Sashe 42
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mubeena tace, “da wani suka zo tare da mahaifin Adnan ɗin wai shine mahaifin mu.” Gaban Manal ya faɗi sosai ta kalli Mama ta kalli Mubeena tace, “kuma da gaske shine mahaifin na mu?.” Mubeena tayi shiru suna kallon Mama suna kuma so su ji me zata ce. Mama tayi ajiyar zuciya tace, “ƙwarai shine, bazan ɓoye muku shi ba, Tabbas shine wanda yayi silar zuwan ku duniya. Ko da za’a shekara ɗari fuskar sa baza ta taɓa ɓacewa daga idanuna ba.”
Manal tace, “kuma bai ji kunyar zuwa yace mu yaran sa bane?” Manal ta faɗa ido yana cikowa da hawaye. Mama tace, “wannan duk bai tashi ba Manal, zama zaku cigaba da yi a matsayin wanda mahaifin su ya rasu, sannan dukiyar da take wajan sa ko yanzu zan faɗi na muku ku tabbatar kun karɓa, ko da baza ku yi komai da ita ba ku sadaukarwa da marayu.”
Manal tace, “to Mama ni me zai haɗa ni magana dashi har da zamu tambayi wata dukiya? Yaje ya cigaba da cin haram, lahirar sa yake lalatawa ba tamu ba, shi zai girbi abinda ya shuka a lokacin da hakan bazai masa amfani ba.”
Mama ta riƙe hannun su tace, “baku da wani uba in ba Baba ba, a yanzu da nan gaba da ko ma yaushe ne babu wani wanda zamu kalla matsayin uba in ba shi ba.” A lokacin Baba ya shigo ya ji abinda take cewa ya ƙaraso yana cewa, “Haba Zahra, haba wannan wacce irin magana ki ke faɗawa yaran nan?.” Sai kuma ya kalle su yaga gabaɗaya hawaye suke yi ya kalle ta yace, “Wannan mutumin da ake magana a kai fa mahaifin su ne, kin amince da shine ya haife su meyasa zaki saka su a gaba kina faɗar wannan maganar?.”
Mama tace, “bashi da wannan darajar a idona balle na cewa yarana su kalle shi da wannan mutuncin.” Jin abinda tace sai Baba yace, “Mubeena, Manal Ku koma falona ina zuwa.” Tare suka tashi suka fita jikin su a sanyaye. Baba ya zauna ya kalli Mama yace, “wannan kalaman da kike faɗa marasa daɗi akan mahaifin su ba daidai bane, ke in bakya son sa saboda abinda ya yi miki ai ke ba haihuwar ki yayi ba, su kuma ki tuna haihuwar su yayi kuma akwai jinin sa a jikin su. Ya zaki dinga kiran da mara mutunci a gaban yaran da ya haifa? Wannan ai ba magana wacce ya kamata ta fito daga bakın ki bace, har kice wai basu da wani mahaifi sai ni? A wajan ki hakan daidai ne?.”
Mama tayi shiru bata ce komai ba Baba yace, “na san bai kyauta miki ba, bai kyau tawa rayuwar ki da ta yaran ki ba amma duk da ya tafi ya bar ki ɗin me kika fasa? Kin daina numfashi?, kin daina rayuwa?, kin daina ci da sha?, kin rasa suttura da farin ciki?, kin rasa cigaban rayuwa ne ko akasin haka?. Babu abinda kika rasa, rabuwar ki dashi wani sabon shafin ya buɗe a cikin rayuwar ki, farin cikin da ki ke yi a yanzu a lokacin da kuna tare baki yi shi ba, kwanciyar hankalin da Allah ya baki a lokacin da kuna tare baki samu ba. Meyasa baza ki tura masa aniyar sa ba? Meyasa baza ki share maganar komai ya wuce bane ba?, In ke bai wuce a wajan ki ba meye na zuga yaran sa akan kar su ga mutuncin sa?, ke a ganin ki tarbiyya ki ke koya musu?.”
Mama tace, “Saboda bai cancanci naga mutuncin na sa bane, bai kai wannan matsayin da za’a girmama shi ba, bai kai wannan darajar da yarana zasu kira shi Baba ba. Wallahi ba dan Manal na son Adnan ba har shi sai ta bari, baban sa ya shafa masa baƙin fenti.”
Ganin ta fara zubar da hawaye Baba yace, “babu wanda ya san abinda kike ji a zuciyar ki sai ke ɗin kawai, ɓacin ran da kike ji a ƙarƙashin zuciyar ki sai dai ke ɗin kawai. A san an cutar dake anyi miki ba daidai ba, an tozarta ki sosai amma yanzu waye yazo yake son magana dake?, waye yazo yana so ki bashi dama kawai ku yi magana? Fatima faɗa min waye yazo gare ki saboda ya nemi yafiyar ki?.”
Mama hawaye take sharewa bata ce komai ba Baba yace, “dan kin nisnta kan ki dashi daman yanzu babu komai tsakanin ki dashi amma yaran sa fa? Dole ko bakya so Manal da Mubeena shine ya haife su, meyasa kike faɗar ko wacce magana a kansa a gaban idanun su?, ɗa da mahaifi fa sai Allah, su zasu iya karɓar sa a matsayin uba a gare su, daga baya kuma su dinga miki kallon wacce take aibata baban su a gaban idanun su, har abada baza su manta da wannan kalaman da kika faɗa akan wanda ya haife su ba, dan kin cire sunan sa a gaban sunan su a makaranta baza ki taɓa goge shi a cikin jinin su ba Fatima. Mahaifin su ne komai lalacewar sa, ko a yanzu da kike zuga su akan sa in suka yi masa wani abun ba daidai ba zunubi Allah zai rubuta musu, in a baya basu san shine ya haife su ba yanzu sun sani. Haba Zahra, kamar ba ke ba kike irin wannan maganganun?, ko dan gaba ba’a aibata iyaye a gaban ƴaƴan su, saboda ke auro ki yayi su kuma haifar su yayi, ke a yanzu baki da gadon sa in ya bar duniya, amma su ko yau ya mutu sai an raba gado an basu kamar yadda Allah yace. Don Allah ki dawo nutsuwar ki.”
