Sashe 73
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta kalli Maryam tace, “Sai abinda Maryam ɗin tace dai, in taga zata koma sai ta koma ɗin.” Maryam dai kanta yana ƙasa hawaye na zubawa daga idanun ta wanda bata san dalilin su ba. Yaya Isma’il yace, “to mu dai gabaɗayan mu nuna goyan bayan ta koma indai an yi binkice an tabbatar da wani hali mara kyau bai shigo cikin halayen sa ba. Har Daddy ya amince da hakan saboda komawar ta shine mutuncin ta da na yaran ta. Bama so a sake samun matsalar da aka samu da Mahmud, tunda aure dole sai an yi bincike, in dai za’a yi bincike kuwa za’a iya samun matsalar da aka samu da Mahmud.”
Mamy tace, “wannan gaskiya ne, nima ina goyan bayan hakan gaskiya amma in taga zata koma. Babu lallai babu dole.” Yaya Bilal ya kalle ta yace, “Maryam me kika yanke?, Kina ganin a bawa Kamal damar mayar dake ɗakin ki ko kuma bakya ra’ayina hakan?.” Maryam tana kuka tace, “Kamal bashi da kirki, bazai iya kare martabata a matsayina na matar sa ba. Kamal ya fita daga raina gabaɗaya, saboda ko na koma auren sa gani nake bazai riƙe ni da mutunci da daraja ba.”
Yaya Isma’il yace, “wannan tsakanin ku ne kuma ai, kuma ko meye ya faru ai ke kika bayar da ƙofa, yanzu kuma yana buƙatar ku gyara tsakanin ku. In kinga zaki koma daidai ne, in kin ga baza ki koma ba shima daidai ne. Babu wanda zai miki dole a gidan nan, kina da ra’ayin da zaki ce baza ki koma ba.” Yaya Bilal yace, “to in bata koma ba waye zata aura?, Ko irin waccan damuwar da tayi silar barin Abba duniya ita take so ta sake dawowa cikin gidan nan?.”
Sai a lokacin ya kalle su Adnan yace, “Yaya ku bata dama tayi tunani.” Yaya Bilal yace, “Tunanin me zata yi? Bafa yarinya bace ba kuma sabon aure zata yi ba. Mijin nata dai da ta bari shi zata komawa, Kun sani rashin haƙuri ne kawai ya raba su tun farko, ba dan yana ƙuntata mata ko yana yi mata wani abun mara daɗi ba.”
Adnan yace, “Duk da haka Yaya, a bata lokaci tayi tunani ta kuma nemi zaɓin Allah.” Yaya Isma’il yace, “Shikenan tayi tunani, Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi.” Suka amsa da amin kafin Yaya Isma’il ya sake cewa, “Sai kuma batun akan ƴan matan ku Mamy.”
Mamy tayi murmushi tace, “to labari ne mai daɗi dai ko?.” Yayi murmushi yace, “Labari ne mai daɗi kuwa. Kausar dai Usman ɗin Daddy ya matsa
akan shi ita yake so. Ina jin ma shida ita sun daidaaita kansu tunda har ya yiwa Daddy magana. Sai kuma abokin Adnan Dr Yasir da yake masa magana akan a Lubna, Shima yau zai je ya samu Daddy akan izinin yin magana da ita.”
A tare Mamy da Mama suka ce, “Alhamdulillah, Allah ya nuna mana ya tabbatar mana da alkhairi a ciki.” Suka amsa da amin kafin Mamy tace, “kuma shi Dr Yasir ɗin ya son komai akan Lubna Bebi?.” Adnan ya ɗaga kai yace, “Ya sani Mamy, bamu da matsala dashi in sha Allah, na yarda dashi ɗari bisa ɗari, zai riƙe Lubna da mutunci in sha Allah.” Mamy tayi murmushi tace, “tunda ka yarda dashi dukkan mu bamu da matsala dashi, kowa ya san baza ka kawowa ɗayan su abinda zai cutar dasu ba
Aka yi dariyar farin ciki kafin Yaya Bilal yace, “Kun ga abinda yake hango mana ko Mamy? muka so aurawa Lubna Mujahid a kwanakin baya, da yanzu nuna nan nuna dana sani.”
Mamy tace, “bari kawai, Allah ya cigaba da haɗa kan ku gabaɗaya.” Suka amsa da amin. Adnan ya kalli agogon hannun sa kafin ya kalli iyayen nasa yace, “Mamy da Mummy tunda ku ka fita daga takaba ban ji kuna zanjen zaku yi wani aurem ba.”
Mamy tayi dariya kafin tayi magana Mama tace, “Aure kuma Adnan? Wanne irin aure ana zaune lafiya?.” Bebi yace, “aure dai nake nufi Mummy, kuna da damar da zaku sake zama a inuwar wani namijin kafin rai yayi halin sa.” Mamy tace, “To Bebi ban da abin ka auren me zamu yi? Ko nace auren me zan yi?, har gwara Mummyn ka babu wanda zai kalle ta yace ta haifi kamar ku, amma ni ai kowa ya san na girma. Me kuma zan nema wanda ban samu ba?, ai sai dai fatan Allah ya sa mu cika da imani.”
Yaya Bilal yayi murmushi yace, “Amin Mamy. Amma duk da haka in kuna da ra’ayin hakan ba laifi bane.” Bebi yace, “yauwa abinda nake so nace kenan, wasu yaran su ne suke hana iyayen su mata aure, dalilin hakan wasu iyayen ko suna so saboda yaran su sai haƙura dan kar yaran su ga kamar an ci amanar mahaifin su. Mummy, Mamy wallahi mu muna da ilimi, mun kuma san daidai da ba daidai ba, in har kuna da ra’ayi babu ɗaya a cikin mu da zai baku matsala. Zamu baku goyan baya sosai in sha Allah.”
