← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 84

Sashe 46

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam yace, "kar ki ce haka, ai babu wanda ya wuce kuskure a rayuwa. Na san sun yi kuskure babba mai girman da manta shi a rayuwar ki za'a jima. Kin san da cewa sun jima suna cewa na taya su da addu'a akan Allah ya bayyana musu ke ko ahlin ki? Basu da tabbacin kina raye amma kullum cikin neman ki suke, Meyasa yanzu sun gan ki baza ki yi haƙuri a ƙarasa rayuwar da ta rage ba, ko Malam?"Malam ya faɗa yana kallon Baba.

Baba yace, "Gaskiya ne, shekaru sun ja mutuwa kowa yake jira." Malam yace, "Allah maɗaukakin sarki yana magana akan masu haƙuri da yafiya yace, "Kuma idan kuna so rama abinda aka muku, to ku rama daidai da abinda aka muku. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shi ne mafi alheri ga masu haƙuri. Wannan ayar tana cikin suratul nahli aya ta 126. Akwai hadisin Annabi Muhammad S.A.W da yake cewa, "Allah yana umartar ku da ku gafartawa wanda ya zalunce ku, kuma ku gafartawa wanda ya hana ku, kuma ku ƙulla soyayya da wanda ya rabu da ku."

Ganin maganar tasa tana shigar Mama sosai sai Malam ya sake cewa, "Afuwa tana daga cikin dabi'un Annabin mu Muhammad (SAW), shi ne shugaban dukkan masu yin afuwa, shi ne mafi tausayin masu tausayi (SAW). Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya faɗawa Ukubatu bin Amir (RA) lokacin da ya tambaye shi kan ayyuka mafiya falala sai ya ce: "Ya Ukbatu! Ka sadar da zumunta ga wanda ya yanke maka, ka ba wanda ya hana ka, kuma ka yi afuwa ga wanda ya zalunce ka."

"Afuwa tana jawo babbar lada a wurin Allah, Allah maɗaukaki yace; Wanda ya yi afuwa kuma ya gyara, to ladar sa yana wurin Allah. A wannan aya Allah bai faɗi yawan ladar ba, kuma kowa ya san Allah Mai kyauta ne ba da lissafi ba idan ya ga dama. Don haka tunda ya ce ladar mai afuwa tana wurin sa ai a tunanin mai tunani ma ya kamata ya san ba ƙaramin tagomashi Allah zai masu sakayya dashi ba."

Malam ya kuma cewa, "a hadisin da na faɗa miki a farko kin ji inda annabi Muhammad S.A.W yake cewa; ka ƙulla zumunci da wanda ya yanke shi, hadisin sai ya tafi kamar dake ake, wani abun in ya faru aai kaji kamar da kan hadisin ya sauka ko ayar. Zahra ki kasance mai yafiya a ko yaushe, ba ina tilasta ki akan ki yafe bane ina faɗa miki falalar da take cikin yafiya, ina faɗa miki falalar da Allah ya tanadawar mai haƙuri da kuma yafiya. Allah da kansa yace; kazam mai haƙuri da yafiya ladan mai yi yana gare shi, ni dake da kowa ya san wannan lada ba ƙaramin lada bane ba."

Mama take yi sosai imani na shiga zuciyar ta Malam yace, "bayyanar ƴan uwan ki ki ɗauka kamar alkhairi ne ya bayyana a gare ki da kuma yaran ki, ki karɓi ƴan uwar ki hannu biyu kar ki zama mai raba zumunci a tsakanin ki da ƴan uwan ki ko yaran ki. Kar laifin da aka yi miki a baya ya saka ki dinga aibata ƴan uwan ki, ko ki dinga ji a zuciyar ki yadda suka nuna basa son ki kema bakya son su. In kin yi hakan ba laifi bane saboda ɓata miki akayi, amma haƙuri da yafiya da cigaba da zumuncin yafi riba yanzu ko nan gaba."

Mama da take kuka tace, "haka ne Malam, na amince da duk abinda kace, kuma dukkan su na yafe musu." Malam yace, "har zuciyar ki kika yafe ko kuma maganar da nayi miki ce ta saka kika yafe musu?, Kar ki yafe a baki a zuciya kuma baki yafe ba."
"Wallahi har zuciyata Malam, nayi haƙuri na yafe wallahi har cikin zuciyata. Ina so na shiga cikin wanda Allah zai yiwa tagomashi na musamman a ranar lahira." Malam yayi murmushi yace, "haka ake so, naji daɗin hakan da kika karɓi gyaran ki lokaci daya, haka ake son zuciyar musulmi ta kasance, ana so musulmi ya kasance mai saurin ɗaukar shawara ko gyara a duk sanda hakan ya riske shi. Naji da kika amince na tabbatar ladan ki yana wajan Allah."

Ya kalli Manal da Mubeena da suke kuka yace, "kuma duk kun ji abinda nace, ku yafewa wanda ya cutar daku, duk da rama cuta ga macuci ba laifi bane amma haƙuri shine riba. Kar ku riƙe su a zuciyar ku domin su iyaye ne a wajan ku gaba da baya." Mubeena tace, "in sha Allah malam, Allah ya sakq da alkhairi ya ƙara girma." Malam ya amsa da amin ya sake musu nasiha mai shiga jiki sosai kafin a koma raha yana tsokanar su akayi dariya Malam yayi sallama ya tafi.

