← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 84

Sashe 33

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon sa tayi itama kamar zata sake magana sai ta fasa kawai ta wuce ta koma falon ta ta zuba nata abincin tana ci harda kunu ma Mama ta yi mata mara sugar. Tana shan kunun tana cin abinci Mama tace, "baki bani labari ba, ya ɗinkin naki?." Manal tace, "maganar rashin lafiyar ce ta ɗauke mim hankali, ɗinki yayi kyau sosai Mama."
"Ma sha Allah" ta faɗa bata sake mata magana ba domin ta fahimci daga fitar si zuwa dawowa su akwai canji a fuskokin su.

Tana gama cin abincin tashi tayi ta koma ciki ta kwanta tana aikin tunanin meye alaƙar shi da Rumana haka? Tana so ta tambayi Mimi ko Kausar amma kuma wata zuciyar na hana ta aikata hakan kar aga kamar ta cika bin diddigi, daƙyar ta iya daurewa tayi bacci.

Washe gari.

Da wuri ya fita ya shiga babban asibiti kafin ya wuce nasu saboda Rumana da take a can a kwance amma da baza shi ba. Da yaje ɗakin da yasan tana ciki ya shiga ya samu Mama ce a wajan ta tana zaune tana hhan tea, Rumana ma tana zaune amma da ka ganta ka san bata da lafiya ta ɗan rame lokaci ɗaya fuskar ta ta faɗa kamar wacce tayi zawo.

"Mummy barka da safiya." Mummy tace, "barka dai Adnan, ya Manal da Ayan ɗin?."
"Lafiya lau, ya mai jikin?" Ya faɗa yana kallon Rumana da take kallon sa tun shigowar sa. Mama tace, "gata nan a zaune, da sauƙi tunanin komawa gida ma muke yi."
"Allah ya ƙara lafiya" Mama ta amsa da amin kafin ya tashi daga gaban Mama ya zauna a kan kujera ya kalli Rumana yace, "ya jikin ki?."

Kallon sa take yi babu abinda yake zuwa idon ta sai lokacin da ta buɗe ɗakin da suke ciki shi da Manal, yanayin da ta gansu a ciki da kallon da ya mata tare da yin tsaki ya sake juyo da fuskar Manal ya ɗora daga inda ya tsaya. Runtse ido tayi nan take idon ta ya ciki da hawaye cikin tsananin zafin kishin da yake azalzalar zuciyar ta tace, "da sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya" ya faɗa yana ɗaukar wasu magani da suke ajjiye a gefe yana kalla yace, "Mummy wannan ne maganin da aka bata? Wanne likita ne ya bata?."

Mama tace, "eh sune, wata likita ce kamar ma bata jin hausa." Ya girgiza kai ya ajjiye maganin ya kalli Mama tace, "wallahi Mummy damuwa ce kawai take tayar da ciwon nan nata, in bata daina saka abinda yafi ƙarfin zuciyar ta ba nan gaba ciwon zai ninka wannan. Sai tana daurewa tana haƙuri ko dan lafiyar ta." Mama ta girgiza kai tace, "na sani Bebi, amma damuwar ta zo ƙarahe in sha Allah."

Gaban sa ya faɗi sosai ya kalli Maman suka haɗa ido ta ɗauke idon ta, ya sauke numfashi ya tashi tsaye yace, "zan je na duba marasa lafiya." Mama ta ɗaga masa kai ya fita. Bayan fitar sa da ɗan jimawa Mama ta masa waya tace sun wuce gida ta gaji da zaman tunda dai ta warware.

BDKB3P018

Mama sai da ta saka Rumana tayi wanka taci abinci ta sha magani ta tabbatar ta huta sannan ta zauna a gefen ta tace, "Rumana na san damuwa ce ta kawo miki wannan ciwon naki, tunda muka je gidan Bebi na lura da kin taho da damuwa, haka za'a cigaba da tafiya kenan sai dai ki daina zaman Kano saboda Bebi?."

Ta kallli Mama tace, "wallahi Mama ina daurewa kasawa nayi."
"Haka zaki cigaba da dauriyar, lokacin da muke jira ya kusa zuwa, matar sa ta haihu duk abinda za'a yi an kusa ayi a wuce wajan."
"Mama in na ganshi tare da ita ne sai naji zuciyata na bugawa fiye da ƙa'ida."

Mama ta riƙe hannun ta tace, "Shikenan baza ki ganshi da matar sa ba kenan? Yanzu in kin aure shi din ma haka za'a dinga yi?. Haka zaki dinga saka damuwa a zuciyar ki saboda kishi? Kan ki fa kike cuta bashi ko ita ba." Ta fara hawaye tace, "Wallahi Mama baya sona ne yanzu, har kyauta na kai masa amma da ya karɓa a inda yake a nan ya ajjiye. Sai kallon matar sa da yake saboda naje gidan kamar yana jin tsoron wani abun. ni naga alamun ma bai faɗa mata maganata ba, bata san maganar ba gaskiya."

Mama ta sauke numfashi tace, "dole ai yaji tsoron matar sa saboda matsayin kishiyar ta ki ke, yana son ki yana son ta dole hakan zai kasance."
"Mama ni ce nake son sa shi baya sona wallahi."
"Ki daina faɗar haka wallahi, Bebi yana son ki na tabbatar da hakan." Rumana tayi murmushi kawai amma bata yadda ba dan tasan ba haka bane, Mama tace, "ki kwantar da hankalin ki ina da rai da lafiya har yanzu, koda bani da rai auren ku babu fashi balle ina numfashi a doran duniya. Ki kwantar da hankalin sai kin aure shi in sha Allah."

