Sashe 17
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗago Manal tayi ta kalle ta tace, "ɗauko wayar ki kira mijin ki ki ce masa yazo da daddare ina neman sa." Manal ta koma jikin Mama ta lafe tana kuka babu alamun tashi a tare da ita, Mama tayi murmushi tace, "sarkin kuka, ki bar wannan kukan ki yi abinda nace." Bata ɗago ba hakan ya saka Mama tace, "Yaya Mubeena bani wayar na kira shi da kaina."
Mubeena ta bata wayar Mama tana kallon wayar tace, "ban iya iPhone ɗin ba, Kira min shi" ta faɗa tana bawa Mubeenawayar. Mubeena ta kira shi ta miƙawa Mama kafin ya ɗauka, Mama ta kalli screen ɗintace, "wannan sunan yan gayu haka, Mubeena me aka rubuta?." Mubeena tace, "life partner, abokin rayuwar ta." Mama tayi dariya ta daki Manal a baya tace, "Lallai Manal, kin gado mahaifiyata. Tun Ina ƙarama na san mahaifina yana son mahaifiyata haka itama tana son sa."
Bebi yana zaune a office shigowar Huzaifa kenan kiran Manal ya shigo ya ɗauka ya saka a kunne yace, "Yaya Mubeena ina fatan ba jikin na ta bane ba?." Mama tace, "ba Mubeena ba ce Adnan, Maman su ce."
Zabura yayi ya tashi zaune sosai yace, "Mama barka da safiya."
"Barka dai Adnan, ya aikin?."
"Alhamdulillah, ya ƙarfin jikin?."
"Jiki da sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin. In kana da lokaci da daddare ka zo ina neman ka."
Adnan yace, "to Mama in sha Allah zan zo." Mama tace "Allah ya nuna mana." Ya amsa da amin ta katse wayar. Kallon Huzaifa yayi da yake a tsaye yace, "Maman su Manal ce fa, tace tana son ganina da daddare. Wallahi gabana faɗuwa yake yi sosai, Allah yasa ba wani abun gane ba."
Huzaifa yace, "kar ka damu, yanayin yadda tayi maka magana ya tabbatar daalkhairi ne in sha Allah."
"Allah yasa hakan Huzaifa, Allah yasa tace ta bani Manal mu koma gida, ni kaɗai na san illar da rashin ta ya kawo min."
"In sha Allah zata amince, shine dalilin kiran." Ya sauke numfashi ya cigaba da abinda yake yi shi kuma Huzaifa ya fasa faɗar abinda zai ce ya fita.
Mama na kashe wayar ta kalli Manal da take jikin ta tace, "zaki koma gidan ki yau in sha Allah." Surayya ce da Maman ta suka shigo falon da sallama Mama ta amsa Maman su Surayya tace, "Manal sannu ya jikin?." Manal ta amsa tana cewa, "wallahi da sauƙi Mama." Surayya tace, "Milky ya jikin?." Ta amsa suka zauna Maman Surayya tace, "lafiya dai naga yanayin ku duk wani iri?."
Mama tayi ƴar dariya tace, "yau dai na sanar dasu waye mahaifin su shine suke kuka." Mama tayi murmushi tace, "ai kuka dole ne, ni kaina nayi kuka a lokacin da na sani." Manal tace, "Au Mama daman kin sani?." Maman Surayya ta harare ta tace, "ɗauka ki ke aminitar ta mu ta wasa ce?."
Mama tayi dariya tace, "faɗa mata dai. Yanzu ma nace Adnan ɗin anjima yazo su koma gida." Maman Surayya tace, "kai amma naji daɗi hakan wallahi, ai gwara ta koma yafi kwanciyar hankali da rufin asiri, Allah ya kaimu anjiman." Aka amsa da amin suka cigaba da hira ana dariya cikin walwala.
