Sashe 71
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi dariya mai sauti tace, “Ka ɓata zuciyar ta dai.” Yayi dariya shima mai sauti tace, “wai yaushe ka fara sona?, ni dai naga ba wata maganar kirki muka yi da kai ba a wancan lokacin, tsoron ka ma nake ji saboda tsawa da haɗe rai. Kallon mara kirki nake yi maka ashe fuskar kace a haka amma kai ba haka ka ke ba. Yaushe ka fara sona?.” Ya kalle ta yana murmushi ya ce, “nima bazan ce ba ga ranar da na fara jin ki a zuciyata ba wallahi, kawai na wayi gari naji in ba ke ba sai rijiya.” Tare suka yi dariya yana kallon ta yace, “Manal ɗina, I so much love you” ya faɗa yana ɗaukar wayar sa. Tayi murmushi tace, “nima ina sonka.”
“Yanzu muje ki bani abinci, yunwa nake ji.” Ta amsa da to suka fito falo suka ƙarasa inda Lubna take.
A falon suka zauna suna ci abinci har Lubna suka gama Lubna ta ɗauke plates ɗin da aka ci ta kai kitchen ta ajjiye ta dawo ta zauna ya kalle ta yace, “kar ki ji komai Lubna, ki saki jikin ki nan ma gidan ku ne, sannan babu wanda zai miki abinda bakya so indai ina nan.”
Tayi murmushi tace, “ni na san na samu kariya tunda Allah ya bani Yaya kamar ka. Allah ya cigaba da kare ka Yaya Adnan, Allah ya baka abinda ka ke so ya saka maka da gidan Aljanna. Yadda ka ke kula damu gabaɗaya Allah ya baka mai kula da naka yaran, Allah ya jiƙan Abban mu ya gafarta masa, Allah ya bar ka da matar ka da ka ke so, Allah yasa baza ka yi mata kishiya ba.” Manal tayi caraf tace, “Amin Lubna, wannan addu’a ce mai kyau.”
Fuska a sake yake kallon Lubna bayan ya amsa da amin yace, “cin hanci ta baki?.” Lubna tayi dariya tace, “A’a, kawai bana so ka yi mata kishiyar ne Yaya.” Yayi murmushi ya kalli Manal yace, “Abbana ma matan sa biyu, nima biyu zan yi.” Manal tace, “kayi huɗu ma.”
“Ƙarya kike wallahi, na tabbatar yanzu gaban ki ya faɗi.”
“Harda wallahi, to meye abin kishin?.”
“Oho miki” ya faɗa yana kallon ta,
Lubna tayi dariya tana kallon su cikin burgewa, ya tabbatar Manal ta gama dacen miji ba dan ya kasance Yayan ta ba. Ta tabbatar Yaya Adnan mijin na gari ne lamba ɗaya.
Sun jima a zaune suna hira kafin Lubna ta tashi ta shiga ɗakin Manal, itama Manal ɗin tashi tayi ta shiga ɗakin da Ayan a hannun ta. Kwantar dashi tayi ta canja kaya zuwa na bacci Lubna ta fito daga banɗaki Manal tace, “na baki kayan bacci?.” Lubna tace, “Yauwa bani.” Manal ta ɗauko mata ta bata Lubna ta karɓa ta ajjiye a kusa da ita.
Manal nauyin Lubna take ji baza ta iya fita ta tafi wajan Adnan ba hakan ya saka ta zauna tana gyarawa Ayan kwanciya. Lubna tace, “Sis ki bar min shi ya kwana a wajena.” Manal ta kalle ta tace, “zaki sha kuka kuwa, Wallahi hana ki bacci zai yi.” Lubna tace, “bar min shi na ɗana kafin nawa nima su zo.” Manal tayi dariya ta miƙe tace, “to bara naje na dawo” ta faɗa tana fita ita kuma ta tashi ta canja kaya ta ɗauki Ayan da yake bacci ta kwantar dashi a kan gadon ta kwanta a gafe tana kallon sa.