Rumana ta kwanta a jikin Maman tace, "Allah yasa Mama, ina son sa wallahi, in na rasa shi bazan iya rayuwa ba." Mama ta dafa kanta tace, "kar ki damu, zaki rayu dashi har ki haifa masa yara in sha Allah." Tana kwance a jikin Mama ta share hawayen ta Mama tace, "ki kwanta ki yi bacci." Ta kwanta kamar yadda Maman tace tayi shiru tana tunanin ƙaunar da Adnan yake yiwa Manal.
Mama da ta fito falo Kausar ce da Lubna suke karatu ta kalle su tace, "in Bebi yazo ku ce masa ina neman sa." Suka amsa da to ta shiga ɗaki.

Ba jimawa ya zo ya shiga wajan Abba yaga baya nan ya dawo falon Maman duk suka gaishe shi ya amsa sannan ya ce, "Ina Abba yaje yau?." Kausar tace, "yace gaisuwa yaje amma zai dawo yanzu." Ya girgiza kai kawai bai ce komai ba ya shiga wajan Mama.

Ganin ta a kwance kamar mai bacci sai ya juya zai fita yaji ta kira sunan sa ya tsaya tare da juyowa tace, "dawo daman neman ka nake yi" ta faɗa tana tashi zaune shima ya koma ya zauna a carpet ita kuma tana kan gadon a zaune.

Mama ta kalle shi bayan ta tattaro nutsuwar ta tace, "Manal ta san da maganar auren ka Rumana kuwa?." Wani irin abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har ƙafafun sa, ya kulle ido ya buɗe ya sauke numfashi cikin yanayi mara daɗi. Mama duk tana kallon sa tana karantar yanayin sa tace, "baka ji me nace ba?." ya ɗago ido ya kalli Maman ganin tana kallon sa sai ya sauke kai ƙasa ya ce, "bata sani ba."
"Amma tun farko nace ka faɗa mata ko? Kenan baka yi abinda nace ba?."

Bebi ya ce, "ba haka bane Mummy, na ɗauka an bar maganar ne." Da mamaki take kallon sa jin abinda ya ce baki buɗe tace, "an bar maganar kace? Lallai da gaskiyar Rumana da tace yanzu baka son ta. Kenan kai ka manta na ce maka ko bayan raina in kana so na kwanta a kabarina cikin farin ciki ka auri Rumana ba? Ka manta na faɗa maka haka?."

Ya sunkuyar da kai Mama tace, "saboda maganar tawa da alqawarin da kayi min bashi da mahimmaci ko?, saboda ka raina ni ni ka ke kallo kana cewa ka ɗauka an bar maganar, wato da na mutu shikenan baza ka iya cika min alƙwarin da ka yi min ba?."

Ya girgiza kai cikin tashin hankali yace, "A'a Mummy, ba haka nake nufi ba don Allah......" ta dakatar dashi cikin fusata tace, "ya ka ke nufi Adnan? Inda na isa da kai baza ka furta abinda ka furta min yanzu ba."
"Ki yi haƙuri don Allah, amma ba haka nake nufi ba."
"Haka ne mana, gashi ka manta da alƙawarin da ka ɗaukar min na zaka auri Rumana ko bana numfashi a duniya, har ka manta saboda ka auri wata kun haihu ko?. Saboda kana da wata a gida ka manta da alƙawarin mahaifiyar ka ko?."

Bebi cikin rauni ya ce, "ki yi haƙuri Mummy, ba haka nake nufi ba, ina sane da maganar alƙawarin da na yi miki a kan ta. Wallahi Mummy zan iya yin komai a kan ki, ki daina cewa na raina ki don Allah."
"To indai baka raina ni ba kuma kana son farin cikina ka cika alƙawarin da ka yi min yanzu, indai kana son ganin walwala a kan fuskata ka auri Rumana a cikin kwanakin nan Adnan. Na bar ka ka zauna da matar ka har ta haihu nayi maka adalcin da ya kamata ace nayi maka matsayina na uwa, kaima lokacin ka ne da zaka yi min adalci matsayin ka na ɗa a wajena. Yanzu ba sai anjima ba kaje wajan Hajiya da kan ka kace mata kai ne ka ke son auren Rumana ba ni nace maka ba, daga nan ka dawo a cigaba da magana."

Gaban sa faɗuwa kawai yake yi ya rasa ya zai yi balle yayi magana Mama tace, "ka sanar da Manal yanzu dan ta san ka kusa kawo mata abokiyar zama. Tun farko na ce ka faɗa mata ka ƙi, yanzu sai ka san da fuskar da zaka sanar mata tunda haka ka zaɓa."

Ya sauke ajiyar zuciya ya kasa magana gabaɗaya, bakin sa ya kulle ya rasa abindai zai cewa Mama. Zuciyar sa bugawa take in ya tuna akan auren Rumana take magana, babban tashin hankalin sa bai wuce Manal ba. Da wacce fuska zai tunkare ta har ta fahimci abinda yake nufi?.

Mama ta lura da yanayin sa sai tace, "Bebi da ace ina da wani ɗan ba kai ba wallahi banza dinga ɓata lokacina ina faɗa maka kana ƙin yi ba, da yanzu na aura mata shi na ƙyale ka tunda kai baza ka iya yi min abinda nake so ba sai kaje ka ƙarata. Matsalar da aka samu kai kaɗai Allah ya bani shiyasa ka ke min abinda ka ke so."
Chapter 33 · 0% Book details