← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 84

Sashe 22

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya girgiza kai yace, "sunan kakar ku kenan." Manal ta ɗaga kai tayi shiru bata ce komai ba. Abba yace, "madallah na gode, duk sanda kika je gida ki gaishe min da mahaifiyar ki." Manal ta amsa suka tashi suka fita.

Wajan Mama suka koma suka zauna Farida tace, "Manal ya school din?." Manal ta ɗan turo baki gaba tace, "wallahi Yaya gabaɗaaya na tsani makarantar." Farida tace, "Meyasa?."
"Oho min" ta faɗa tana ƴar dariya kaɗan.

A lokacin ya dawo falon Mama ta kalle shi tace, "ga abinci fa, yau abinda ka ke so muka yi funkaso." Ya zauna yace, "Mummy meyasa jini Abba yake hawa ne, daman yana da hawan jini?." Mama tace, "ban sani ba wallahi, amma gabaɗaya ya canja ya koma kamar ba shi ba." Bebi ya sauke numfashi bai ce komai ba yana tunanin damuwar da take damun mahaifin sa har haka, dan shi ya ɗauka damuwar Maman su Manal ta wuce. A lokacin aka kawowa Manal nata abincin ta girgiza kai tace, "na ƙoshi Kausar."

Mama tace, "kin ƙoshi a ina? Karɓi kici rai da sha'awa, banda lalura ma a hana ka shan zaƙi ko a kafa doka akan abinda ka ke son ci?. Bana son baƙuntar nan taki Manal, har yanzu kin kasa sakin jikin ki a cikin mu." Manal tace, "ba haka bane ba Mummy."
"To karɓi ki ci." Mimi tace, "wallahi yayi daɗi kuwa, ya sha sugar." Manal ta karɓi plate ɗin da aka miƙo mata ta kalli Bebi suka haɗa ido sai ta kalli Mama tace, "Allah Mummy ba sai na ci ba."

Mama tace, "ina gani kina kallon sa ai, shiyasa ya ɗaure fuska saboda kar ki ci. Ni nace ki ci indai kina so." Manal ta girgiza kai tace, "A'a Mummy ba haka bane, sugar na yayi high in naci zai sake yin sama, shiyasa ba zan ci ba tunda Mimi tace da sugar." Farida tace, "Allah ka raba mu da lalura, kina son ci lalura ta hana." Manal tayi murmushi ta ajjiye amma ya bata sha'awa son ci kawai take yi.

Yana kallon ta ya san tana son ci sosai amma bazai yu ba dole tayi haƙuri. Manal ta kalli Kausar tace, "Sis don Allah kai shi kitchen in ina gano zan iya ci." Kausar ta ɗauka tace, "sannu, Allah ya yaye miki wannan ciwo." Ta girgiza kawai bata ce komai ba.

Message taji a wayar ta sai ta duba taga shine ya rubuto mata, _Ki yi haƙuri, yanayin ciwon ki ne ya saka hakan amma naga kina so ki ci ko?._ Manal bata kalle shi ba ta mayar masa da, _Ina so, amma na haƙura._ ajjiye wayar yayi bayan yaga abinda tace bai bata amsa ba.
Lubna ce ta shigo da kaskon turaren wuta hayaƙi yana tashi ttace, "Mama wai in ji Mamy kiji ƙhamshin sa."

Ganin Bebi a zaune sak tace, "Lah Mama Yaya Bebi yana nan na tafi" ta faɗa tana ficewa da sauri. Murmushi yayi kawai baice komai ba. Farida ta kalli Manal tace, "wai har yanzu bakya yin turaren wuta a gidan ki?." Manal ta ɗaga kai tana murmushi tace, "Sai dai nayi da safe in ya fita kafin ya dawo ƙhamshin ya ragu sai kaɗan."
"Ji ƙaddara" Farida ata faɗa tana kallon sa. Ta sake kallon Manal tace, "To ki koya masa so ta dole mana, ki dinga kunnawa ko yana nan." Manal ta wara idanu tace, "taɓɗijam! Rufa min asiri Yaya." Mimi tayi dariya tace, "kice halin nasa yana nan." Kallon Mimi yayi sai tayi shiru tana dariya, Bai kula suba ya tashi ya fita ya bar musu falon.

Sai bayan magriba suka tafi suka biya gidan Huzaifa daga nan suka wuce gida. Bai shiga gida ba sai da yayi i'sha ya shiga ya samu har tayi wanka ta idar da sallah. Kallon ta yayi ya ajjiye mata leda ce, "karɓi wannan ki yi blending ki dinga sha" ya faɗa yana nuna mata ledar cucumber da green apple.

Manal ta duba ledar ya sake cewa, "zaki iya haɗewa duka waje ɗaya ki markaɗa, ya zama kamar shine lemon ki ko yaushe ki dinga sha, zai taimaka miki wajan redusing sugar ki."

Manal ta cire hijjabin jikin ta tace, "to bara naje nayi yanzu."
"In kuma kina ganin zaki jurewa ci ko yaushe ba sai kin mayar dashi ruwa ba." Manal tace, "gwara nayi blending ɗin zai min daɗi." Ta miƙe tsaye ya ce, "muje na raka ki."

Tare suka shiga kitchen ya samu waje ya zauna yana kallon ta. Wanke su ta fara yi ya ce, "ki saka gishiri ki wanke." Ta amsa ta saka musu gishiri ta yanka sannan ta saka a juicer ta mayar dashi ruwa. Sai da ta gama samu babban jug ta juye ta buɗe fridge ta saka, sannan ta ɗauki glass cup ta zuba wani a kofin ta sha ta kalle shi tace, "wallahi daɗi sosai."

