Sashe 28
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kalle shi sai ta ɗauke kai tace, "babu labarin ne." Bebi ya ce, "ni na san akwai, kawai yau baki yi niyar bani labarin bane ba, ko akwai abinda yake damun ki ne?."
"Babu komai."
"Yanzu kin ga kuna lokacin ƙarshe a makaranta, in kika gama me zaki yi?."
Manal tace, "Sai abinda Allah ya zaɓa min."
"Amma ai kina d abinda yake sanki wanda kike burin Allah ya tabbatar miki." Manal tace, "ni dai na san ina da ra'ayin buɗe bakery da cafe kuma ka sani, daga nan shikenan kawai."
"Allah yasa ya kuma cika miki burin ki." Ta amsa da amin y ace, "kuma naga zaki iya sosai." Bata ce komai ba tayi masa shiru tafiya kawai take yi kafin ta tsaya ya kalle ta tace, "bayana naji ya riƙe, ruwa zan sha."
"Oh god! Gashi ban ɗauko ruwa ba yau." Manal tace, "muje kawai."
"A'a tsaya na koma na ɗauko miki."
"A'a bar shi zan iya."
Tafiya suka cigaba da yi a hankali har suka je farkon estate ɗin kafin su dawo, daƙyar take tafiya sosai bayan ta ya riƙe ganin baza ta iya ba sai ta samu wani ɗan tudu a ƙofar wani gida ta zauna a kai tace, "na gaji." Da yake yana da ɗan faɗi kaɗan sai ya zauna shima ya ce, "Sannu." Kai ta ɗaga yana kallon fuskar ta, gabaɗaya babu walwala a tare da ita shi kuma ba haka ya saba ganin fuskar ta ba duk ya damu da hakan.
Wayar sa ake kira ya ɗauka yana magana kafin ya kashe wayar ta kalle shi tace, "aikin ne?." Ya girgiza kai yace, "akwai wacce aka yiwa aiki shine ta farka, ba sai naje ba zan saka ayi handling case ɗin." Bata ce komai ba ya kira waya yana magana kafin ya sake kashe wayar.
"Assalamu alaikum."
A tare suka kalli wajan da akayi sallamar Bebi ya amsa yana kallon matar da take tsaye a kan su, Babba ce mai shekaru duk da bai nuna ta ba amma ido ba mudu ba ya san kima, kana ganin ta ka san ta manyanta dan shekarun zata kai sa'ar Mama ko ta girmi Mama. Tayi murmushi tace, "Sannun ku fa, nazo na tsaya a kan ku baku sanni ba. Ku yi haƙuri tambaya nake yi."
Bebi yace, "babu komai, Allah yasa mun sani." Ta kalli Manal da take kallon ta tace, "wallahi matar ka ce take min kama da wata wacce na sani, shine nake so na tambaye ta naji ko ta santa?." Bebi yace, "babu komai ki tambaye ta."
Ta kalli Manal tace, "sannu daughter, ya jikin?." Manal ta amsa matar tace, "Allah ya raba ku lafiy, ya baki haihuwa mai sauƙi." Ta amsa da amin ta kalle ta tace, "Akwai wata da na sani fuskar ta irin ta ki ce, duk da nasan baza ki san wacce na sani din ba amma duk yadda akayi kamar kina da alaƙa da ita. Don Allah kin taɓa sanin ahlin marigayi Muhammad Jalingo?."
Gaban Manal ya faɗi sosai ta kalli Bebi shima ita yake kallo yana jiran yaji abinda zata ce, Manal ta kalli matar bayan ta aro nutsuwa tace, "Muhaammad Jalingo! Gaskiya ban san su ba, ban taɓa jin sunan ba ma sai yanzu da ki ka faɗa min." Ta girgiza kai tace, "kaico! Wataƙila kama ce kawai, amma kin yi kama da ita sosai hakan ya saka nake ji a jikina kina da alaƙa da ita, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci."
Bebi zai yi magana Manal ta riƙe masa hannu hakan ya saka ya kalle ta ta kalle shi ta ɗauke kai daga kallon sa tace, "babu komai." Ta yiwa Bebi godiya ta shiga wani babban gida da yake kusa da wanda suke zaune tana sake waiwayen Manal.
Manal tashi tayi daƙyar shima ya miƙe ya riƙe ta suka cigaba da tafiya bai mata maganar ba dan so yake sai sun je gida. Ba jimawa suka je gida bata zauna hutawa ba tayi wanka ta saka riga ta fito taci zogalen da ya haɗa kafin su tafi, ta sha ruwan cucumber da Apple da ya zaka kamar ruwan shan ta. Sai da yaga ta dawo hankalin ta sannan ya zauna kusa da ita ya ce, "amma Partner meyasa kika cewa matar can baki san ahlin kakan ki Muhammed Jalingo ba?."
Shiru tayi bata yi magana ba hakan ya saka ya ce, "magana nake miki fa kin yi min shiru." Ta kalle shi tace, "Mama bata bani damar hakan ba, umarnin ta nake jira in ta bani dama zan yi magana. Kuma meye ma amfanin maganar? Mutanen da suka aurar da mahaifiyata ga wanda basu sani ba, kuma suka bashi ita ya tafi da ita duk inda yake so alamun yaje da ita su basa da buƙatar zaman ta. Me zai saka ma in na gansu nace ni ahlin su ce? Yadda suka zare Mamana daga cikin su babu amfanin faɗa musu, koda dukkan su zan gani wallahi bazan nuna na san su ba" ta faɗa tana kallon wani wajan daban.
