Sashe 13
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya kalli Bebi da yake kallon wani wajan daban kamar bai amince da abinda ya faɗa masa ba sai yace, "abinda na faɗa maka gaskiya ne Bebi, ka daina kokwanto a kan maganar ban tsallake maka komai a ciki ba na faɗa maka iya abinda zaka fahimta. Matar ka ba jinina bace, nace maka ƴata ce saboda ƴar tawa ce tunda a wancan lokacin bani da aboki kamar mahaifin ta. Kuma ni ne na karɓi auren mahaifiyar ta ni na zama waliyin mahaifin ta, kai hatta Fatima ni na ce a zaɓa mata a madadin Zahra kamar babar ta."
Bebi ya girgiza kai cikin gamsuwa yana mamaki a zuciyar sa, Daman shekarun baya da suka cewa akwai macuta masu cutar da marayu?, Shi ya ɗauka a yanzu zamanin ya lalace ake cin dukiya ta halak da ta haram, ashe tun a da akwai su tunda gashi harda mahaifin sa ma a cikin su.
Bebi ya kalli Abban sa da yake kallon sa yace, "Abba bawai ban amince da abinda kace bane ina so kawai ina so naji gaskiya akan maganar, don Allah baka ci komai a dukiyar ta ba?." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, "zare a dukiyar ta bai zo hannuna ba Adnan, yadda ya kawo min haka ya koma da abar sa dan ban karɓa ba." Bebi ya sauke ajiyar zuciya cikin rashin sanin abinda zai ce, gabaɗaya ya kasa furta komai mamaki yake a zuciyar sa yana jin kamar akwai wani abun a ƙasa bayan wannan. Abba ya kalle shi yace, "babu lallai ta amince ta baka Manal tunda ta san ni na haife ka, tana jin haushina sosai a zuciyar ta kuma nasan zata ji, duk da ban ci komai ba amma dani aka tsara guduwa a barta. Kuma da na koma bai kamata ace na barta ba ko me zata yi min saboda nasan a inda muka ɗauko ta, ban yi hakan ba na dawo gida na barta ba tare da nayi tunanin illar da hakan zai haifar ba."
Bebi gaban sa sai faɗuwa yake sosai ya ja numfashi ya fesar yace, "in sha Allah Abba wannan ya wuce."
BDƘB3P08
Abba ya kalle su gabaɗayan su cikin nauyin zuciyar da ya tokare masa ƙirji ya hana shi sauke numfashi, daƙyar ya iya jawo numfashin ya fesar ya kana bin su da kallo jikin sa ya sake yin sanyi sosai yace, "dare ya yi zaku iya tafiya gida." Bebi ya girgiza kaiyace, "Allah ya ƙara lafiya." Duk suka amsa da amin suka tashi kowa ya fito. Suna tafiya a harabar gidan shi dasu Yaya isma'il suna ta bashi baki da tabbacin Manal zata dawo gare shi cikin sigar kwantar da hankali.
Rabuwa suka yi dasu a wajan ya shiga wajan Mama su kuma suka wuce gida. Yana shiga falon ya tarar babu kowa sai kawai ya tsaya a falon yana kallon waje ɗaya ba tare da ya zauna ba, yayi shiru baice komai ba yana kallon wani wajan daban kamar mai karanta wani abun. Mama ce ta fito daga ɗaki a tsaye tace, "Bebi baka wuce ba?." Ya kalle ta ya sauke numfashi yace, "Mummy ina nan, yanzu dai zan wuce."
Ta kalle shi tace, "har yanzu hankalin ka bai kwanta ba? Naga yanzu ka san gaskiya Manal ba jinin ka bace akwai aure tsakanin ku, meyasa ka ke cikin damuwa kuma?."
"Mummy Maman Manal baza ta amince da dawowar ta gare ni ba."
Mummy cikin lallashi tace, "zata amince in sha Allah. Abun ne akwai ciwo sosai, ɓacin rai ne ya saka ta take faɗa maka haka. Amma in sha zata amince ai ba laifin ka bane ba." Cikin karaya da sanyin jiki Bebi yace, "Anya kuwa Mummy? Sai nake ji kamar akwai abinda Abba ya rage a labarin nan bai faɗa mana ba."
Mama tace, "Nima haka nake ji, Amma wannan tsakanin su ne kaima tsakanin ku daman. in sha Allah zata baka matar ka farin cikin ka ya dawo kamar da. Ni ko su Hajiya ban faɗawa ba wallahi, cewa nayi saboda yanayin aikin ka yana zuwa na dare ga laulayin ciki shiyasa ta koma gida."
Wani iri yaji a jikin sa jin Mama ta san da maganar cikin, ya kalle ta kaɗan dan shi ya san bai faɗa mata ba yayi mamaki da ta san dashi. Kunya ce ta kama shi ya ɗan kawar da kansa gefe yana jin nauyin Mummy a jikin sa sosai. Mama ta fahimta sai tayi murmushi tace, "Allah zai kawo mafita kar ka damu."
Bebi yace, "Allah ya amince."
"Amin ya Allah. Ina zaka je yanzu? A nan zaka kwana ko gida zaka wuce?."
"Asibiti zan je, Manal ɗin ce a kwance babu lafiya, ɗazu yayar ta take sanar dani. Ɗazu da ban zo da wuri ba ma nan naje shiyasa na ɗan jima." Mama tace, "Subahanallahi! Me ya same ta?."