BDƘB3P10
Bebi gabaɗaya bashi da nutsuwa tunanin sa yana ga dalilin kiran Mama, meyasa Mama ta kira shi?. Abinda zai faru kawai yake hangowa gabaɗaya ya ruɗe tunanin yaƙi barin zuciyar sa. A haka ya gama abinda zai yi wuce zuwa gida wajan Mummy, lokacin yamma tayi sosai yana shiga wajan Mummy da sallama ya same ta ita yaran ta mata suna zaune ana hira.
Amsa sallamar sukayi ya shigo ya zauna yace, "Mummy barka da yamma." Ta amsa tana faɗin, "ya aikin?."
"Alhamdulillah, ya gida?."
"Lafiya lau Adnan." Mimi ta kalle shi tace, "Yaya sannu da zuwa." Ya kalle ta kaɗan yace, "Yauwa sannu" ya sake kallon ta yace, "ke wai bleaching kika koma ne? Indai zan gan ki sai naga kin sake haske, me kike shafawa?."
Mimi tayi dariya har su Mummy Farida tace, "to ina ruwan ka? Kwanciyar hankalin auren kenan ai. Kai mun taɓa ce maka me ya saka Manal take haske?, daman ita ga haske har yaso ya yi mata yawa."
"Ji mana, ki dinga haɗawa da tabarakallah. wannan haske nata maganar ki kawai sai ya saka shi disashewa, ko yaushe sai kin tanka kuma bakya haɗawa da ma sha Allah."
Ta riƙe baki tace, "Allah ko Bebi? Lallai ka ga mai mata ko?. Taɓe baki yayi baice komai ba ya kalli Kausar da take karatu yace, "Kausar ina kika je jiya?." Gaban ta ya faɗi matuƙa ta ɗago kai alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita zatayi magana yace, "kar ki yi min ƙarya."
Kausar tace, "Gidan su ƙawata naje a nan state road."
"Me ake yi a gidan nasu?."
"Kawai zuwa nayi, ziyara na kai mata."
"Kuma duk direbobin gidan nan kaɗan suka yi miki da zaki fita da mota?." Kausar ta yi shiru yace, "bakya ji ne?." Kausar tace, "ina sha'awar tuƙa motar ne kawai shiyasa." Ya girgiza kai yace, "yayi kyau, ki cigaba kin ji, ki ɗauki halayen da ba naki ba."
"Bazan sake ba, ka yi haƙuri. Kuma kafin na fita har Mama na faɗawa sai da ta bar ni na tafi."
Ɗauke kai yayi baice komai ba ya kalli Farida sai ta riga shi magana tace, "Ni kuma me nayi Yaya?." Sai yayi murmushi itama tayi dariya ya sake mayar da fuskar sa yadda take yana kallon wani wajan daban.
Mama ta lura dashi sai tace, "Mimi kawo masa abinci." Mimi ta tashi ta kawo masa couscous da miya a kai da cole slow a gefe, karɓa yayi ya kalli abincin ya kalle ta yace, "koma ki kwashe miyar nan ki kawo min ketchup." Farida tace, "Kaii matar aure ce fa, dan ta taimaka maka ta kawo maka abinci sai ka wahalar da ita?."
"Allah ya sa aure ce da kansa" ya faɗa cikin baƙar magana yana kallon Farida. Farida tayi dariya tace, "wannan ikon Manal zaka yiwa ba ita ba." Mimi ta juya tana dariya tayi abinda yace ta kawo masa Mummyta kalle shi tace, "Wai cin couscous da zallan ketchup, ai bazan iya ba."
Karɓa yayi kafin yace Mimi ta kawo masa ruwa ta ajjiye, fara ci yayi yaci sau ɗaya sau biyu sai ya ajjiye ya dafe kansa. Mama tace, "ya jikin Manal ɗin?." Jin muryar Mama sai ya kalle ta yace, "taji sauƙi, tana gida."
"Yanzu nake faɗawa Farida su je su dubo ta ashe ta koma gida."
"Uhum ta koma" ya faɗ yana jawo yana juya spoon ɗin hannun sa a cikin abincin.
