← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 84

Sashe 57

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta riƙe hannun Rumana da take kusa da ita tace, "na san kina son Adnan Rumana, na san da cewa ke kaɗai kika san abinda kike ji a zuciyar ki, na san ke kaɗai kika san raɗaɗin da kike ji a zuciyar ki. Amma ina so ki tuna haka jarabawar ubangiji ce, Akwai zafi sannan akwai sakamako nai kyau. Wannan duk abubuwan da suke faruwa dake wataƙila wani alkhairin ne zai faru dake, sannan Adnan ba alkhairi bane a rayuwar ki tunda har aka zo wannan ɓangaren, inda ya kasance alkhairi a wajan ki tun kafin a kai ga auren sa da Fatima ke zai fara aure amma da yake Allah bai ƙaddara hakan ba kalli abinda faru har hakan ya zama silar bayyanar mahaifin ki. Kar ki ɗauka Adnan ya ƙi ne, Wallahi Adnan yana sonki matsayin ki na ƴar uwar sa, da kin tsaya a wannan matsayin da na tabbatar miki zaki fi kowa da sa'ar samun ɗan uwa mai kula da lamarin ki. Bai zaɓi matar ya bar ki saboda baya son ki ba sai dan hakan shine mafita, in ya zaɓe ki ya bar matar sa a ganin ki yayi adalci?."

Rumana ta girgiza kai alamun a'a tana hawaye Hajiya tace, "kin gane abinda nake nufi kenan, ki yi haƙuri ki ta addu'a wataƙila ke matar gwamna ce ma baki sani ba, kinga ni za'a yiwa first lady." Rumana tayi murmushi Hajiyan ma dariya take yi kafin ta kalli Mama tace, "komai ya wuce Hauwa, bana so ki canja wa matar sa, bana so ki cigaba da ganin Adnan da laifi don Allah, bashi da laifi  matar sa ma haka, don Allah ki sassauta masa sai hararar sa da ki ke yi."

Mama ta girgiza kai tace, "in sha Allah Hajiya ya wuce." Hajiya tace, "Yauwa haka nake so naji, Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Aka amsa da amin har Rumana da take zaune ta goge idon ta tace, "Ni gidan Abban Abuja zan koma da zama gabaɗaya" ta faɗa muryar ta na kakarewa saboda yanayin yadda numfashi ta yake sauka.

Alhaji Mustapha yace, "babu komai Rumana, kina da ikon zama a duk inda kike so. Amma ki tuna yanzu mahaifin ki Allah bayyana shi, in kika samu lafiya sosai zaki je ki gaisa da ƴan uwan ki dashi kan sa mahaifin naki. Ki je kowa ya san ki in yaso sai ki dawo Abujan mu cigaba da zama." Alhaji Sulaiman ya ce, "gaskiya ne wannan, yana da kyau yanzu tunda kin labari ki je gidan dangin mahaifin ki a gaisa kowa ya san ki ki kuma san su, in yaso daga baya sai ki tafi Abuja kafin Allah ya kawo miki miji na gari ki yi auren ki." Hajiya ta amsa da amin suka ɗan cigaba da tattaunawa akan batun kafin su tafi gidan Mama da Rumana da Maman da kuma Adnan.

Bai shiga falon Maman ba sai da yayi sallah sannan ya shiga wajan Maman yaga bata nan ya shiga ya  shiga ɗakin Mmaan da sallama ya hango Rumana a zaune a kan gado, ya ƙarasa ya zauna akan kujerar ɗakin yace, "Ya jikin naki?."

Rumana ta gyara zama tace, "yayi sauƙi."
"Me kike ji yanzu?."
"Numfashi ne dai har yanzu bai min daidai ba" ta faɗa tana alamun sama da hannun ta ba tare da ta ƙarasa ba sannan tace, "in na zauna bana jin daɗin ƙirjina." Yace, "sannu, Allah ya ƙara lafiya. Ki dinga shan magani shi zai taimaka miki ki samu lafiya."

Ta ɗagq kai alamun eh yayi shiru bai ce komai ba itama bata ce komai ba. Ya ɗago ido ya kalle ta suka haɗa ido alamun yace, "ki yi haƙuri da abinda ya faru Ruman." Tayi murmushi tace, "babu komai, kamar yadda Hajiya ta faɗa ƙaddara ce na amince da haka, Allah ya rubuta ƙanwata ce matar ka shiyasa tun farko Allah bai baka ikon amincewa da...." Ta kasa ƙarasa faɗa saboda kukan da ya taso mata.

Tasowa yayi daga inda yake ya ƙarasa kan bedside ya zauna yace, "ki daina kuka don Allah, shima zai cutar dake."  Ta goge ido amma kukan yaƙi tsayawa ta kasa daina zubar da hawaye yace, "Allah bana so naga kina kuka, bana son ko kaɗan kin sani, don Allah ki daina bana jin daɗi."
"Mafarkina na zama matar ka bazai tabbata ba, mafarkina na so a kira ni matar Dr Adnan bazai tabbata ba har abada,da gaske ba da wasa ba ina son ka, amma son bazai min amfani ba” ta faɗa muryar ta na rawa sosai tana kuma sarƙewa.

"Allah bai rubuta hakan alkhairi bane a wajan ki shiyasa bai faru ba tun farko, tun kafin na san zan san wata me suna Manal a rayuwata nake tare dake, in da Allah ya rubuta zan aure ki da yanzu nuna da yara biyu dake ko uku ma Ruman. Kinga ko bayyanar mahaifin ki a yanzu bazai canja komai ba saboda Manal ba kowa bace a wajena. Amma rabon haihuwar Ayan shine ya kawo wannan tangarɗar tun asali, ba laifin ki bane ƙaddara ce wacce Allah ya rubuta faruwar ta bamu isa mu tsallake mata ba dole tazo ta tarar damu a inda muke."

