Sashe 55
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya jima sosai a haka sai da ya kira Dr Fulani ya dubo masa ita ya tabbatar da numfashi nata yayi sama sannan hankalin sa ya ɗan kwanta. Huzaifa ne ya shigo yace, "Bebi ka nustu kaje gida zan kula da komai a nan, ga Dr Fulani ma zai kula da komai. Zaman ka a nan damuwa zai saka maka ba komai ba." Ya girgiza kai yace, "bazan iya tafiya su Mummy suna nan ba."
"Haƙuri zaka yi, zaman ka a nan babu abinda zai ƙara maka sai damuwa, kuma Mama baza ta baka damar zuwa inda take ba, haƙuri zaka yi ka tafi."
Yayi shiru bai ce komai ba Huzaifa ya dinga bashi baki a haka ya fito ya tafi gida hankalin sa gabaɗaya baya jikin sa.
Yana ajjiye motar ya shiga cikin gidan ya samu falon babu kowa bai bi ta kan Manal ba ya shiga ɗaki dan bashi da nutsuwar sauraren ta a wannan lokacin. Manal kuka yake yi kamar ranta zai fita, hankalin ta ya tashi sosai jikin ta har rawa yake yi saboda kuka.
Kukan Ayan yake ji yayi yawa soaai ya saka shi ya fito ya shiga falon nata yaga bata nan ya shiga ɗaki ya hango ta a zaune tana kuka gashi a jikin ta shima yana kuka. Daƙyar ya iya cewa, "ki bar wannan kukan ki kula da Ayan kina ji yana kuka."
Tayi masa banza kamar bata ji abinda yace ba, Bebi yace, "ba magana nake miki bane?." Nan ma tayi masa banza ransa ya ƙara ɓaci cikin faɗa yace, "ba magana nake miki bane? Kina jina kin min banza tsabar kin raina min hankali?."
"Eh ina ji ɗin. Bazan amsa bane sai me?" Ta faɗa cikin matuƙar faɗa da fusata itama.
"What!" Ya furta yana kallon ta jin abinda take cewa kafin yayi magana Manal tace, "Meyasa ka munafurce ni ka ɓoye min maganar ka da Rumana? Meyasa baka faɗa min aurena da kai shekara ɗaya kawai ka ke jira ka kawo wata ta tare ba?" Tayi wani murmushi takaici tana kallon sa tace, "shiyasa ko yaushe cikin damuwa ka ke akan ta, in na tambaya ka ɓoye min ashe kai ka san munafurcin da ka ƙulla ka kasa faɗa min, Meyasa ka zaɓe ni? ai da ka sani ka ɗauke ta tunda ita ƴar uwar ka ce kuma wacce ka fara so a duniya. Ni daman na san akwai munafurci a lamarin ka kai da ita, yanayin kallon da take maka da yadda ka ke faɗar sunan ta daman na san za'a zo wannan gaɓar, da nayi magana kace kai ba haka ba ashe ka san abinda ka ƙulla ka munafurce ni baka faɗa min ba" Manal ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai da nuna zallar fusatar da take ciki.
"Munafurci!" Ya maimaita a zahiri yana kallon ta cikin ɓacin ran da ya ninka nata. Manal cikin ɗaga murya tace "munafuci, ka munafurce ni, na sake faɗa ka munafurce ni. Daman tun da ni nasan za'a zo nan saboda yadda alaƙar ku take, meyasa ka zaɓe ni wai? Meyasa baka zaɓe ta ba tunda itace wacce ka so kafin ni?."
Tashi tsaye tayi ta kwantar da Ayan a lokacin ya ƙaraso inda take ya ɗaga hannu zai mare ta sai kuma ya fasa ya nuna ta da yatsa yace, "in kika sake furta wannan kalmar zaki dana sani, ke wacece da zan munafurce ki?, Har kin kai matsayin da zan munafurce ki?, Wacece ke?."
"Ka mare ni mana, ko kashe ni zaka yi bazan fasa faɗar abinda yake zuciya ta, kayi min duk abinda zaka yi min. Adnan sai ka mare ni sannan zaka nuna min Rumana ta fini mahimmaci a rayuwar ka, in baka mare ni baka ƙaunar Allah. Na faɗa ka munafurce ni, meyasa baka zaɓe ta ba?, meyasa ka zaɓe ni bayan ka san ita ka ke so? Meyasa ka aure ni bayan kasan ka ƙulla munafurci a zamana da kai ba?. Na faɗa ka munafurce ni kai munafuki ne, sai mee?!."
Bai san ya tsinke ta da mari ba sai da yaga tayi baya ta haɗu da bango ya san ya mare ta, ya nuna ta da yatsa yace, "in kika sake furta wannan kalmar ta munafurci wallahi sai kin yi dana sani. kuma Ina so ki sani saboda wannan ya saka na ɗauke ki, ba dan Ayan ba da ke kin san ko kallon inda kike bazan yi ba. Kuma wallahi kika sake yi min wata magana sai na yi miki abinda naki taɓa tunani ba."
Manal hannun ta na kuncin ta tana kallon sa tana kuma tace, "ka mare ni?." A fusace yace, "na mare ki ko zaki rama?" Ya faɗa cikin faɗa sosai.
Kuka take yi sosai muryar ta har bata fita saboda kuka tace, "da ka sani baka zaɓe ni ba, yanzu ma kana da ikon saki na ka aure ta sai ka bar mata Ayan ɗin ta kula dashi. Kuma kalmar an munafurce ni bazan fasa faɗa ba. Ka munafurce ni na maimaita ka yi duk abinda zaka yi, munafuki ne kai na faɗa, in kaga dama ka kashe ni kar ka barni da rai."