Yayi murmushi yace, "kuma zai taimake ki sosai, dan cucumber tana saurin saukar da sugar da hawan jini, masu hawan jini da ciwon sugar ana so su dinga yawaita amfani da ita. Ita kaɗai ta isa tayi miki maganin ciwon ki, kuma kinga tana rage ƙiba kuma zata taimaka miki a other room."

Manal ta sake sha tana kallon tace, "meye kuma other room." Ya wara ido yace, "baki san other room ba?."
"In na sani zan tambaya ne?."
"Zan faɗa miki, gama tukunna."

Manal tace, "ko ɗan gyara wajan nan wai baza ka taya ni ba? Gaskiya baka iya soyayya ba." Bebi yayi dariya yace, "naji muje a haka, bazan yi ba. Wai ke ni ɗan aikin ki ne?."
"Ba shi bane, dan ka taya ni aiki ai ba komai bane."
"Ke dai kika sani, bazan yi ba."
"Shiyasa nace baka iya ba ai, inda a india ne tare zamu yi."
"Shima a film ko?." Manal tayi dariya tace, "har a zahiri ma."

A bayan ta taji ya tsaya ta tsakanin hannayen ta ya sako hannun sa ya riƙe abinda take ɗaurayewa ya kalle ta yana yi mata magana a daidai kunnen ta tare da fesa mata numfashin bakin sa ya ce, "kince na taimaka miki ko."

Shiru tayi dan ko yaya ta jita a jikin s a yanzu sak ta canja daga yanayin da take ciki, shi kuma yana sane yake haɗa jikin sa da nata yana riƙe hannun ta da sunan wanke-wanken da take yi zai taimaka mata.
Shirun da yaji tayi ne ya saka shi ya tabbatar akwai wani abu, bai ce komai ba ya ajjiye abinda take yi ya juyo da ita yana kallon ta ya ce, "ya dai?."

Sai kawai ta kwanta a jikin sa idanun ta a kulle tana dhafa bayan sa a hankali. Riƙe ta shima yayi ya ce, "faɗa min me ya canja ki?."
"Ba kaine ba."
"Da nayi me kenan?" Ya faɗa yana karyar da murya. Sake riɗe shi tayi soaai yayi murmushi ya ce, "kin ce ban iya soyayya ba ko? Bara na nuna miki adadin soyayyar da Adnan ya iya a yau, fatana kar ki nuna min kin gaji" ya faɗa yana sunkuya ya ɗauke ta, ko hasken kitchen ɗom bai kashe ba ya shiga ɗaki da ita.

Bayan wasu kwanaki.

Cikin Manal ya bayyana sosai kai da ka ganta ka san ya girma dan a lokacin yana wata na takwas kenan kana ganin ta zaka tabbatar ta kusa haihuwa. Ta raini cikin lafiya da taimakon Bebi dan ba dan shi ba abinda yake cikin ta yana cikin hatsari babba saboda yanayin ciwon da take fama dashi.

A hakan ma duk kwana uku sai ya auna blood sugar ɗin ta dan ba a so ya kasance yayi high kafin haihuwar ta ko kaɗan. Cikin ikon Allah baya sama saboda tana ƙoƙarin kawar da kai daga abinda take so saboda lafiyar ta. A cikin kwanakin babu wata matsala da ta sake taspwa daga gidan su Bebi, matsalar Maryam an maganace ta tuni Kamal bai sake waiwayar ta ba itama ta manta dashi ta cigaba da rayuwar ta.

Manal na zaune a falo ita da Mubeena suna hira Mubeena tace, "ke umrah ai da daɗi zan so mu sake komawa, tunda dai Mama tace kuɗin ta za'a kashe tunda daman dalilin ɓoyewar saboda mu ne, amma yanzu tunda mun san komai za'a sake komawa."

Manal tace, "in dai za'a koma kan dani za'a je, Wancan ai ba a tafiyar Mama naje ba." Mubeena tace, "hutar da Maman akayi mijin ki ya kai ki." Tayi dariya ta kalli Mubeena tace, "Yaya Mubeena har yanzu babu wanda kika tsayar ne?." Mubeena ta kalle ta sak tayi murmushi tace, "Na tsayar mana, Mama bata faɗa miki ba?."

Cikin zumuɗi tace, "bata faɗa min ba, waye shi?." Mubeena tace, "Sunan sa Munir yana aiki a Abuja iyayen sa duka shna can, a sa'anni da tsaho da jiki bazai wuce mijin ki ba amma shi ya taɓa aure matar sa ce ta rasu bayan sati biyu da auren su. Har sun yi magana da Baba ma fa, Baba yace yaje zai neme shi."

Manal da farin ciki ta riƙe Mubeena tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya, Allah yasa shine mijin ki." Mubeena tace, "amin ya rabbi."
"An munafurce ni, da ban tambaya ba za'a faɗa min ba kenan?."
"Na ɗauka kin sani ne ai, ashe Mama bata faɗa miki ba."
"Kai amma naji daɗi wallahi."

Mubeena tayi ƴar dariya tana kallon tv Manal ta tashi tsaye tana cewa, "da alama Abuja zamu je kenan" ta faɗa tana shiga kitchen. Ba jimawa ta fito a lokacin Bebi ya shigo da sallama ba tare da ya kalli cikin falon ba ya hango ta a tsaye tana ajjiye abinci a kan dining yace, "shugabar masu girki ba nace kar ki abinci ba?" Ya faɗa yana ƙarasawa inda take.
Chapter 22 · 0% Book details