← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 84

Sashe 7

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magana yake so yayi amma ya kasa saboda nauyin da zuciyar sa tayi masa sai ido da yake kallon Abba idanun sa a waje, bakin sane yake motsi amma ya kasa magana ganin yanayin da yake ciki ya saka Daddy yace, "kamar ya kenan me ka ke nufi? Nufin ka kaine mahaifin matar Adnan?. Daman mai riƙon ta yace ba shine ya haife ta ba kenan kai ne ka haife ta?."

Abba ya kalli Yayan sa ya sauke numfashi cikin nauyin zuciya yace, "duk yadda zan muku bayani babu lallai ku gane, kaina ciwo yake sosai, damuwa tayi min yawa a abar maganar nan kawai zai fi." Uncle yace, "Ta ya ya za'a barta, in aka barta shi Adnan ɗin wanne hali ake so ya shiga? Ka duba yadda ya ƙame ƙam yana kallon ka kana ganin sa ka san yana cikin tashin hankali matuƙa, na tabbatar yanzu tashin hankalin da yake ciki ya ninka damuwar da kace kana ciki, da gaske kaine mahaifin matar sa?."

Abba ya dafe kai yana kallon Adnan da shima shi yake kallo ya kulle ido ya buɗe ya koma ya jingina da kujera bai ce komai ba. Daddy yace, "kayi magana, wannan shirun naka ba shine mafita ba fa, ka tuna akan matar Adnan ake magana, ta ya zaka ce kaine mahaifin matar sa kuma kace a bar maganar?." Abba yayi shiru sai kansa da ya dafe yadda kansa yake ciwo baya jin zai iya cewa komai.

Daddy ya kalli Adnan cikin rarrashi da tausar da murya yace, "Adnan nutsu don Allah, dawo hankalin ka." Kallon Daddy yayi cikin rauni yace, "hankali na bazai taɓa dawowa jikina ba Daddy, indai ba gaskiyar maganar nan naji ba bazan taɓa dawo daidai ba." Uncle da yake kusa dashi ya dafa kafaɗar shi yace, "zaka iya, ka nutsu babu wanda ya wuce ƙaddara a rayuwar sa, in ma ƙanwar taka ce...." Da sauri ya katse Uncle yace, "don Allah Uncle kar kace haka, bazan iya jure wannan kalaman naka ba. Ta ya ya za'a ce matata  wacce na rayu da ita tsahon kwanaki ƙanwata ce? Meyasa tun da baku gano hakan ba? meyasa tun lokacin da nake neman aure ta ba a ce ni da ita yaya da ƙanwa bane sai yanzu?. Ya ku ke so nayi?!"Ya ƙarasa faɗar maganar a sanyaye yana kallon Uncle.

Kallon Abban Uncle yayi ya kalli Bebi yace, "in sha Allah ba haka bane, ka kwantar da hankalin ka, yanzu mahaifin naka ba lafiya ce dashi ba." Kallon Abban yayi ya kulle ido tsoro ya gama mamaye masa zuciyar sa, babban tashin hankalin sa kar maganar nan ta tabbata, in ta tabbata zai iya rasa ransa ? Ta ya ya zai cigaba da rayuwa da Manal a matsayin ƙanwar sa bayan ya fara rayuwa da ita matsayin matar sa?."

Daddy yace, "ka nutsu Adnan, ka nutsu don Allah. Wannan damuwar illa zata yi maka, amma in ka nutsu ka dawo nutsuwar ka komai zai zo da sauƙi. Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya amma jikin sa har rawa take yi saboda tashin hankali.

Tashi yayi a sanyaye ya fita ya daga falon dan zama a ciki zai iya saka shi hauka na wucin gadi, mota ya shiga ya fita daga gidan a guje.