Ta girgiza kai ta kalle shi idon ta yayi ka sosai tace, "haka ne, ni ma na amince hakan amma zuciyata ta gaza fahimta, na kasa gane hakan shine gaskiya."
"Zaki gane, zaki fahimta amma sai kin dawo hankalin ki kin nutsu sosai zaki banbance abinda yaje gaskiya da wanda yake ba gaskiya ba. Shaiɗan ne yake miki ihu a kunnen ki shiyasa kike ganin hakan ba daidai ba, amma da zarar kin nutsu kina karatun Al kur’ani zaki dawo daidai Ruman!" Ya faɗa murya a can ƙasa yana kallon idon ta.

Hannun ta ta ɗora akan hannun sa ya kalle ta suka haɗa ido ta riƙe hannun sa sosai tace, "zuciyata zafi take min sosai, na rasa yadda zan yi na cire son ka a zuciyata, ka bani shawara don Allah" ta faɗa tana kuka tare da ɗora goshi ta a hannun sa yana jin ɗumin hawayen ta a hannun sa.

Shiru yayi ya rasa abinda zai ce mata jin yadda take kuka sosai tana kuma riƙe da hannun sa. Baya son kuka yana daga cikin abinda yake ɗaga masa hankali. Kukan babba ko yaro ko kaɗan baya son ji yanzu sai ya damu. Daƙyar ya ce, "Na faɗa miki wannan kukan damuwa ce a wajan ki, kuma komai sai a hankali ba lokaci ɗaya zaka sauƙin abinda kike ji ba a zuciyar ki. Addu'a zaki dinga yi."

"Ka taya ni addu'a Allah ya cire min kai daga zuciyata, Allah ya bani ikon kallon ka matsayin Yayana kuma mijin ƙanwata. Ka dinga yi min addu'a kaji, in ba haka ba zan iya rasa rayuwata saboda yadda nake jin zuciyata nayi min ƙuna" ta faɗa tana kallon idanun sa da jajayen idon ta sake riƙe hannun sa duka biyun.

Ta bashi tausayi matuƙa, har zuciyar sa yake jin tausayin ta musamman maganar ta ƙarshe ji yake kamar in ta rasa rayuwar ta shine silar faruwar hakan.  Tausayin ta ya dabaibaiye shi sosai, jikin sa yayi sanyi sosai. Daƙyar ya iya furta, "baza ki mutu ba, zaki cigaba da rayuwa da farin ciki kamar kowa." Ta kalle shi tace, "Farin ciki...?" Sai tayi murmushi mai ciwo tace, "tunda na rasa ka bana tunanin zan iya sake samun farin ciki a rayuwata, Wallahi kaine farin cikina."
"Babu ta inda ɗan adam yake zama farin cikin wani, Sai dai ya za silar farin cikin wani Ruman. Allah ne yake bada farin ciki ga bawan sa a duk sanda yaso, don Allah ki miƙa lamarin ki ga Allah zai taimake ki zai kuma share miki hawaye."

Kai ta girgiza ya sake cewa, "in kina wannan maganar sai naga kamar baki amince da ƙaddara ba, kamar baki amince da Allah ne yake yi ba."
"Na amince, abin ne akwai ciwo."
"Haƙuri zaki yi, Allah ya baki ikon cinye jarabawar nan" ta girgiza kai ta kalle shi har lokacin bata saki hannun ba. Ta kalle shi tace, "Da gaske ka daina sona?."

"Rumana wannan ba maganar da zamu tattauna bace."
"Na sani, ina so na sani ne kawai. Da gaske ka daina sona ko kana faɗa min ne dan naji daɗi?." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "bazan miki ƙarya ba, amma Allah ya cire min soyayyar ki raina daga lokacin da kika auri Jawad. Na shiga irin wannan damuwar amma da na bawa Allah lamarina sai komai ya zama tarihi. Soyayyar da nake miki ta Yaya da ƙanwa ce da kuma shaƙuwar da muka yi wacce baza ta taɓa gushewa daga zuciyata ba."

Ta kalle shi ido jajaye tace, "da ka rasa ni kaima kaji abinda nake ji?." Yayi murmushi yana kallon ta ya ce, "Ruman don Allah ki adana wannan maganar, mu yi facing abinda ya faru a yanzu mu karɓi ƙaddara kawai ni da ke." Ta girgiza kai tace, "haka ne, Allah ya baka zaman lafiya da ƙanwata Manal" ta faɗa murya na rawa sosai.

Ya zame hannun sa daga riƙon da tayi masa yace, "Amin ya Allah. Allah ya baki wanda ya fi ni." Zatayi magana ya ɗaga mata hannu yace, "Allah na roƙa kar ki ce min komai." Ta ɗan murmusa kawai tana kallon wani wajan daban kafin tace, “ko babu komai na amsa sunan matar ka na ƴan kwanaki.”

Bebi ya kalle ta ya share abinda tace ya ce, "a ko yaushe ƙofa a buɗe take in kina son magana dani. Shawarar ko abinda yayi kama da haka zaki iya sanar dani nayi miki alqawarin baza ki zubar da hawaye ba. Matsayin biyu kike dashi a wajena ko nace uku, matsayin ƙanwata, ƙawata, kuma Yayar Matata."

"Kuma tsohuwar budurwar ka." Suka yi dariya a tare ta share hawayen ta ya kalle ta yana murmushi yace, "matsayin huɗu ne dake zan ce." Tayi murmushi itama tana girgiza kai bata ce komai ba.
Chapter 57 · 0% Book details