"Ƙaddarar zuwan ki duniya, ƙaddarar abinda yake cikin ki shine ya saka duk abubuwan nan da kika faɗa suka faru. In hakan bai faru ba da yanzu wataƙila bakya duniya, Allah yayi nufin halittar ki shiyasa hakan ta kasance." Taɓe baki tayi alamun maganar bata wani ratsa ta ba ta cigaba da kallon tv zuciyar ta na zafi in ta tuna riƙe hannun sa da Rumana tayi.
Azurfar da Rumana ta bashi ta kalla taga tana inda ya ajjiye bai ɗauke ba tace, "baka son kyautar buduwar taka ne ka bar ta a wajan?." Kallon abinda take kalla yayi ya kalle ta ya ce, "Partner wacece budurwa ta kuma?." Ta kalle shi tace, "Ka fini sani ai." Ƙoƙarin tashi take ya riƙe hannun ta ya ce, "wai daman akan ta ki ke wannan fushin Partner?."
Ta kalle ta tace, "akan me zan yi fushi bayan tare na gan ku? Ƴar uwar kace kuma wacce ta kasance ta musamman a wajan ka, meye na Manal da aka auro daga gefe ita da ba ƴar uwa ta musamman ba?. Akan me zan yi fushi da wacce na gan ku tare? Ƙanwar ka ce fa."
"Partner!" Ya faɗa yana amtsowa kusa da ita sosai yana kallon ta tare da riƙe hannun ta yace, "meye na wannan maganar? Ko ya mahimmacin ta yake ai bata kai ki ba ko?."
"Anya kuwa, ko bata kai ni ɗin ba tana gab da zuwa ta wuce ni."
"Haba Manal, kokwanto ki ke a kaina?."
"Zahiri na gani."
"A duniya Mummy kawai za'a cire sai ke, duk wata mace a duniya bayan ki zata biyo ko ya muke da ita."
Manal ta ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ban saba da wannan fuskar taki ba, kin saba da fuskar walwala da murmushi don Allah ki cire wannan ki saka waccan ta fi yi miki kyau."
"Ka kasa faɗa min meye alaƙar ka da ita ne."
"Ai na faɗa miki wacece ita a wajena."
"Ban yarda ba, gwara ma ka san wallahi ban yarda ba na jika ne kawai."
Yayi shiru yana kallon ta tace, "har gidana, har cikin falona tazo tana riƙe hannun mijina kuma ace min babu komai a tsakani?, daga yadda ka yi mata magana nuni yake da ta saba yi maka. Tun a gidan Mummy na tabbatar da akwai wani abun a ƙasa, saboda kallon da take maka da yanayin da take maka magana daban da na ƴan uwan ka, yadda take kallon idon ka tana magana ko ni bana yi. Kuma kawai sai kace min babu komai a tsakanin ku ƙanwar kace kawai na yarda? Meyasa Mimi, Lubna, Kausar duk basa yi sai ita?."
Ganin ta fara fusata tana magana cikin faɗa sai shi ya sauka dan ya san laifin sa ne da ya faɗa mata tun farko da ba haka ba. ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, faɗan nan ne bana so saboda yanayin da kike ciki." Ta kawar da kai gefe fuskar nan a daure soaai bata ce komai ba.
Ya ce, "yanzu ya ki ke so nayi miki? Na faɗa miki abinda yake gaskiya amma kin ƙi yarda, to ƙarya zan faɗa miki?." Ta kalle shi tace, "ƙaryar ka faɗa ka ɓoye gaskiyar, a kan fuskar ka ga hakan nan ya bayyana. Wallahi ban yarda babu komai tsakanin ka da Rumana ba, Akwai abinda ka ke ɓoye min wanda baka so na sani."
"Partner ni nake miki ƙarya?."
"Ban ce kayi ƙarya ba, nace kawai ƙaryar ka faɗa ka ɓoye gaskiyar. In baza ka faɗa min ba shikenan a bar shi kawai ba sai naji ba" ta faɗa tana sake yunƙurawa da niyar tashi. Komawa tayi ta zauna saboda ciwon da taji ya riƙe mata baya ga marar ta na riƙewa.
"Me kike ji? Lafiya dai?" Ya faɗa yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "babu komai." Shiru yayi ya sauke numfashi yana son faɗa mata gaskiya amma tashin hankali ne baya so ta shiga Allah ya sani, hakan ya saka ya ce, "zan faɗa miki ko meye ma yake faruwa akan ta amma sai kin haihu." Ta tashi da ƙarfin hali tace, "ka riƙe abinda ka kawai ba sai na ji ba, ai ni ganau ce ba jiyau ba" ta faɗa tana shiga ɗaki ta bar shi a wajan a zaune. Numfashi ya sauke bai tashi ya bita ba dan yasan baza ta saurare shi ba, yayi shiru yana kallon tv domin kuwa yana tunanin lokacin da Mama zata dawo da maganar da ta wuce.
Ranar haka ta kwana sai shi ya bita ɗakin ya kwanta dan bata sake fitowa ba kuma bata ce masa komai ba, duk da yana yi mata magana akai akai amma taƙi bashi amsa dole ya ƙyale ta duk da taso fusata shi haƙuri yayi ya danne.