Sai da yayi nisa ya tsaya a kan hanya ya kifa kansa a kan sitiyarin motar cikin tashin hankali da tsoro mai yawa. Zuciyar sa bugawa take yi sosai ji yake kamar yayi hauka, tunanin sa yana ga abinda Abba ya faɗa masa, da gaske dai matar Manal ƙanwar sa ce ta jini ko wasa ake masa?, in hakan ya tabbata ya zai yi? In hakan ya tabbata me zai faru wanne hali zai shiga? In hakan ya faru ya zai yi da ransa?. Allah ya sani yana matuƙar qaunar Manal, yana kallon ta matsayin abokiyar rayuwar sa kuma bugun zuciyar sa, kallon matar sa ma'ajin sirrin sa yake mata, kallon Manal yake matsayin uwar yaron sa da yake cikin ta. Ta ya rana tsaka ake so a juya ta ta koma ƙanwar sa wacce suke uba ɗaya?, in hakan ya faru da wanne ido zai iya kallon ta matsayin ƙanwar sa da suke jini ɗaya? Ya matsayin ɗansa da yake cikin ta? Ɗan sa ne ko ɗan ƙanwar sa?.

"In sha Allah hakan bazai faru ba, bazai tabbata ba in sha Allah!" Ya faɗa a bayyane yana sauke numfashin wahala, a wahale maganar take fita saboda nauyin da zuciyar sa tayi masa.

Waya ya ɗauko a aljihun sa ya kira  number Manal a karo na babu adadi, ɗauka akayi kafin yayi magana Mubeena tace, "ba ita bace Mubeena ce, ta sha magani amma taƙi cin abincin gabaɗaya, ko tea taƙi sha komai aka bata sai tace wai bata so."

"Ya salam! Tana ina?" Ya tambaya cikin raunin zuciya. Mubeena tace, "gata" ta faɗa tana bawa Manal wayar. Jin shiru sai numfashin ta kaɗan-kaɗan ya saka yace, "Partner meyasa baza ki ci abinci ba? Haka kike so ki zauna babu abinci?, ta ya zaki samu lafiya in bakya cin abinci?."

Manal bata yi magana ba yana jin saukar numfashi ta yace, "please ki sha ko da tea ne, Amma kar ki ce sai kin saka sugar kin ga har yanzu sugar ki bai yi daidai ba. Bana so ace kin kwana baki ci abinci ba, ki daure ki ci." Sai a lokacin tace, "bazan iya ci ba." Jin yadda tayi maganar da rauni ya sake kwantar da murya yace, "zaki iya, ki gwada zaki iya ci in sha Allah." Yana ji ta sauke numfashi amma bata ce komai ba yace, "ko akwai abinda kike so na kawo miki?."

Manal tace, "a'a."
"To ki sha tea ɗin please."
"To" ya amsa a taƙaice yace, "Yauwa ko ke fa, maganin zai saka ki bacci, ki sha bayan kin ci abinci zaki yi bacci." Nan ma ta sake amsawa da to kafin yace, "Partner!." Jin yadda ya kira ta sai tace, "uhum!."
"ki kular min da kan ki, I love you so much" ya faɗa yana kashe wayar ya ajjiye a gefe ya ɗora hannun sa duka biyun a kansa. Bai san adadin lokacin da ya ɗauka a wajan ba, shi kansa ya san ya jima a zaune a wajan kafin yaja motar ya nufi gidan sa kai tsaye.

Huzaifa da Hamza suna zaune a gaban Mama bayan sun gaisa kamar yadda suka saba cikin fara'a, Hamza yace, "Mama mun zo ne damn akan Adnan." Mama ta gyara zama tace, "to wani abun ne ya faru?."

