Sashe 8
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba bai jima da dawowa daga Katsina ba yana zauna shida Mama Mubeena ta kawo masa abinci kafin ya fara ci ya kalli Mama yace, "ni ba wannan ba, ina shigowa unguwar nan da abinda aka fara tara ta dashi shine Manal kwanan ta biyu a gidan nan. Da gaske ne Manal ta kwana biyu a gidan nan?."
Mama cikin mamakin halin mutane tace, "ikon Allah, Mutane da gulma suke, har a san ta kwana biyu a gida?." Baba yace, "kiwon mutum ake yi ba dabba ba ai, me ya faru tayi kwana biyu a gida? Adnan ɗin ne yayi tafiya ya turo ta nan?." A lokacin Manal ta fito a guje daga ɗaki, kafin ta kai ga inda fanfo yake ta fara shara amai a tsakar gidan hannun ta na dafe da kanta da kuma cikin ta saboda yadda take ji kamar basa jikin ta.
Da hanzari Baba ya tashi Mubeena ma ta fito daga ɗaki ta ƙaraso wajan ta Baba yace, "Subahanallahi! Manal daman baki da lafiya ne?." Mubeena ta riƙe ta ta kwanta a jikin Mubeena Baba ya taɓa wuyam ta yace, "Zazzaɓi ne a jikin ta sosai, Mubeena daman bata da lafiyq ne? Ko daman rashin lafiyar ce ta saka ya kawo ta gida?." Kafin Mubeena tayi magana sai yace, "Ko da yake mai zai saka ya kawo ta gida dan bata da lafiya shi da yake likita?."
Baba ya sake cewa, "An je asibiti kuwa?." Mubeena tace, "ba'a je ba, amma akwai maganin da take sha. Rashin cin abinci ne ya mayar da ita haka wallahi, bata son cin komai tunda tazo nan." Baba yace, "meyasa bata ci? Bata samu abinda take so ba?." Mama da take gefe tace, "Laulayin ciki fa take yi, sai a hankali."
Baba ya kalli Manal ya sake kallon Mama yace, "duk da hakan dai, jikin ta akwai rashin lafiya ba iya na ciki bane wannan." Ya kalli Mubeena yace, "ga kunu can ki bata tasha sai yafi shayi riƙe mata ciki, in ta sha sai ta sha magani, in bata daina jin ciwon ba sai mu je asibiti. Kama ta ki shiga ciki" Baba ya faɗa yana ɗago Manal daga zaunen da take Mubeena ta riƙe ta ta shiga da ita ciki.
Baba da kansa ya ɗebo ruwa ya zubawa wajan da tayi aman duk da babu komai a aman sai ruwa saboda babu abincin kirki. Wajan Mama Baba ya dawo ya zauna ya kalle ta a nutse yace, "baki faɗa min ba, me take yi a gidan nan a wannan halin?."
Mama tace, "auren su ne ya ƙare." Da mamaki Baba yace, "kamar ya kenan? Sakin ta yayi ko me?."
"Bai sake ta ba, Amma zai sake ta ɗin."
"Ki min bayani na gane mana!" Ya faɗa yana ɗaga murya kaɗan.
Mama tace, "daman ka san Ibrahim shine mahaifin wanda ka bawa auren Manal?." Baba yace, "eh Mu'azzam Alhasan shine mahaifin sa, meye aibu a nan?." Mama ta girgiza kai tana kallon sa tace, "to shine na ta mahaifin ta."
Baba ya kalle ta da hanzari cikin faɗuwa gaba da tashin hankali yace, "ban gane ba." Mama tace, "ina nufin shine uban ta itama."
"Ban yarda ba, taya ya zama mahaifin ta bayan nasan shi mahaifin ta ba haka sunan sa sa yake ba? Kar ki dagula min tunani ki faɗa min gaskiya abinda yake faruwa."
Mama tace, "ai ban taɓa yi maka wannan wasan ba, tunda kaji na faɗa ka amince kawai in ba haka bane ai bazan faɗa ba. Auren ta da Adnan ya ƙare ko tana so ko bata so, saboda Adnan matsayin Yayan ta yake kuma kasan babu aure tsakanin Yaya da ƙanwa a musulunci." Baba ya bi Mama da kallo haka kawai yaji bai abince da abinda tace ba ko kaɗan. yace, "meyasa nake jin ban amince ba da abinda kike faɗw ba?."
Mama ta tashi tsaye tace, "kuma gaskiyar kenan ba" ta faɗa tana wucewa ciki. Baba yayi shiru yana tunani kafin yace, "Hakan bazai yu ba, akwai abinda take ɓoyewa amma zan gano shi."
*******Bebi yana zaune gaban Abba kamar yadda ya saka a kira masa shi tunda suka gaisa bai ce masa komai ba. Ya jima a zaune yana jiran yaji mai zai ce shi kuma bai ce a saboda nauyin da yake a zuciyar sa bakin sa ya kasa furta komai.
Sai daga baya sannan Abba yace, "Kana ta jiran tsammani ko Adnan? Nasan zuciyar ka tana cike da tashin hankali da wasuwasi akan auren ka da matar ka, ni kaina a wannan halin nake. Amma kafin nan ya maganar Kamal?."
Bebi yace, "an gama da maganar Abba, duk dai ban bibiyi lamarin sosai ba saboda yanayim da nake ciki, Amma komai ya ƙare shi kansa Kamal ɗin yayi nadamar abinda ya aikata." Abba ya sauke ajiyar zuciyar yace, "nauyi nake ji a ƙirji na Adnan, lokacin ɗaya Allah ya saukar min da wannan nauyin a zuciyata. Ku yi haƙuri kaji." Bebi ya kalli Abba yace, "Abba me akayi?."
