← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 84

Sashe 84

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

“In ma da gaske ka ke ai gaka gasu nan.”
“Wasa nake yi, ni da nake da kamar ki ai so zan yi suje wajan Mummy ko wajan Mama su yi hutu su bar mu mu sake.” Murmushi tayi ya zo inda take ya dungure mata kai ya ce, “ni na san fushin naki bashi da dalili.” Tayi dariya ya kalle ta ya ce, “Ayda shekarar ta uku Manali, yaushe za a haifar min Jidda?.” Ta rausayar da kai kafin tayi magana ya ce, “har yanzu tsoron haihuwar ne? To kawai kema ki ce min a other room ki ka fo zaƙewa, a labour room kema raguwa ce.” Tunawa da abinda ya wuce sai suks yi dariya gabaɗayan su ta taso daga inda take ta shiga jikin sa ya rungume ta tace, “Allah ina tsoron haihuwa har yanzu.”

Yayi dariya ya ce, “haka zaki daure a samo min mai sunan Mummy na Jidda kenan. In ba haka ba kema na fara yi miki gorin babu abinda ki ka iya sai harkar other room.” Tayi dariya tace, “Kamar wata kai?.”
“Au haka ne? To mu gani a ƙasa.” Tayi dariya ya sake riƙe ta yana jin farin ciki a zuciyar sa.
“Ni fa ko na haifi mace Ayra zai saka mata, sunayen ƴaƴana daga A zasu dinga farawa.”
“Don iyayi?.”
“Haka nake so.” Ya taɓe baki ya ce, “to ni dai in dai na saka sunan Mummy Jidda zan ce.”

Manal tace, “babu ruwan ka kuma da wannan, ai ni zan haife ta ko?” Ta faɗa tana kallon idon sa. Shima kallon ta yake ya ce, “ke zaki haife ta, amma waye zai baki cikin?.” Manal tace, “Allah. Ko lokacin cikin Ayda da ka dinga yi min wayo Allah ne fa ya bani ba kai ba.” Yayi dariya mai sauti ya ce, “na san Allah ne ya baki, amma waye sila?.”

Manal ta kawar da kai gefe tana dariya ya juyo da fuskar ta ya ce, “faɗi mana, a ruwa ki ka sha ko a ƙafa ki ka tako?.” Manal ta tayi dariya tace, “oho dai.”

“Ammi zan sha corn flakes.” Muryar Ayan da suka ji sai ya sake ta ya shigo ɗakin ta kalle shi tace, “Ayan baka jima da cin abinci ba fa, daga yin bacci a farka sai a sha corn flakes?.”
“Ni dai Ammi ina so” ya kalli Adnan yace, “Abie ka cewa Ammi ta bani corn flakes.” Yayi murmushi ya riƙe hannun sa ya ce, “zo mu je mu sha tare.” Suka fita ita kuma ta shiga wajan Ayda ta tarar itama ta farka ta riƙo ta suka fito falon.

Tare suke sha dashi ita dai kallon su take yi tana yi musu video cikin ƙaunar su gabaɗaya. Aka yi kiran sallah suka tafi masallaci da Ayan itama tayi sallah. A ɗakin sa ya same ta tana gyarawa ya rungume ta ta baya yana bin wuyan ta da kiss mai kashe jiki tana lumshe idanun ta kafin ya ce, “In na kalle ki keda Ayan da Ayda ina jin matuƙar farin ciki Manal.”

Ta juyo tana kallon sa bayan ta riƙe hannun sa tace, “da kuna shan corn flakes video nake yi muku saboda ina ƙaunar ku gabaɗaya Partner.” Tayi masa kiss a kumatu ta kwanta a ƙirjin sa tace, “ina ji a raina kamar babu wacce ta kai ni yin sa a a gidan auren ta.”

Bayan ta yake shafawa a hankali ya ce, “Tarbiyar da ki ke bawa Ayan itace ta saka nake ji a raina da na rasa ki da nayi babbar asara a rayuwata. Ina son ki Manalin Mama.” Tayi murmushi tace, “Nima ina son ka Bebin Mummy. I so much love you.” Yayi dariya zai yi magana suka ji Ayan ya ce, “i love you Ammi, i love you Abie.” A tare suka kalle Bebi yayi murmushi yayi masa alamun ya taho ya ƙaraso a guje Ayda tana bayan sa ya haɗa su ya rungume a jikin sa yana hamdala ga Allah maɗaukakin sarki.

Alhamdu lillah!
Staring writing on August 2024
Completed on December 2024
Released on 1th January 2025
Finished on February 2025.

_Abinda na rubuta daidai Allah ya bamu ladan, wanda na yi kuskure Allah ya yafe mana Amin. Allah ya sa mu cigaba watan ramadan lafiya mu ga ƙarshen sa lafia, Allah ya karɓi ibadar mu ya bamu lafiya bauta masa a wata mai girma Amin._

_Ni ce taku Nana Haleema, na gode masoyana Allah ya sake haɗa mu a sabon littafina wanda zai zo a ƙarshen shekarar 2025 in muna da rai da lafiya. In kuma an samu labarin mun amsa kira mahaliccin mu a taya mu addu’a Allah yasa zaman kabari ya fi mana zaman duniya daɗi Amin._

Nana Haleema❤️
0701 809 8175
09030398006.
Chapter 84 · 0% Book details