← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 84

Sashe 38

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya kashe wayar ne ya kalli Daddy yace, "gwara na nuna musu kai matsayin mahaifin Manal, na basu labarin komai da ya faru ya kamata komai ya zo ƙarshe ko zan huta da abinda yake damuna." Daddy ya kalle shi ya ce, "yanzu kai sirikina ne, ɗan ka yana auren ƴata, ko da yake ban cancanci kiran ta da ƴa taba." Abba yayi murmushin takaici tunawa da abinda ya faru tsakanin sa da Mubeena, zuciyar sa nayi masa ciwo sosai yanayin jikin sa duk ya canja.

Daddy ya ce, "zuciyata bugawa take yi, dana sani da kunya lulluɓe ni suke yi, amma babu yadda zan yi abinda ya faru ya riga ya faru." Abba yace, "tun daga lokacin da na ganta ta ganni ban sake samun lafiya ba, ko yaushe zuciyata cikin zullumi take da tashin hankali."
"Nima na san bazan sake samun lafiya ba, abinda ya faru a baya nuƙurƙusar ƙasusuwan jikina yake yi." Daddy ya sake cewa, "da wanne ido zan kalle ta balle yaran da basu sanni ba?, yanzu da wanne ido zan kalli yaran nan nace musu ni ne mahaifin su?, Mubeena har na barta ba fi shekara ɗaya ba, da wanne ido zan kalle ta nace ni na haife ta?. Meyasa na aikata hakan Mu'azaam? Meyasa na butulcewa amanar da aka bani?."

Abba ya dafe kai idanun sa sun yi ja yace, "wannan duk ihu muje bayan hari, abinda ya faru ya riga da ya faru , yafiyar ya zamu dage mu nema koda zata dinga yankar naman jikin mu, inda hali mu koma Jalingo mu nemo dangin ta mu mayar musu amanar ta da suka bamu."

Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "mun yi kuskure, mun tafka babbar asara, mun bar baya da ƙura, yanzu gashi yanzu mun dawo zamu share ƙurar da muka bari wacce zata bamu wahala matuƙa." Abba yace, "in aka yi sallar i'sha zan nuna musu kai matsayin mahaifin Manal."
"Nima duka su taru na faɗa musu duka binda ya faru, kusuren da muka aikata, butulci da satar da nayi da komai ma." Ajiyar zuciya Abba yayi jikin sa ya sake gumewa da zazzaɓi..
Sai da akayi sallar i'sha sannan Abba ya kira kowa yace yazo har ƴaƴan Daddy da mahaifiyar su da suke wajan su Mama.

Kowa tsoron ya kama masa zuciya na dalilin kiran, Huzaifa da Bebi ne kawai suka sani har su suka shiga aka zauna dan jin abinda za'a gabatar a wajan.

Bayan kowa ya zauna duk suka bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya sannan Abba yace, "na san kowa zuciyar sa tana cikin zullumi da ruɗanin wannan kiran, musamman iyalan gidan Alhaji Ali, zasu dinga mamaki daga zuwa baƙunta an haɗa meeting har dasu. Dalilin kiran na ku dukka ba komai bane illa na sake maimaitawa muku abinda na fa muku kwanaki, na san kun san wacece Manal matarAdnan a wajena, kun san labarin iyayen ta da komai na faɗa muku. Cikin ikon Allah labarin ya gama bayyana kansa, babu zato babu tsammani ƙarshen labarin yazo a lokacin da bamu yi tunanin faruwar hakan ba. A yau ga mahaifin Manal da Mubeena, abokina Ali wanda na baku labari sa, wanda na tsaya masa ya karmi auren Zahra mahaifiyar Manal matar Adnan kenan. Yau gashi a zaune a kusa dani" ya faɗw yana nuna Daddy da yake zaune.

Kowa kallon Daddy yake yi ana kallon Abba da mamaki haɗi da al'ajabi, Yaya Isma'il ya ce, "Abba shine mahaifin Manal kenan?." Abba yace, "ƙwarai shine, shine mahaifin Manal matar Adnan da kuma Yayar ta Mubeena. Kaka a wajan ɗan da aka haifawa Adnan cikin kwanalin da suka gabata."

A lokacin Daddy ya kalli Maman su Huzaifa da kansu ya kalle suna buƙatar ƙarin bayani, yace, "Eh, gidan Adnan da muka je barka matar sa ƴata ce, bayan ita akwai Yayar sunan ta Mubeena." Mama kallon sa take yi cike da mamaki tace, "ban gane ba, ban fahimci maganar sosai ba zaka iya min bayani yadda zan gane?. Yauhe ka aure ta har ta haihi kamar su ban sani ba?."

Daddy yace, "Gaskiyar maganar kenan, abinda kika ji shi ne gaskiya kuma ya faru. Na auri mahaifiyar su Manal a lokacin da nake yawon zuwa gari-gari domin kasuwanci, na tare da ita a garin Zaria kina wani wajan daban tana wani wajan daban, baki san ta bata san ki ba gwara ita ta san akwai ki amma ke baki san akwai ta ba. A haka muka haifi yara biyu da ita kafin na barta mu koma Abuja dake."

Mama kallon sa take yi mamaki ya hanata magana, gani take kamar labari yake bata ko kuma raina mata hankali yake yi. Ganin hakan Daddy ya ce, "zan warware muku duk abinda ya faru yanzu" ya faɗa yana fara basu labarin da Abba ya bawa su Adnan har ƙarshe.

