Sashe 34
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya kalle ta ya ce, "Mummy don Allah ki daina wannan maganar, kina da ikon sakani nayi duk abinda kike so koda ni bana so, ki yi haƙuri ba haka nake nufi ba." Tayi tsaki tace, "bani da wannan ikon, da ina dashi baza ka kalle ni kace min kai ka ɗauka an bar maganar auren ka da Rumana ba."
"Don girman Allah ki daina wannan maganar, wallahi babu abinda zaki ce nayi ban yi miki ba, ki yi haƙuri."
"in dai hakan ne kayi abinda nake so, ka auri Rumana yanzu ba nan gaba ba. Saboda kai ta samu ciwon zuciya amma komai ko a jikin ka, to bazan bari na rasa ta ba saboda kai, auren nan za'ayi a yanzu dan bazan bari a ɗauki lokaci ba Adnan."
Bebi jikin sa ya gama yin sanyi Manal kawai yake tunani ba kowa ba, in ba dan ita ba zai amince a lokacin ma a ɗaura masa aure da Rumana, sai dai kash in ya tuna Manal sai yaji komai ya fita daga ransa lokaci ɗaya. Amma ya zai yi? hakan zai daure ko da baya so, zai san hanyar da zai bi wajan faɗawa Manal halin da ake ciki duk da ya san baza ta taɓa fahimtar sa ba. A hankai ya ce, "To Mummy, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" ya faɗa kamar zai yi kuka. Mama ta kalle shi jin yadda yayi maganar tace, "Allah ya yi maka albarka." Ya amsa da amin a lokacin wayar sa take ƙara.
Ganin Huzaifa ne sai ya ɗauka yayi shiru alamun ana yi masa magana kafin ya ce, "to yanzu zan koma gida sai kun zo" ya faɗa yana kashewa ya kalli Mama yace, "ƴan gidan su Huzaifa ne zasu zo, zasu zo har nan gaishe da Abba." Mama tace, "Allah ya kawo su lafiya."
"Amin, zan koma dan na tarbe su."
"sai ka dawo." Miƙewa yayi ya fita zuciyar sa sai bugawa take yi.
A haka ya tafi gida cikin sanyin jiki da rashin walwala da kuma bugawar zuciya, jikin sa har zafi yayi saboda tashin hankali dan bai san da wacce fuska zai yiwa Manal bayani na. Da ya shiga gidan ya faka motar ya fito yashiga cikin gidan.
Mama ya samu a zaune a falon da Ayan a hannun ta tana saka masa kaya suka gaisa da girmamawa yana yi mata sannu da aiki tace, "Manal ɗin ai tana ciki."
Bai shiga ba sai ya koma ɗakin sa saboda haka kawai yake jin kunyar ta, haka kawai yake jin bazai iya haɗa ido da ita ba domin babu adalci a abinda yake shirin yi mata.
Mama ganin bai shiga ba kuma Manal bata fito ba sai ta ƙwalawa Manal kira tana fitowar tace, "mijin ki ya dawo." Manal ta sauke numfashi dan har lokacin haushin jiya bai bar zuciyar ta ba, ta wuce ta shiga ɗakin nasa ta same shi a zaune ya zubawa waje ɗaya ido alamun tunani.
Sallama tayi hakan ya saka ya kalle ta sai ya tashi tsaye yana kallon ta, ta ƙaraso inda yake tana kallon sa itama kamar yadda yake kallon ta, ganin kallon da yake binta dashi kamar wanda ya jima bai ganta ba sai tace, "lafiya? Jikin Rumana ɗin ne ya tashi?." Jin abinda tace sai kawai ya jawo hannun ta ya rungume ta a jikin sa, tayi sak gaban ta yana faɗuwa sosai ba tare da ta san dalilin faruwar hakan ba.
Bugawar da zuciyar sa take yi take jin sautin ta har cikin kunnen ta gashi ya riƙe ta sosai a jikin sa kanta yana kwance a ƙirjin sa a daidai saitin zuciyar sa. Ɗagowa tayi daga jikin sa ta ɗora hannun ta a saitin zuciyar sa tace, "lafiya zuciyar ka take bugawa haka? Me ya faru?." Kallon idanun ta kawai yake yi kafin ya ɗauke ido, ya kulle idon sa ya buɗe ya sake kallon ta yaga dai shi take kallo har lokacin tace, "ka faɗa min me ya faru, zuciyar ka na bugawa sosai alamun kana cikin tashin hankali, me ya faru Partner?."
"Ina sonki Manal" abinda yace kenan yana sake mayar da ita jikin sa tare da zagayawa da hannun sa ƙugun ta, faɗar hakan da yayi sai ya sake tsorata ta ta riƙe shi amma zuciyar ta na ta kawo mata abubuwa kala-kala akan hakan.
Ɗago ta yayi daga jikin sa yana kallon ta yace, "Huzaifa da ƴan gidan su zasu go ganin Ayan, a samu ayi musu abinda zasu ci ko ya ya ne." Ta riƙe hannun sa duka biyun tace, "kafin wannan, meye damuwar ka?."
"Kar ki damu ba wani abun bane, zan sanar dake bara su zo baƙin su tafi." Manal tace, "amma ka tsorata ni, da zaka faɗa min yanzu zan fi jin daɗi." Ya murmusa kaɗan yace, "kar ki damu." Manal ta sauke numfashi tace, "Sury tana nan, bara naje sai a san abinda zaa yi. Na kawo naka abincin?."
