ita kaɗai, gwara mu koma." Shiru yayi bai ce komai ba sai tayi murmushi tare da yin ƙwafa ya kalle ta ya ce, "na faɗa miki babu wannan maganar gwara ki barta, Meyasa kike min haka ne?, kina kawo tunanin da ba shine yake faruwa ba na faɗa miki kuma kin ƙi yarda. Ya kamata ki daina wannan tunanin kar kishi ya rufe miki ido."
Ganin ya fara yi mata faɗa alamun ransa ya fara ɓaci sai tace, "kwantar da hankalin ka, meye na faɗan kamar mara gaskiya?." Jin abinda tace sai ya sauke numfashi kaɗam ya ɗauke kai daga kanta yana cigaba da jan motar. Manal tace, "Shikenan ai babu komai, kaji na sake cewa wani abun ne?." Bai ce komai ba itama tayi shiru a haka suka koma gida babu wanda ya sake yiwa wani magana a cikin su.
Suna shiga gidan Manal ta wuce wajan Maman Surayya tana cewa, "Mama na jima ko? Wallahi wata ƙanwar sa Rumana aka kwantar a asibitin ciwon zuciya yana damun ta, shiyasa muka zauna a wajan Mummyn sa."
Mama tace, "Allah sarki! Allah ya bata lafiya." Manal ta amsa da amin fuskar ta babu walwala ta shiga ɗaki. Shima a lokacin ya dawo yana sake maimaita mata abinda Manal ta faɗa mata Mama tace, "Manal ta faɗa min, Allah ya bata lafiya."
"Amin Mama, Mun barki ke kaɗai."
"Babu komai kar ka damu, ga Aysha ai muna tare."
Fita yayi daga falon Mama ta kira Manal da ta canja kaya ta zuwa na bacci tace, "nayi abinci fa,
ki kai masa ko zai ci." Manal ta sauke numfashi ta shiga kitchen ɗin. Dambu Mama ta ajjiye musu da alama ma daga gida tazo dashi ya sha gyaɗa da zogale, Sai salad ɗin Manal da ta haɗa mata da basmati rice da aka dafa.
Zuba masa dambun tayi daidai yadda ta san zai cinye ta nufi falon da ta san yana can, ta same shi a zaune yana kallon ball ta ajjiye masa ta ɗauko ruwa da lemo ta ajjiye. Ta kalle shi taga ya ɗaure fuska ko kallon ta bai yi ba tace, "Wai duk akan Rumana ka fusata haka? Kuma a haka ka ke so wai na yarda babu komai?. Hmm! Kana ɗauka ta mara wayo ne kawai Partner, ko na ce kallon yarinya ka ke yi min har yanzu" ta faɗa tana niyar barin wajan bai ce mata komai ba.