Manal tana shiga ɗakin Adnan ya kalle ta yace, “ina Ayan ɗin?.” Ta ƙarasa inda yake zaune ta zauna ta kwanto a jikin sa tana kallon sa tace, “Lubna tace na bar mata shi.”
“In yayi kuka me zata iya yi masa? Ke kuma sai kika bar nata shi ɗin?.”
“Haba Partner, ka bar mata shi in ya tashi yana kuka zata neme ni.”
Ya Harare ta yace, “kawai saboda ɗaukar haƙƙin sa yana kuka har sai an fito daga can nazo nan ana buga min ƙofa?, Ai kawai ki tashi ki karɓo shi.” Ta kalle shi tace, “Don Allah ka bar mata shi tunda itace ta nema, in naje karɓe shi baza ta ji daɗi ba.” Shiru yayi baice hakan ya saka ta kalle shi tace, “Wai wannan glasses ɗin naka na gayu ne ko kuwa na ƙara ƙarfin gani ne?.”
Ya zare shi daga idon sa yace, “idona ras yake har na fiki gani, ina sakawa ne saboda hasken computer da hasken takarda.” Manal tace, “ai ku likitoci dole ma idon ku ya mutu saboda kallon tsaraicin mutane.” Yayi ƴar dariya yace, “waye yace miki kallon tsaraici mu ke?.”
“Shi ku ke yi mana, abinda har haihuwa kuna karɓa.”
Ya kalle ta yace, “ni da nake cardiologist me ya haɗa ni da haihuwa?, Sai nayi wata ɗaya ban bi hanyar maternity ba indai ba Hamza nake nema ba ko wata likitan. Ni ai ɓangarena bai wani shafi kallon tsaraici ba gaskiya.”
“Amma in zaku yi theater ko zaku yi gwajin zuciya ai sai mace ta cire riga ko?.” Ya kalle ta yana murmushi bai ce komai ba tace, “eh nan ma ai tsaraicin ne, balle kai da ka ke aikin zuciyar har taɓa ƙirjin matan kana yi.”
Ganin yanayin ta ya canja sai ya sake yin murmushi yace, “eh haka ne, amma wallahi in dai ba na san mutum ba da zarar ya bar asibitin na manta dashi balle har surar wata mace ta tsaya min a rai, mutanen suna da yawa sosai, in ba sanin mutum nayi tun farko ba bana gane shi in ya bar asibiti sai dai shi ya gane ni.”
Manal tace, “amma dai kana ganin ƙirjin matan ko?.”
“Duk cikin aiki ne Manal.” Turo baki tayi tana kallon gefe tace, “wallahi zafin hakan nake ji.” Ɗan murmushi yayi yace, “ai ba wani abun bane, ni da ba gynecologist ba, sune suka san mata ciki da waje, yadda gyne ya san jikin mace ku matan baku sani ba.”
“Naji daɗi da ba kai ba ɗin bane, Allah da ka kasnace gynecologist bana tunanin zan iya bacci in ka fita, dan kawai gani zanyi mata kawai ka ke kallo.”
Yayi murmushi ya ja hancin ta amma bai ce mata komai ba. Ido ta lumshe tace, “Bacci nake ji.”
“Bacci fa kika ce? Kuma a ɗakin nan?.” Ta kalle shi tace, “eh mana.”
“Lallai ma, kema kin san ba a shigowa ɗakin nan ayi bacci ko?.” Ta kalle shi tace, “kamar wani labour room?.” Yayi dariya mai sauti yace, “da alama ɗakin nan da kika shiga ya gigita ki, da anyi magana kice labour room” ya faɗa yana dariya sosai yana kallon ta.