"Rashin cin abinci ne da damuwa." Mama tace, "wayyo Allah, Allah ya bata lafiya." Ya amsa da amin tace, "a asibitin ku take?."
"A'a, wani clinic ne nan kusa dasu."
"Amma kafin kaje ka fara cin abinci mana, kaima ai ba ci ka ke ba."
Yace, "Naci ɗazu Mummy, bana jin yunwa yanzu." Mama tace, "kawai dai damuwa baza ta barka ci ba." Ya murmusa baice komai ba ya fita bayan ya mata sallama.
Yana shiga asibitin ya tarar da Manal ta farka tana zaune ita da Mubeena a ɗakin, da sallama ya shiga ɗakin jin maganar sa sai ta kalle shi suka hɗa ido, murmushi yayi mata mai kashe jiki ya kalli Mubeena da take zaune bayan ta amsa sallamar yace, "Sannu Yaya, ya jikin nata?."
Mubeena tace, "jiki da sauƙi, yanzun nan ta farka tana tambayar ka." Ya ƙarasa ya zauna a kan kujera yana kallon Manal yace, "sannu." Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba yace, "me yake damun ki yanzu?."
"Babu komai" ta faɗa a hankali.
"Kin tabbatar babu?." Ta ɗaga kai alamun eh babu ɗin.
Mubeena tace, "Sun ce dan ma dare yayi ne da zasu iya sallamar mu yanzu saboda ta samu lafiya, amma da safe zamu tafi in sha Allah." Bebi ya girgiza kai yace, "Allah ya nuna mana lokacin." Ta amsa da amin tana cigaba da danna wayar ta. Kiran ta akayi a wayar hakan ya saka ta tashi ta fita dan taga su ma suna buƙatar space.
Tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna a gefen ta ya riƙe hannun ta yace, "akwai abinda kike so ki ci?." Ta kwantar da kanta a kafaɗar sa tace, "babu." Bebi ya ɗora hannun sa a kanta yace, "in akwai ki faɗa min, kinga ba abincin kirki kika ci ba." Kai ta girgiza kawai ya sauke numfashi yana shafa fuskar ta yace, "in sha Allah komai yazo ƙarshe, kar ki damu."
Tashi tayi daga jikin sa tana kallon idon sa tace, "na kasa cika alƙawarin da na yiwa Mama, na cewa Mama zan barka tunda hakan take so amma na kasa yin hakan, so nake kawai na ganka a kusa dani fiye da komai. Ina son yiwa Mama abinda take so" ta faɗa hawaye na sakkowa daga idon ta.
Murmushi yayi ya saka hannu ya share mata hawaye yace, "Ɓacin rai ne ya saka tace miki haka, Amma nan gaba da kanta zata ce nazo na sauke ki mu tafi gida Manal. Mama tana son zaman ki dani Manal, kawai ɓacin rai ne ya saka take cewa ki rabu dani, Amma wallahi tana son ki zauna dani sosai."
Manal ta kalle shi tace, "ta ya akayi ka sani?." Bakin sa ya ɗora a kan nata yayi mata kiss na sacannin da basu wuce biyu zuwa uku ba ya janye bakin sa yace, "saboda haka abin yake Partner. Ni babban farin cikina da na tabbatar dani sake babu alaƙar jini balle ace aurena sake ya haramta, wannan shine farin cikin da naji fiye da tunanin ki kuma hankalina ya kwanta. Duk wata matsala in ba wannan ba zamu shawo kanta daga baya."
Manal jin bakin sa take har lokacim a kan nata, Allah ya sani abinda take da buƙata kenan a wajan sa amma ta kasa bayyana masa hakan, dan gani take in ta bayyana ma bashi da amfani tunda basa gida kuma babu kwanciyar hankalin da hakan zai faru. Ya lura da idanun ta suna lumshe tunda ya mata kiss har ya gama magana bata buɗe ido ba, lumshe ido yayi ya buɗe dan kuwa tunda cikin ta ya bayyana y lura tana son zama inda yake sosai, tana son kwanciya a jikin sa duk da daman haka take tana da son jiki sosai, amma na yanzu yafi na baya.
Fuskar ta ya riƙe da duka hannun sa yana shafa kumatun ta da yatsun sa yana kallon idon ta shigar kwantar da hankali da tausasa murya irin ta masoyan da suke cikin shauƙi yace, "me ki ke so?." Ta sauke ido ƙasa ta ɗora hannun ta a kan nasa saboda sanyin hannun sa yayi mata daɗi. Ganin tayi shiru bata ce komai ba yace, "ina jin ki, me kike so?." Ta girgiza kai alamun babu yace, "ban yarda ba, faɗa min me kike so, uhmm."
Baki ta turo gaba bata kalle shi ba yayi murmushi mai sauti ya mata kiss a goshi yace, "faɗa min mana, baki taɓa faɗa ba tunda muka yi aure, faɗa min yanzu zan ji daɗin hakan." Hannun ta saka ta zagaya dashi bayan sa ta kwantar da kanta a ƙirjin sa tana jin yadda zuciyar sa take bugawa a kunnen ta tace, "ni ban san me zance ba."
"Kin sani, faɗa min ko meye zan samo miki shi." Sake gyara kwanciya tayi a jikin sa tace, "ina kewar ka, bugun zuciyar ka na kwantar min da hankali sosai, bana so na daina jin sa a kunnena, tana bani nustuwa sosai."