Ya shafe hawayen idanun sa ya ce, "Zahra bata da kowa sani, ni kaɗai ta sani domin ko dangin babar ta bata sani ba, saboda kyaun da take dashi dangin ta suka tsane ta daga ita har mahaifiyar ta. Na karɓi auren ta duk da nasan bata da uwa bata da uba, da taimakon abokina gashi muka karɓi auren ta babu bincike babu komai aka bani ita na dawo da ita Zaria. Allah ya sani a zuciya ba niyar zama da ita na aure ta a farko, amma da naga tarin duniyar da aka haɗo ta da ita sai tuannina ya canja gabaɗaya. Da farko Mu'azzam bai goyi bayana a kan hakan ba, amma daga baya ya bani goyan bayan ɗauke kadarorin da ta gada wajan uwa da uba ɗari bisa ɗari."

"Ta yarda dani, ta bani dukkan kadarar ta wacce ta mallaka masu yawan gaske, dan ko zunzurutun kuɗim da aka bata suna da yawa sosai balle kadarar. Mun fara zama na wasu lokaci, babu yadda Mu'azzaɓ bai yi ba akan na faɗa miki maganar Zahra amma naƙi, ƙarshe da ya dage sai na faɗa miki sai nace ai na sanar sake bayan baki san labarin ta ba, ita dai ta sanki a baki ta kuma san Huzaifa a baki. Saboda barin ta ita kaɗai a gida tana kwana in ya kasance bana gidan ya saka na samu gidan haya mai mutane biyu, tana jin motsin mutane kuma babu abinda zai same ta ba a sani ba."

"Nayi amfani da wayo da dabara wajan kawar miki da hankali dan kar ki gane ina da wata matar musamman ta hanyar yadda nake kwana a gidan, cikin ikon Allah baki gane ba. A lokacin kuma kika haifi Aysha ita kuma ba jimawa ta haifi Nusaiba. Matar da suke gida ɗaya itace ta kula da ita soaai, tayi mata komai cikin ƙauna saboda mace ce wacce take da haƙuri da kirki sosai. Tazarar haihuwar Nusaiba da Fatima shekara ɗaya da rabi ne ta haifi Fatima, ni kuma a lokacin ina kan tattara dukiyar ta ina siyarwa saboda gabaɗaya a Jalingo suke."

Daddy ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru kafin yace, "Sai bayan na gama komai a lokacin Fatima bata fi wata bakwai zuwa goma ba, na rubuta takardar saki na ajjiye mata bayan na faɗa mata ƙudurina a kanta. Saɓanin da muka samu da Mu'azaam akan kuɗin ne, yaƙi karɓar wanda na bashi saboda ya yi masa kaɗan ni kuma sai nace bazan ƙara ba shi kuma yace baya so, daga wannan lokacin muka raba hanya bamu sake haɗuwa ba ko a mafarki sak yanzu, dan daga wannan lokacin Abuja muka koma da zama kafin arzuƙi yayi nisa mu koma ƙasar Qatar da zama."

Daddy ya kalle su gabaɗaya kowa ya nutsu yana sauraren sa  ya ce, "na barta ban san a yanayin da take ciki ba, na kwashe komai nata ban bar ko ɗaya da ya rage ba, na tafi na barta da yara bayan na san ni  ne kawai wanda take dashi a duniya. Na manta da amanar ta na karɓa daga gidan su, na manta da marainiya ce, na manta da rana irin wannan, na manta da cewa haƙƙin ta bazai taba barina naji daɗi ba. Amma daga baya na koma, bayan shekaru biyu na koma don na ganta amma...." Mama mahaifiyar Huzaifa ya dakatar dashi tace, "daga baya ka koma kayi mata ne? Ka koma ka ƙarasa kwashe abinda baka kwashe ba?" Ta faɗa murya na rawa da alama kuka zata yi.

Daddy yayi shiru ya sunkuyar da kai ƙasa Mama ta kalli su Mummy da Mamy ta sake kallon Daddy tace, "amma kaji kunya wallahi, marainiyar yarinya tun a lokacin baya ka wulaƙanya haka, daman akwai irin ku tun duniya na kwance, daman akwai irin ku a zamanin da yafi na yanzu tsafta?." Huzaifa ya kalle ta yace, "Mama don Allah" ya faɗa yana mata alamun tayi shiru.

Shiru falon yayi babu wanda yake magana saboda abinda suka ji wanda ya taɓa musu zuciya, Mamy ce tace, "ku yi haƙuri dukkan ku, amma gaskiya baku cancanci yafiya daga wajan Zahra ko ahlin ta ba, tayi matuƙar ƙoƙarin da ta bar Manal tana auren jinin ku, tayi ƙoƙari da ta iya haɗa zuri'a da ku."

Bebi ya kalli Mamy da alamun don Allah tayi shiru tace, "bazan shiru ba Adnan, su basu ji kunyar abinda suka aikata ba bazan ji kunyar faɗar gaskiya ba. Wallahi in nice ita ƙafar ku na gani a inda nake kotu ce zata raba ni daku."

Mummy da take zaune ta kalle su tayi murmushi takaici tace, "yanzu kana sane da cewa dukiyar da ka tara, da komai da ka mallaka nata ne?" Ta faɗa tana kallon Daddy. Daddy yayi ajiyar zuciyaAjiyar zuciya ya kalli Abba yace, "ko a shekarun da suka wuce a lokacin iya kuɗin da bar mata sun fi naira miliyan biyar, kasancewar lokacin babu banki a buhu aka shirya mata, naira miliyan biyar ɗin da wacce a yanzu ta tafi miliyoyi masu yawa, banda gidaje da filaye da gonakin da aka siyar."
Chapter 38 · 0% Book details