Shan kunu tayi yana dariya ya riƙe kumatun ta duka biyun yana ja yace, “Bani labarin labour room ɗin, ya yake shi da gaske ba a bacci a ciki?.” Murguɗa masa baki tayi ya sake yin dariya ya jawo ta ta ya kwantar da kanta a ƙirjin sa, ya yi mata kiss a goshi yana shafa bayan yace, “my dear wife, mother of my child. Ke ta musamman ce a rayuwar Adnan.” Ta kwanta a jikin sa tana dariya tace, “nima kai na musamman ne a rayuwar Manal.”
Bai bata amsa ba sai murmushi da yake yi tace, “Don Allah ka dinga murmushi kamar haka kafi kyau wallahi. Kai kullum fuska a ɗaure?.” Ya kalle ta yace, “to ya zan yi da halittar da Allah yayi min?.” Tayi murmushi tace, “wallahi in ka ɓata rai tsoro ka ke bani.” Murmushi ya sake yi bai ce komai ba tace, “bacci nake ji fa.”
“Baki isa ba ai, babu ke babu bacci.”
“To kaima ai baccin ka ke yi.”
“Da bani da lafiya ba, yanzu na samu lafiya kuma kinga nayi missing ɗin ki.” Manal tace, “tsoron ka nake ji, in aka kwana biyun nan ba a yi komai ba in ka waiwayo wahala ka ke bani” ta faɗa tana kallon sa a shagwaɓe.
Ya sake yin dariya yace, “kema cewa kika yi in ba a yi komai ba, to ai kwanakin da ba a ayi ɗin ba nake fanshewa.”
“Nidai a’a, kamar ma period zan yi.”
“Kafin ki yi ɗin yanzu lokaci na ne ƴan mata.”
“Don Allah kar ka yi min mugunta” ta faɗa tana kallon sa a lokacin da ya kashe hasken ɗakin ya tunkaro ta.
“Shiiii! Ki yi shiru” ya faɗa yana zama kusa da ita tare da ɗauko ta gabaɗaya ta dawo jikin sa. Manal murya a sarƙe tace, “ni dai partner….” Shiru tayi ta ja numfashi jin abinda ya sa tsaya cak da maganar.
Kwanan Lubna biyu a gidan babu wanda ya ce mata ta dawo gida, daɗin zaman gidan itama take ji in ya fita hira suke sha da Manal, shima yaji daɗin zaman ta saboda in zai yi aikin dare bashi da matsala tafiya yake dan ya san duk abinda zai faru da ɗayar su ɗaya zata iya kiran sa ta faɗa masa.
Maganar Mujahid ta lafa babu wanda ya sake yi mata maganar shima Mujahid ɗin bai sake yin magana ba sai dai Allah ya jarabce shi da ƙaunar Lubna mai tsanani wacce ya tabbatar da bazai same ta ba a wannan lokacin.
A cikin kwanakin aka yi bikin Mubeena su Manal an sha hidima kullum bata nan dan ya hanata kwana duk dare zai je ya ɗauko ta da safe ya kai ta. Su Daddy sun zo Kano shi ne ya bada auren Mubeena da kansa aka yi komai lafiya lau aka kai amarya Abuja a ranar ne Manal ta kwana can washe gari suka dawo Kano.
Satin da ya dawo aka fara da Surayya Manal bata huta daga na Mubeena ba aka shiga hidimar bikin babbar ƙawa. Manal tayi hidima sosai ta kuma bayar da gudunmawa da jikin ta da kuma aljihun ta,
kowa ya yaba da abinda tayi dan tayi bahinta mijin ta ma yayi. Maman su Manal kan ba’a magana, dan babban abu ta ɗauka a hidimar bikin tace itace ta ɗauki nauyi gabaɗaya, ta faɗawa Daddy shima ya ɗauki nauyin kayan ɗakin amarya gabaɗaya. An yi kara da karamci sun rama alkhairin Maman su Surayya da alkhairi.
Bayan wasu kwanaki.
BDƘB3P45