Ya girgiza kai yace, "bana jin yunwa."
"Amma baka ci komai ba tun safe."
"Na sha tea da naje office."
"Amma tea ba abincin ka bane, gwara ka ci abinci." Ya kalli hannun ta da yake cikin nasa ya ce, "in su Huzafa sun zo sai mu ci gabaɗaya."
Ta zame hannun ta daga nasa tace, "to bara naje." Ya girgiza kai bai ce komai ba ta fita. Ya zauna a gefen gadon ya ce, "taya zan faɗawa Manal Mummy?, Mummy ta ya zan cewa Manal zan auri Rumana a cikin kwanakin nan?" Ya faɗa yana dafe kansa cikin damuwa mai yawa.
BDƘB3P19
Abba ko da ya fita babban store ɗin sufi mart yaje da yake zoo road saboda abinda yake so zai siya, yana son fita da kansa dalilin da ya saka bai saka an kai shi ba ya dauƙi driver ba ya tafi da kansa. Yana cikin duba abinda yake so ya hangi Mubeena daga ɓarin turaruka ita da ƙawar ta Bily suna kallon wani turare suna dariya.
Jikin sa ne yayi sanyi sosai ya kulle ido ya buɗe a kan su yana jin nadama da dana sanin abinda ya aikata. Godiya yake ga Allah da bai bashi ikon aikata wani abun da Mubeena ba, duk da jajircewar tace ta kawo hakan da an biye tashi da yanzu wataƙila ya ɗauki wuƙa ya cakawa kansa saboda baƙin ciki.
Ajiyar zuciya yayi yana kallon ta har lokacin tana wajan sai dai ta matsa gaba daga inda take tsaye, kulle ido yayi ya buɗe ya tattaro nutsuwar da ya samu ƙarfin guiwar nufar inda take da niyar neman afuwar ta. Kasancewar ta juya baya tama ɗaukar turare bata ganshi ba sai maganar sa taji a bayan ta yace,"Mubeena." Juyowa suka yi ita da Bily dariyar da take yi ta tsaya ganin wanda yake gaban su a tsaye. Mubeena ta ɗaure fuska matuƙa ta juya ta cigaba da abinda take yi bata kalle shi ba.
Ganin hakan sai Abba yace, "Ba wani abun zance ba Mubeena, zuwa nayi nace miki...." Da sauri ta juyo tace, "kace min me? Meye nayi min magana bayan na riga na manta da abinda ya faru a baya?, Na manta da kai a cikin rayuwata, na share ka na cigaba da mu'amala da dangin ka saboda ɗan ka Adnan!. Shi ɗin mijin ƙanwata ne, bana son wata hatsaniya ta haɗa ni da kai saboda matsayin da ka ke dashi a wajan ƙanwata, amma ba dan haka ba baka isa ka tsaya a gabana kana yi min wata magana ba."
Abba ya girgiza kai ya ce, "na sani, amma ki yi haƙuri da abinda ya a baya faru."
"Wannan ai bani ta shafa ba kai ta shafa ba wani ba, kai zaka ga sakayya da idanun ka tun a duniya ba wani ne zai gani ba. Ko iya kunyar yaran ka ma ta ishe ka a duk ranar da halin ka ya bayyana a gare su. Sannan ina so ka sani Adnan ya san komai, duk abinda ka ke ɓoyewa Adnan ya sani. Har ni Mubeena ya samu da maganar ka, kasancewar ka mahaifin a wajan sa ya saka ban furta komai a kan ka ba saboda duk lalacewar ka kai ka haife shi, amma wallahi da wani ne daban bashi ba da na haɗa kai dashi na wanke tas. Ka gode Allah da ban faɗawa Mama abinda ya faru tsakanina da kai ba, da ta sani yafe maka ɗin da tayi wallahi baza ta yafe ba, sannan kuma dole ta raba auren ƙanwata da ɗan ka" ta faɗa tana kallon Bily.
Bily tace, "Mubeena zo mu tafi, kar mu tarawa kan mu jama'a" ta faɗa tana jan hannun ta suka bar wajan. Abbba ya tsaya a wajan kamar an dasa shi a wajan, babban abinda ya saka ƙafafun sa yin sanyi da yaji Adnan ya san maganar Mubeena. Zuciyar sa bugawa take yi sosai bai iya siyan abinda yazo siya ba ya fito ya tafi.
*** Manal koda ta bar wajan Adnan wajan Surayya taje ta faɗa mata abinda yaje faruwa suka shiga kitchen tare suka dan yi fan cake da yake shi bashi da wahala. Aikin gabaɗaya Surayya ce tayi Manal tana daga zaune ne kawai tana kallon ta, ba jimawa aka gama aka zuba an abu mai kyau suka ajjiye.
Mama ce ta shigo tace, "ku ace muku za'a yi baƙi tun daga wata ƙasa amma ku rasa ne za'a basu sai cake? Ina laifin ayi abinci?." Surayya tace, "haka nace nima, Sai tace yace ayi abinda ya samu kawai." Mama ta kalli Manal tace, "ya faɗa ne ai kawai amma ba wai dan kar ayi ɗin ba, iyayen aminin sa ne fa zasu zo, kuma daga wata ƙasar zasu zo sai mu rasa me zamu basu sai fancake?."
"Mama ba sai a haɗa musu da naman sunan can ba?tunda akwai sai sake soya shi saboda kar yayi tauri da yawa."