Mummy tace, “mun san da hakan, amma ni a ɓangarena gaskiya bana wannan tunanin a yanzu, ban sani ba ko nan gaba. Amma a yanzu dai zamana a cikin gidan nan yafi min komai kwanciyar hankali.” Mamy tace, “kema kenan balle ni, tunda har aka bar gidan nan ba’a raba gado dashi ba, aka barshi matsayin gidan mahaifin ku in sha Allah kamar yadda aka fitar da gawar mahaifin ku daga gidan nan haka mu ma za’a fitar da mu. Ko yanzu Nabilan Maryam da Ummin Isma’il da Nana Farida sun isa ayi musu aure, muna kai jikokin mu ɗaki mu ma sai su kai mu ɗaki?.”
Bebi yayi murmushi yace, “ba a nan take ba ai Mamy, tunda dai kunce bakwa ra’ayi shikenan, amma ko yaushe ƙofa a buɗe take in ra’ayin yin ya tashi zamu karɓe ku hannu biyu.” Yaya isma’il yace, “in sha Allah.” Mama tayi dariya tace, “Allah yasa mu cika da imani. Suka amsa amin Bebi yace, “To ni zan wuce gida” ya faɗa yana tashi tsaye. Mamy tace, “a gaishe da Manal da Ayan.” Ya amsa da zata ji ya fita.
BDƘB3P46
Bebi bayan ya fita kai tsaye wajan motar sa ya nufa dan gida yake so ya koma. “Adnan!.” Yaji Maryam tana kira sunan sa ya tsaya a jikin motar yana kallon ta tana tahowa inda yake. Ta ƙaraso inda yake tsaye tace, “Kaji abinda su Yaya suke cewa akan Kamal, ya ka ke gani?.” Ya harɗe hannayen sa a ƙirji ya jingina da mota ya ce, “To ai yanke hukunci naki ne ba nawa ba, in kina ganin zaki koma masa ki koma mana.”
“Na sani, neman shawara nazo yi wajan ka da kuma a ka ke gani, a tunanin ka ya kamata na koma ko kar na koma?.”
Yayi murmushi yace, “ai tunanin nan naki ne.” Tace, “ai na faɗa maka shawarar ka nake so.” Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “mutuncin ki na ɗiya mace da na yaran ki duka ya karkarata ne a kan komawar ki wajan Kamal, darajar ki da ta yaran ki duka tana gidan Kamal saboda abinda ya faru. Amma matsalar itace; ina jin tsoro in ya canja daga halin da kika sani a baya, ina jin tsoron kar muje daga kan ki ya cigaba da neman mata ko wani abun da yayi kama da haka. Kin fi kowa sanin halin sa, in kina ganin akwai halin sa wanda yake yi dashi a baya wanda daman bai yi miki ba zaki iya ƙin komawa, amma yadda ki ka gani”
Maryam tace, “A baya Kamal bashi da wani hali mara kyau da zance bazan koma ba saboda dashi, rabuwar auren mu ma ƙaddara ce da saurin fushi irin nasa. Amma ba wai dan saboda wani hali nasa mara kyau ba.”
Adnan yace, “to in dai har aka tabbatar yanzu bai canja hali ba zaki iya koma masa.” Maryam ta yi ajiyar zuciya tana kallon sa yace, “kar ki damu, abinda ya faru a baya bazai faru ba. Nasan zaki kiyaye matsalar da ta jawo aka samu babbar matsalar a rayuwar ki, nasan baza ki sake aikata kuskuren da kika yi ba. Shi kuma amfani yayi da wannan dama kawai, in da babu ita bazai neme ki ba.”
Maryam tace girgiza kai tace, “har abada, hakan bazai sake faruwa ba.” Yayi murmushi yace, “ina goyan baya ki koma auren sa indai har bai canja hali ba.” Tayi murmushi tana kallon sa tace, “shikenan na gode Bebi.” Yayi murmushi bai ce komai ba ya shiga mota ya bar gidan.
Da wannan fara’ar ya shiga gida yana kiran Manal tun daga falon yana cewa, “kyakykyawar Matata, kina ina?.” Faɗa yake yana shiga ciki amma bai ganta ba har ya shiga ɗakin ta, a nan ya same ta a zaune sai jan numfashi take yi alamun babu lafiya. Da sauri ya ƙarasa ciki ya zauna kusa da ita yace, “Manal Lafiya? Me ya same ki?.”
Manal cikin yanayin rashin lafiya tace, “cikina ne yake ciwo, mara ta ɗaurewa take yi.”
“Sannu, amma kin jima baki ciwon marar nan ba in zaki yi period, to yau me ya kawo shi?.” Manal tace, “haka kawai yau yake damuna, kaina ma ciwo yake min sosai.” Kallon fuskar ta yake yi yana nazari ta, tunanin sa kar fa yaje ciki ne da Manal hakan ya saka yace, “period ɗin yazo ne ko bai zo ba?.” Ta girgiza kai tace, “bai zo ba.” Ya sauke numfashi yana son yi mata allaura yana tsoron kar yaje da ciki a jikin ta.
Tashi yayi ya ɗauko mata pracetamol ya bata ta sha ya kwantar da ita a kan gadon, ya zauna a kusa da ita bayan ya ɗauko towel ya jiƙa shi ruwan ɗumi ya ɗora mata a kan marar ta. Shafa kanta yake yi tana jikin sa a haka har yaga ta fara rufe ido alamun bacci zata yi ya cigaba da shafa kanta har tayi bacci.