Sashe 78
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manal tace, “bawai na damu bane, mutane ne suka ganin kamar family planing nake yi.” Adnan yace, “ina ruwan ki da mutane? Indai dan mutane zaki yi abu kina haihuwa ma wani cewa zai yi kin haihu da wuri.”
“Ni dai ka san yadda zaka yi dani.” Yayi dariya yana mamakin ta yace, “ya zanyi dake kuwa?, ɗauko ciki zan yi na buɗe bakin ki na zuba a ciki?.”
Manal ta turo baki tace, “ba kai ka san ta ya akayi aka samu wancan da wuri ba?.” Yayi dariya yana girgiza kai yana mamakin autancin Manal yace, “ai kam na sani, zan kuma sake bin wannan hanyar amma ina da sharaɗi.” Manal tace, “ina jin ka.”
Adnan yace, “na farko ba complain; ke kin gaji bayan ki ya riƙe waye waye babu, na biyu babu guduwa ki kulle kan ki, na kuka babu yi min kuka.” Manal ta kalle shi idon ta yayi rau rau kamar zatayi kuka. Ya wara hannayen sa yace, “ba dole a lamarin nan fa, ke kika kawo kan ki.” Manal a sanyaye tace, “to naji na yarda, amma kar ka dinga min mugunta kaji.” Yayi dariya yace, “wannan kuma duk daga baya ne, ba dai ciki kike so ba?.”
Ta ɗaga kai tana kallon sa, yadda ta ɗaga kai ya bashi dariya sosai ya girgiza kai yace, “ki ɗauka an yi an gama. In dai ciki ne cikin kwanakin nan zan samar miki dashi.” Kallon sa tayi tace, “ban yarda da wannan murmushi na ka ba.” Yace, “oho miki dai, taimaka miki zan yi fa.” Manal tace, “to dan zaka taimaka min baza ayi min mugunta ba.” Ta sake kallon sa yana dariya ya kalle ta ya sake yin dariya yace, “Hajiya Manal, kar ki damu kin kusa yin ciki.”
Manal bata ce komai ba sai kallon sa da take yi ganin ya mayar da abin wasa. Bebi yace, “ko zamu fara ɗaukar hanyar daga yanzu ne?.” Ta rausayar da kai tace, “yunwa nake ji.”
“Kin ji matsalar ai, taya zaki samu ciki a haka?, da an yi magana ki kawo uzuri.” Manal ta turo baki tace, “ni fa sai a fasa wallahi.”
“A fasa mana, wa za’a yiwa kishiya saboda bata sake haihuwa ba?.”
Ta kalle shi tace, “Da gaske zaka iya yi min kishiya saboda ban haihu ba?.”
“Eh, yara da yawa nake so kuma ke ɗaya kika haifa.”
“Amma baka kyauta min ba,kuma duk son da kakw cewa kana yi min ba so bane” ta faɗa tana fara yi masa kuka.
Baya so a ɓata masa daddaɗan maraicen da yake ciki mai daɗi da zallar soyayya sai yace, “Wasa fa nake miki, ki daina kuka ke baki san wasa bane?.” Manal tace, “tsoro nake ji kar kace zaka ƙaro wata saboda na haihu sau daya.” Ya kwantar da ita a jikin sa yace, “ni ko baki haihu ba babu wacce zan ƙaro balle ga mai sunan Abbana ina dashi me zai deme ni?.”
“Da gaske ka ke?.”
“Da gaske nake mana Manal.”
“Amma meyasa yanzu ban haihu da wuri ba?.”
“Haka Allah ya rubuta, kuma na faɗa miki ciwon ki yana hana mata irin ku saurin samun ciki, a lokacin farko ma Allah ya taimake ki kika samu da wuri, a wannan lokacin ma Allah ya jinkirta miki. Kuma ni naji daɗin hakan, kinga ga Ayan har ya far zuwa makaranta in kika haihu baki da fargabar raino zai haɗar miki biyu.”
Manal tace, “nima naji daɗi da ya kai wannan shekarun ban kuma haihuwa ba, kaga har makaranta na kusa gamawa hankali kwance. kawai ina jin tsoro kar naje haihuwar ta tafi.”
“Babu inda ta tafi, indai haihuwa sai kin gudu da ƙafar ki. Amma in kina son samun cikin zan kawo miki folic acid ki dinga shan da kullum zai taimaka miki wajan ɗaukar ciki.”
Manal tace, “Haka ma Small mom tace min ɗazu.”
“Shi folic acid ko wacce mace in tana son ɗaukar ciki zata iya shan sa, bashi da side effect.”
Manal ta kalle shi ta sauke tace, “ina son haihuwa amma tsoron haihuwar nake ji, kuma tsoron wannan shan sugar da nayi a lokacin Ayan nake yi.” Adnan yace, “ke dai kika sani, kince kina so kince bakya so kuma yanzu.” Ta kwanta a jikin sa tace, “ina so bana so.” Yayi dariya yana tungure mata kai yafe, “daga baya kenan.”
Wayar sace da take gefe take ƙara ya kalla yaga Huzaifa ne ya kalle ta yace, “Wannan Yayan naki ya takura min, amma bara nayi maganin sa” ya faɗa yana ɗaukar wayar ya saka a speaker.