Hamza yace, "Mama gabaɗaya Adnan ya canja daga yadda muka san shi, yanzu ko yaushe cikin damuwa yake ko aiki baya iyawa sai dai ya zauna ya zubawa waje ɗaya ido yana kallo. Hakan baya yi mana daɗi, mun saba ayi wasa ayi dariya dashi. Mun tambaye shi me yake damun sa matsayin mu na manyan abokan sa kuma mun zama kamarƴan uwa, duk mun zama ɗaya bama ɓoyewa junan mu komai, amma sai yace shi babu abinda yake damun sa. Hankalin mu ya kasa kwanciya da abinda ya ce, dan mun san ba gaskiyar kenan ba.  Shiyasa muka zo wajan ki ko zamu ji gaskiyar abinda yake faruwa."

Mama tayi murmushi tace, "ai bazai faɗa ba kun fi kowa sanin halin sa, wani lokacin kana jin damuwar sa wani lokacin bazai faɗa ba. Amma ku ai ba wanda za'a ɓoyewa damuwa bane, ku abokan kuka ne kuma abokan dariya ne. Maganar gaskiya yana cikin damuwa sosai, auren sa da matar sa ne yake ɗan rawa kaɗan, amma muna addu'a in sha Allah abinda ake tunani bazai faru ba." Huzaifa yace, "Subahanallahi! Mama Manal ɗin?."
"Itafa Huzaifa, an kasa gane abinda yake faruwa daga nan ɓangaren da ɓangaren gidan su, mahaifiyar ta tunda taga Abban su Bebi a asibiti da Maryma tana kwance tace Manal tazo su wuce gida. Anyi-anyi ta faɗi alaƙar su taƙi, Babban abinda bama so Allah yasa kar ace da Adnan da ita Yaya da ƙanwa ne. Wannan shine abinda ya dagula masa lissafi, shiyasa ku ke ganin sa cikin damuwa."

A firgice Hamza yace, "in sha Allah Hakan bazai kasance ba. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Lallai dole Adnan ya shiga damuwa sosai, wannan tashin hankali har ina?."

Huzaifa ya kasa magana ma shi saboda tashin hankali da mamaki da kuma tausayin Adnan da ya mamaye masa zuciya, lallai dole ya shiga damuwa mai yawa, yadda yake matuƙar ƙaunar Manal in aka ce ƙanwar sa ce zai iya samun ƙaramin ciwo. Mama tace, "in sha Allah bazai kasance ba, in hakan ya faru a yadda Bebi yake sai wani abun ya same shi, in akace an raba su da Manal Adnan bazai dawo daidai cikin daɗin rai ba sai an haɗa da roƙon Allah,  gabaɗaya ya fita daga hankalin sa dan yana da juriya ne da yanzu ya kwanta ciwo."

Huzaifa yace, "Allah ya amince Mama, ko ni na shiga tashin hankali da jin wannan maganar balle shi da kansa. Ya Allah ka kawo mana mafita da gaggawa." Mama ta amsa da amin kafin tace, "wannan shine silar canjin da kuka gani, yanzu ma naji ya ɗauki mota ya fita ban san inda ya nufa ba kuma."

Hamza yace, "Allah ya kawo mafita a lamarin, Amma Mama dole ya shiga tashin hankali, ai wannan ba ƙaramin abu bane dole ya rasa nutsuwar sa. Allah ya daidaita lamatin." Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba kafin su yi mata sallama su tafi.

  ****Bebi bai jima da zuwa gidan saba aka kira shi Abba babu lafiya dole haka ya dawo gidan. Lokacin da yazo har sun kai shi wani ƙaramin private hospital da yake kusa dasu dan bashi taimakon gaggawa. Koda yaje Yaya isma'il ne kawai a ɗakin an sakawa Abban ruwa.

Fita yayi ya nemi likitan da ya duba Abban a nan yake sanar dashi jinin sane yayi kasa shiyasa yake fama da ciwon kai mai tsanani amma da ruwan da aka saka masa ya ƙare zasu iya tafiya gida. Har ruwan ya ƙare suna nan, a lokacin sha ɗaya na dare suka dawo da Abba shi kuma shida Yayan da suka wuce unguwar su.

                Washe gari.
Chapter 7 · 0% Book details