Yaya Farida tace, "ashe Mama bata san ma tana da ciki ba, nice nake ce mata laulayi take." Hararar ƙasan idanu ya yiwa Farida ba tare da yayi magana ba. Tayi dariya tace, "ƙarya nayi? Ba cikin ne da ita ba ka ke harara ta?. Ka raina ni wallahi, dan kaga har matar ka tana da ciki shiyasa ka ke ganin kan mu ɗaya." Kulle ido yayi cikin jin nauyin maganar a gaban Mama ya buɗe idon ya yiwa Faridan banza bai amsa ba. Mama tayi ƴar dariya dan ta fahimci kunyar ta yake ji ta share batun bata ce komai ba.
Wayar sace tayi ƙara ya duba sai yayi tsaki yace, "Mummy yarinyar nan bata san bana son takura a waya bane? Ƙiris nake jira nayi blocking ɗin ta." Mama tace, "wacece?."
"Ruman" ya faɗa cikin taƙaice. Mama bata ce komai ba kawai tayi murmushi dan bazai gane abinda yake faruwa ba.
Shiru ya ratsa falon babu mai magana a cikin kafin ya ture abincin a bayyane yace, "Ya Allah!" Ya faɗa yana sauke numfashi. Mama ta kalli Farida da ƙannen sa suna kallon sa dukkan su tausayi yake basu. Kallon agogo yayi yace, "Mummy zan je gida, Maman Manal ta kira ni tace tana son ganina da daddare, bayan sallar i'sha in sha Allah zan je. Allah yasa kiran na alkhairi ne na gaji da wannan tashin hankalin, daga wannan sai wannan abubuwan yawa suke min."
Mama tace, "kar ka damu kiran na alkhairi ne in Allah ya amince." Ya kulle ido ya buɗe yace, "Allah yasa Mummy, abubuwan sai sake lalcewa suke yi."
"To ya za'a yi? jarawabar kenan." ya girgiza kai ya tashi ya fita.
Kamar yadda ya faɗa bayan sallar i'sha yayi kwalliya cikin manyan kaya harda hula ya nufi gidan su Manal, kafin ya ƙarasa sai da ya tsaya yyi tsaraba sannan ya wuce. Da yaje ƙofar gidan babu kowa, babu wanda zai aika balle ya yi masa iso zuwa cikin gidan hakan ya saka shi kiran wayar Manal amma n
Bata ɗauka ba.
Numfashi ya sauke yana tsaye sai ga Mubeena ta fito daga gidan su Surayya da kwano a hannun ta ganin sa sai tace, "A'a Dr ya ka tsaya a nan kamar wani baƙo? Ka shiga ciki mana, muje ciki" ta faɗa tana yin gaba bai shiga ba sak da ya tabbatar ta sanar dasu sannan ya shiga cikin gidan da sallama.
Tsakar gidan da haske sosai suna zaune a tsakar gidan gabaɗaya akan tabarma, shigar sa ya saka Baba ya kalle shi da fara'a yace, "banda abin Adnan sai ka tsaya a waje kamar wani baƙo?." Murmushi yayi ya ƙarasa suka gaisa da Baba ya zauna daga gefe suka gaisa da Mama ta amsa fuska sake kamar yadda ta saba.
Mubeena ta kalli Mama tace, "Gashi Mama na samo mata." Mama tace, "kai mata mana, ki kira ta ma tazo nan." Mubeena ta shiga da kwanon ciki. Mama ta kalli Baba tace, "ai ni nace yazo da daddare ina neman sa." Baba yayi dariya yace, "Allah sarki, Gashi kuwa ya amsa kira." Mama tayi murmushi tace, "ai ba wani abun bane akan maganar Manal ce dai."
Gaban sa ya faɗi matuƙa ya kulle ido yana jira yaji abinda zata ce masa sai addu'a yake a zuciyar sa. A lokacin Manal ta fito da hiijabi ta ƙaraso ta zauna Mubeena ma ta zauna Mama tace, "Adnan ka ɗauko matar ka Manal ku koma gida, komai ya wuce in sha Allah." Tana kallon yadda ya sauke ajiyar zuciya da yadda bakin sa ya furta alhamdulillah tare da yin murmushi mai sanyi.