Huzaifa yace, “wai kana ina ne? Baza ka fito ba yau?.” Adnan yace, “bazan fito ba, ka ishe ni da waya ka takura min, babu damar na zauna a gida da matata sai ka fara yi min waya?. Itama gata a zaune tace ka takura mata ka hanata sakewa da mijin ta, malam kar ka sake kirana kana ɓata min yanayin da nake ciki.” Manal ido a buɗe take kallon sa ya kalle ta ya ɗaga mata gira. Huzaifa yace, “ƙarya ka ke, ƙanwata baza ta taɓa faɗar haka ba wannan sharrin ka ne. Kai ta zama in kaga dama kar ka fito sai ta haihu sau goma.”
Bebi yace, “ka san da hakan ka kira ni?.”
“Kai ta zama kaji, kar ka fito. Kuma wallahi wani abun ya samu ƙanwata maganin ka zan yi.” Adnan yayi dariya kawai ya kashe wayar yana kallon Manal.
Tace, “wai baka jin kunyar da ka ke faɗa masa haka? Yayana ne fa.”
“Yayan naki fa, ai na faɗa miki ni a Huzaifa nake kallon sa ba Yayan Manal ba.” Ta tashi daga kan gadon ta sakko ƙasa ta tsaya a tsaye tace, “Kaji tsoron ranar da zai murza kambun sa na babban Yaya, sai ka zube masa a ƙasa.” Ya Harare ta yace, “wuce nan my love, sau ɗaya ya raina min hankali kuma ya wuce.” Tayi dariya tace, “partner yunwa nake ji ni dai fita zan yi.”
Shima sakkowa yayi yace, “muje tare.” Tare suka fito suka shiga kitchen tayi musu girki yana zaune har ta gama, suka ci abincjn bayan sun gama ta wanke kwanukan a lokacin ya koma daki ta san wanka zai yi yayi alwala saboda lokacin sallah. Itama ɗaki ta shiga tayi tana ta jin haushi ko walha bata yi ba gashi azahar tayi.
BDƘB3P49
Adnan sai da yaje yayi sallah ya dawo ya sake samun ta a kitchen, ya shiga yana kallon ta yace, “my chef me za’a dafa mana ne?.”
“Yanzu zan ɗora lunch.” Ya kalle ta yace, “yanzu fa muka yi breakfast, ki bar girkin ba sai kin yi ba kizo mu koma inda muka fito” ya faɗa yana rƙo hannun ta. Ta turo baki tayi tana turjewa tace, “ko gyara ɗakin ma ban yi ba fa, kuma ni zaman ɗakin isa ta yake yi.”
Ya bin fuskar ta da rikitaccen kallo yace, “ke fa kika ce kina son haihuwa, to in baki zo mun koma ba taya zaki samu cikin?, Ki kashe gas ɗin nan ki zo mu je, in a falo ki ke so sai mu zauna a falon” ya faɗa yana kashe gas ɗin yana kallon ta.
Manal ta kalle shi ta fara buga ƙafa tace, “yanzu fa rana ce zamu iya yin baƙi.” Da ƙarfi ya jawo ta jikin sa yana binta da shegen kallo yace, “na cewa Sayyadi ya cewa duk wanda yazo bama nan, na faɗa miki till down zamu yi.” Zata yi magana ya ɗora hannun sa kan bakin ta yace, “Bana son complain” ya faɗa yana jan hannun ta suka koma ɗakin.
Duk yadda Manal taso a ranar ya hana ta motsi, till down ɗin da yace kusan hakan ne ya faru har dare suna maƙale da juna, sallah ma su biyu suke yi da an idar zai sake jawo ta jikin sa duk tayi laushi amma babu bakin magana tunda yace ai ita tace tana so.
Washe gari Manal ta siyo kwalin pt stick ta ajjiye tana gwada fitsarin ta ko za’a samu ciki. Ranar da ya gani ya dinga dariya yana cewa, “kice tafi da gidan ki kike yi, wannan shine sauke tukunya juye ɗin, da an fito daga wanka sai ki shiga ɗaki sai ki hau duba mudubin ki ko?.” Taƙi kula shi ya dinga tsokanar ta mai son yin ciki dole tayi masa biyayya.
A cikin satin Ayan ya gudo wajan ta tashi sasafen da ta tsana ya dawo saboda shirya shi makaranta, haka take tashi tayi masa abinci ta yi masa wanka ta shirya shi school bus tazo ta miƙa shi ya shiga sannan ta dawo.
Ranar alhamis bayan Ayan ya tafi makaranta Adnan yana gida ranar yace bazai fita ba aiki zai yi, Manal ta fito daga ɗaki a guje ta faɗa kansa tana murna. Ya kalle ta yace, “ke lafiya dai ko?.” Manal ta nuna masa PT stick ɗin ya kalla yaga jajayen zane guda biyu alamun tana da ciki.
Tashi tayi daga jikin sa ta fara tsalla ya riƙo hannun ta yace, “ki daina tsalle mana ko kina so a rasa shi?.” Komawa tayi ta rungume shi tana murna. Yayi dariya yace, “sai a bani kyauta, na samar miki da abinda kike so cikin kwanaki kaɗan, kinga adadin capacity ɗin da nake dashi nasan kin tabbatar ɗin jarumin gaske ne. A bani kyauta ko nan gaba na rama.”
Manal tayi dariya tace, “to me ka ke so?.” Ya kalle ta yace, “a sake bani damar till down. Kin san wancan lokacin na ji daɗin harkar sosai. Ta yi masa Hararar wasa tace, “da cikin?.”
“Ai na san yadda zan yi.”
“Ni dai a’a ka zaɓi wani abun.”
“Lallai ɗan Adam butulu ne, ni za’a yiwa haka Manal? Shikenan zan rama.”