BDƘB3P28

Mama ajiyar zuciya tayi bayan Malam ya fita ta kulle idanun ta ta buɗe ta kalli Manal da take zaune tana kuka haka Mubeena ma. Kafin tayi magana Baba ya dawo daga raka Malam ya zauna ya kalle ta fuskar ta duk tayi ja saboda kuka, haka fuskokin yaran ta suma sun yi ja saboda tsabar kuka.
Baba yace, “Kar ku ɗauki nasihar Malam kamar tursasawa, Ku yi abinda zuciyar ku take so ba abinda aka yi muku dole ba.”

Mama tace, “Baban Manal ai ya riga ya wuce kuma, dukkan su na yafe musu daga kan mahaifin su Manal ɗin har ƴan uwana. Zan kuma cigaba da zumunci dasu tunda bani da wanda ya fisu a duniya. Sai dai zan dinga addu’a Allah ya kawar min da shaiɗan daga zuciyata dan in ina tuna irin abubuwa da suka faru na kan kasa mantawa.”

Baba jin haka sai yaji daɗi sosai har ya nuna akan fuskar sa yace “Alhamdulillah! Haka ake son ko wanne musulmi Zahra, ya kasance mai afuwa da yafiya ga wanda ya cutar dashi. Naji daɗi da kika ce komai ya wuce, nayi farin sosai Allah ya yafe mana baki ɗaya.” Ta amsa da amin ta kalli Manal da Mubeena tace, “na janye kalamai na a kan mahaifin ku, ku karɓe shi hannu biyu, kamar yadda Malam yace baku da kamar sa tunda shine ya haife ku.”

Manal ta goge idon ta tace, “Haka ne Mama, komai ya wuce ko Yaya Mubeena?.” Mubeena ta ɗaga kai tace, “komai ya wuce mu ma Mama, tunda kin yafe musu mu ma haka, daman laifi ke aka yiwa ba mu ba, mun tsinci abun a sama ne kawai.” Mama ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Baba tace, “Amma fa duk wani abu da ya kasnace mallakina ne Ali sai ya dawo min dasu, ina nufin dukiyata da take wajan sa, ya tattaro ya dawo da ita na barwa yarana.”

Baba yace, “baki yafe ɗin ba kenan?.”
“Na yafe masa duk abinda yayi min, kawai dai kuɗim ne sai ya dawo dasu ko yanzu ko nan gaba.”

Baba yayi murmushi yace, “to ki yi me da kuɗin?.” Mama ta kalle shi tace, “ko zuba musu fetir zan yi na ƙona kuɗina ne ko?.” Baba yace, “naki ne, amma kar ki manta kina da wani kuɗin, kina da kadarar da yanzu in aka siyar da ita Manal da Mubeena in suka juya kuɗin in Allah ya saka musu albarka babu abinda baza su yi ba. Wannan gidan da muke ciki naki ne na kan ki, to me kike nema kuma?.”

Mama ta girgiza kai tace, “kuɗin wajan sa nake nema.” Baba ya girgiza kai kawai yace, “Shikenan.” Ta kalle shi zata yi magana yace, “zan kira su anjima dan dukkan su hankalin su yana ga abinda zaki ce, Ashe Yayan ki ma yana da abinda zai yi a Abuja amma ya bari saboda ke, kaf ƴan uwan ki na Jalingo da wanda suke aure a wani wajan duk suna Kano saboda ke.”

Mama ta kawar da kai bata ce komai ba tana kallon Manal da take zaune sai tace, “Manal har yanzu jego ki ke fa, ki tashi daga tsakar gidan nan ki koma cikin falo nan da sanyi.” Manal ta sake jingina da bango tace, “nan yafi daɗi Mama.”
Surayya ce ta shigo da Ayan yana kuka Mama ta kalli Surayya tana murmushi tace, “uwar goyo ya tashi kenan?.” Surayya ta bawa Manal shi tace, “Ya tashi Mama, tun ɗazu yake kuka.” Manal da ta karɓe shi sai ta tashi ta shiga ciki bata iya bashi nono a gaban Mama kunyar su take ji.

Tana jiyo hirar su sama-sama daga falon da ta gama shayar dashi yayi shiru ta kwantar dashi itama ta kwanta a kan gadon tana yi masa wasa yana kallon ta tana kallon sa har bacci ya ɗauke ta.

Kiran wayar ta ne ya tashe ta ta tashi zaune ta kalli wayar ganin mai kiran sai ta ɗauka ta saka a kunne tace, “Hello partner.” Daga can ɓangaren yace, “Partner ya naji muryar ki haka? Ba dai kuka ki ke yi ba?.”
“Nayi kuka dai ɗazu, amma yanzu bacci nake ka tashe ni.”
“Ayya sorry ban san kina bacci ba.”
“Ya aiki?.”
“Bana asibiti ma, ina nan wajan Abba bashi da lafiya, ga Daddyn su Huzaifa ma shima jinin sa ya hau sosai.” Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, “Allah ya bada lafiya.” Ya amsa da amin kafin yace, “Ina Ayaan?.” Ta kalli gefen ta taga baya baya wajan tace, “Nayi bacci yana kusa dani, yanzu dai ban ganshi ba na san Yaya Mubeena ce ta ɗauke shi ko Surayya.”

Yayi murmushi yace, “Ina Maman Surayya? Bamu gaisa ba gabaɗaya, ɗazu na kira number ta da kika bani ban same ta ba.” Manal tace, “nima tun safe da muka gaisa ban koma ba, tace mun ai na gama jego ɗakyar in bata gudo gida ba.” Yayi ƴar dariya yace, “nima naga kin gama jego ɗin ai, kin kyau abin ki.” Tayi dariya kaɗan kafin yace, “zan kira ki” ya faɗa yana yanke wayar ta ajjiye wayar ta fito a nan ta lura ma har magriba ta kusa.
Chapter 46 · 0% Book details