Ya sauke numfashi yace, "komai ma anyi Bebi. Yanzu abinda zai faru ka tashi ka raka ni gidan su matar taka ina so naga babar ta." Bebi ya kalle shi da mamaki da tsoro yace, "Abba baka da lafiya bai kamata ka fita ba."
"Na sani Adnan, ina so muje ko dan kaima ka nutsu, in ban je mun yi magana da ita ba baza ka samu sauƙin abinda yake damun ka ba." Bebi ya sauke numfashi yace, "Abba ka bari kawai duk sanda ka samu lafiya sai mu je." Abba ya girgiza kai yace, "yau nake so muje kuma yanzun nan, ka Kira Yayyen ka maza mu je tare." Bebi ya amsa da to yayi musu waya da yake duk suna kusa sun taso duba Abban ba jimawa suka ƙaraso, a tare suka fito suka shiga mota zuwa gidan su Manal.
Gaban Adnan sai faɗuwa yake yi da yake shi yake jan motar zuwa gidan, tashin hankalin sa ya bayyana sosai a zahiri dannewa kawai yake yi baya nunawa, Babban tashin hankalin sa ace Manal ƙanwar sa ce, ji yake zai iya yiwa kansa illa a lokacin da abinda yake gudu ya zama gaskiya, zuciyar sa zata iya bindiga nan take ta tarwatse.
A ƙofar gidan su Manal ya faka cikin ikon Allah aai ga Baba yana niyar shiga gidan, ganin sa sai Bebi ya fito yana yi masa magana. Baba ya tsaya ya juyo yana cewa, "A'a Adnan kai ne tafe?." Suka gaisa da Baba ya amsa da fara'a kafin Bebi yace, "tare muke da Abbana, yace yana son magana da Mama ne shiyasa muka zo."
Baba yace, "to jira ni, bara na sanar da ita sai nazo mu shiga." Kafin ya shiga gidan har Abba sun fito daga motar, Baba ya tsaya suka gaisa sannan ya shiga ciki.
A falon ya tarar dasu Manal na shan tea kamar tana shan maɗaci sai yatsina take yi, ya shiga da sallama ya kalli Manal yace, "Manal ya jiki naki?." Manal tace, "da sauƙi."
"Allah ya ƙara sauƙi, ki daure ki dinga cim abinci kin ji?." Ta daga kai alamun to.
Baba ya kalli Mama yace, "Adnan da mahaifin sa suka zo, suna waje suna son shigowa saboda subyi magana dake." Mama ta kalle shi ganin ita yake kallo tace, "meyasa yake son magana dani kuma?."
"In ya shigo sai ki tambaye shi" ya faɗa yana juyawa ya fita. Ta kalli Manal da take kallon ta tace, "Ku koma ciki."
Manal ta tashi tana riƙe bango ta shiga ciki Mubeena ma ta shiga, a lokacin suka ji sallamar Adnan da mahaifin sa da ma Yayyen Adnan ɗin.
BDƘB3P06
Sallamar mahaifin Bebi da shiga falon ya saka Mama ta kulle ido ta buɗe, ko kusa bata yi maraba da zuwan su har zuciyar ta, in ba dan Baba ba babu dalilin da zai saka su zo mata har cikin gida. Zama suka yi dukkan su kafin yayi magana Mama tace, "me kuma kazo kayi a nan? Ko kazo ƙarasa abinda baka gama ba na shekarun baya da suka wuce?."
Baba yace, "haba Zahra, ko gaisawa kya jira ayi sannan ki yi magana, wannan wacce irin magana kike yi?." Mama tace, "ko kaɗan bana maraba da zuwan sa nan balle na na tsaya a gaisa, ban shiryawa magan a yanzu ba ba kwata-kwata. Da ace na san hakan zai kasnace a yau wallahi da ban zauna a gidan nan ba." Abba yayi murmushin takaici yace, "Nima ban shiryawa hakan ba, lokaci ne yazo dole mu warware ƙullin da yake tsakani ko dan mu cire yaran mu daga duhu."
"Har wani ƙulli ne a tskaanina da kai? Wanne ƙulli zan ƙulla dakai?." Abba yace, "na san babu." Mama ta girgiza kai ta rufe ido tace, "Adnan kawai nake kallo, Amma..." sai tayi shiru bata ƙarasa ba ta ɗauke kai gefe bata ce komai ba.
Abba yace, "Nasan daman bani da darajar da zaki magana dani, rigar alfarmar Adnan da na shiga kuma na gode da hakan. Don Allah Zahra ki yi haƙuri da abinda ya faru a baya, na san ban kyauta ba daga na biyewa son zuciya amma dana sani, na kuma koma har inda kike da niyar baki haƙuri na tarar bakya nan."
Abba ya sake cewa, "ba dan ni ba saboda Allah, ga kuma saboda Adnan da ya shiga damuwa akan wannan lamarin sosai, na tabbatar itama matar tasa a yanzu haka tana cikin damuwa."
"Tsohuwar matar sa dai zaka ce, domin babu shi babu Manal" ta faɗa a fusace har lokacin bata kalle shi ba.
Abba ya numfasa yace, "Ni ne nayi miki laifi ba Adnan ba, meyasa laifina zai shafe shi?." Cikin fusata Mama tace, "saboda bana da buƙatar haɗa jini da kai da irin ka gabaɗaya, sannan...." Haɗa ido suka yi da Adnan sai ya sunkuyar da kansa ƙasa itama sai ta kawar da kanta ta fasa faɗar abinda zata ce.