Mama tayi shiru kawai bata ce komai ba, maganganun sa kuma ba shigar ta suke yi ba shiyasa tayi shiru. Ban baki ya cigaba da yi mata yana nuna mata kuskuren ta kafin ya koma wajan su Manal ɗin.
Su ma faɗa yayi musu akan faɗar ko wacce magana akan mahaifin su, ya kuma nuna musu ko meye shine ya haife su kuma yana da haƙƙi a kan su, ko yanzu suka zage shi suna da zunubi dan sun san baban su ne. Babu wacce tace komai har ya gama musu faɗan ya fita, Manal tsabar haushi ko tashi ma bata yi daga wajan ba tayi zaman ta zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi.
BDƘB3P24
Manal bayan sallar magriba Baba ya saka ta tafi gida, tare suka koma da Mama duk da tana cewa ta kusa godowa gida tunda ta warware kamar ba mai jego ba. Da suka koma gidan Bebi baya nan, Manal ta zama wani iri har Mama ta tambaye ta abinda yake damun ta ganin yanayin ta. Bata ɓoye mata ba ta bata labarin komai, Mama ta dinga jinjina lamarin ta bata haƙuri tacigaba da rarrashin ta.
Bebi sai da ya tsaya ya taho musu da abinci dan ya san baza a samu damar girki ba, a kan hanyar sa ta wucewa zuwa gida yaga ana tsayar dashi. Tsayawa yayi da motar ya suke glass ganin matar da suka taɓa magana da ita a lokacin da suka fito tattaki shida Manal da cikin Ayan.
“Kayi haƙuri, na tsayar da kai akan hanya, Wallahi na jima a nan a tsaye ina jiran ka.” Bebi yace, “babu komai, Allah yasa dai lafiya.”
“Ba lafiya ba.”
“Ina jin ki.”
“Don Allah ka faɗa min gaskiya, Tsakani da Allah matar ka tana da alaƙa da dangin Muhammad Jalingo?. Wallahi ban gamsu da abinda tace ba kwanaki, gabaɗaya zuciya faɗa min take ita jinin gidan ce, suna matuƙar kama da matar gidan margayiya Hajiya Nusaiba, wannan kamar ta tafi fitowa da ƴar gidan da ta ɓace aka nema aka rasa, in ka san wani abu ka sanar dani son Allah.”
Bebi ya sauke numfashi yace, “amma meye alaƙar ki dasu wanda ki ke magana a kai?.” Matar tace, “Sunana Halima, wannan gidan shine gidan da nake zaune a duk san da nazo kano. Ni ƴar Muhammad Jalingo ce, hakan ya saka nake da tabbacin wannan jini na ce, saboda akwai wacce ta ɓace mana itace ƙarama a gidan mu, mun nema ta sama da ƙasa amma mun rasa, Sai nake ganin kamar wannan ɗin ce duk da shekarun ba ɗaya bane amma ni wallahi na kasa gasgatawa.”
Kallon ta Bebi yake yi ganin kamar bai yarda da ita ba sai tace, “bazan maka ƙarya ba, a haife na haifi wanda suka fi ka shekaru. Da gaske nake ni jinin marigayi ce kuma abinda na faɗa maka shi iyalan gidan mu suke so su ji gabaɗayan mu.”
Bebi yace, “ina da buƙatar ganin iyalan gidan naku gabaɗaya in akwai damar hakan.” Matar tace, “me zai hana, Sai dai yawanci su ba a kano suke zaune ba a Abuja suke, mazauna Jalingo ɗin kaɗan ne kuma mata ne wanda aure ya zaunar dasu a can. Amma gobe zan iya haɗa maka zama da babban Yayan mu gabaɗaya na gidan, wataƙila ko zata gasgata abinda nake faɗa.”
Bebi yace, “zan so hakan.”
“Ga number ta, gobe in sha Alalh zai zo Kano gaisuwar rasuwa zan maka waya kazo ku je inda yake a nan garin.” Bebi ya saka hannu ya karɓa tayi godiya sosai shi kuma ya ja motar ya tafi. Bazai faɗa mata wacecw Manal ba har sai ya tabbatar da abinda take faɗa gaskiya ne sannan zai sanar dasu Manal jinin su ce.
Ko da ya shiga gidan a falon sa a tsaye ya same tana kwashe kaya, yayi sallama ta amsa ya bita da kallo ganin ta babu walwala ya san gaji labari. “Sannu da zuwa” ta faɗa daƙyar ya amsa yana kallon ta kafin yace, “ga abincin nan, ki kawo min nawa” ya faɗa yana ajjiye mata ya shiga ɗaki.
Ɗauka tayi tare da yin abinda yace ta kaiwa Mama ragowar da yawa ta fito ta ɗauki wanda ta zuba ta kai masa. A zaune ta ganshi yana danna waya ta bashi abincin ya karɓa ta ajjiye masa ruwa da lemo zata wuce ta fita ya ce, “An baki labarin mahaifin ki kenan.”