Dafe kai yayi zuciyar sa nayi masa mugun zafi akan kalaman ta, hannun sa rawa yake haka zuciyar sa tunzura shi take ayi akan ya buɗe bakin da hannun sa na jan gangar jikin sa zuwa jikin ta. Ganin bai ce komai ba sai jikin sa da yake ɓari ta bishi da harara da jajayen idanun ta tace, "kuma wallahi bazan kwana a gidan nan ba, in na fita ka kawo Rumana ta cigaba da zama da kai, amma ni wallahi bazan zauna ba."
"In kinga dama kar ki sake kwana daga yau, in kin ga dama in kin tafi kar ki dawo, in kin ga dama daga nan in kin fita ki bar duniyar. Stupid girl wacce bata san abinda take yi ba" ya faɗa yana fita ya barta dan in ya cigaba da zama zai iya yin abinda zasu yi dana sani shi da ita.
Manal ta ɗauki jakar goyon Ayan ta ɗaura a jikin ta aaka hijjabi ta, ta saka shi a jakar goyon tana kuka sosai jikin ta har rawa yake yi, ta ɗauki key na mota ta fita a guje. Fitowar sa daga banɗaki kenan yaji fitar ta da mota da mugun gudu.
BDƘB3P33
Manal tana fita daga estate ɗin taja ta tsaya tana kuka sosai, kanta ta kifa akan sitiyarin motar tana kuka cikin baƙin ciki da kishin da yake damun zuciyar ta. Kallon Ayan tayi da yake kwance a kajerar gaba ta gyara masa kwanciya ta jingina da kujera tana kuka.
Tunani take yi ina zata je?, Gidan Mama ne yazo ranta ta girgiza kai a zahiri domin baza ta iya zuwa wajan Mama tace ta baro gidan mijin ta ba, kuma tana da tabbacin Baba bazai barta ta kwana ba. Gidan Adda Halima wacce suke cewa Mummy nan ma taga baza ta iya zuwa tace mata ai faɗa suka yi da mijin ta ba, ta sauke numfashi gidan Daddyn ma yazo ranta taga shima baza ta iya zuwa ba.
Ƙwanƙwasa glass ɗin motar akayi hakan ya saka ta kalli masu ƙwanƙwasawa taga vegilanty ɗin da suke gadin estate ɗin ya sauka ta sauke galss ɗin ya kalli Manal yace, "Hajiya lafiya kika tsaya a nan?." Manal ta goge idon ta tace, "lafiya lau, zan je duba Mamana ne nata jin daɗi."
"Amma Hajiya da kin fito da driver naga kina cikin wani yanayi."
"Babu komai yanzu zan ƙarasa."
"Allah ya kiyaye" ya faɗa yana matsawa ta ɗaga glass ɗin motar kawai ta wuce gidan Huzaifa.
Tana shiga gidan ta faka motar ta ɗauki Ayan ta shiga ciki a nan ta tarar Ayra ƙanwar su tana gidan. Zama Manal tayi a falon matar gidan da take fitowa daga ɗaki tace, "Ahh Manal kece tafe da daren nan?." Yanayin fuskar Manal ɗin kawqi ta kalla tasan akwai damuwa, dan ɗaga mata kai kawai Manal ɗin tayi sannan tace, "ina wuni."
"Lafiya lau, kawo Ayan ɗin" ta faɗa tana karɓar sa idanun sa biyu yana ya kalle-kalle. Manal shiru tayi tana kallon wani wajan daban, ganin hakan sai bata ce mata komai ba dan yanayin ta ya nuna ba lafiya ba. Ganin shiru yayi yawa sai tace, "Manal ki shiga ciki ji huta mana" ya faɗa tana kallon ta kafin ta kalli Ayra tace, "Ayra raka ta ɗaki."
Manal ta tashi ta shiga ciki ta barta da Ayan a hannu, ya jima a wajan ta kafin ta kai mata shi. Huzaifa bai san tana gidan ba dan ya jima bai dawo ba har dare, ko da ya shigo bacci yayi bata sanar dashi zuwan Manal ɗin ba sai da safe suna breakfast ta kalle shi tace, "Beb Manal fa a gidan nan ta kwana."
Kallon ta yayi da mamaki yace, "wacce Manal ɗin?." Tayi dariya tace, "wacce Manal ka sani? Ina tunani a kaf duniya ita kaɗai ka sani mai suna Manal." Ya ajjiye cokalin hannun sa yace, "Wai Manal matar Bebi?." Matar sa tayi dariya tace, "ita fa, tazo tun dare da ganin ta kasan akwai damuwa sosai. Ban tambaye ta abinda ya faru ba, kuma har yanzu bata fito ba na ji kukan Ayan dai."
Huzaifa yace, "Subahanallah! Allah ya sa lafiya." Ta amsa da amin sai ga Manal ɗim ta fito ita da Ayra Ayan a hannun ta. Zama tayi akan kujear falon ba tare da ta ƙarasa dining ɗin ba tace, "Yaya Huzaifa ina kwana." Ya kalle ta yace, "lafiya lau Manal, ya Ayan ɗin?."
"Lafiya lau, ina kwana Antyn mu" ta faɗa tana kallon matar sa. Ta amsa da murmushi tace, "ai na shiga naga bacci ki ke har Ayra ɗin, ga breakfast ɗin ku."
Manal tace, "na jima ban yi bacci ba jiya shiyasa." Waya ake yiwa Manal ta ɗauka bayan ta kashe ta kalle su tana cewa, "delivery man ne, bara na karɓo saƙon" ta faɗa tana tashi ta fita. Jim kaɗan sai taga ta dawo da leda a hannun ta tana zama.