Sashe 69
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Komai ya wuce ka ke cewa fa Mujahid, fyaɗen da kayi mata shine komai zai wuce?." Mujahid yace, "nasan a wajan ka da ita da kowa ma nata bazai wuce ba, amma ku daure ku yafe min tunda na bar nan kullum cikin tunanin ta nake, na so na daure na kawar da komai daga rajna amma abin yaci tura na kasa. Wallahi Adnan Allah ya ɗora min son Lubna a lokacin da ban yi zaton haka ba, a yanzu ji nake in ba da Lubna ba bazan iya rayuwa ba."
A fusace Adnan yace, "za kuwa ka mutu, domin baza ta taɓa yin rayuwa da kai ba har abada wallahi. Ka ma rajna min hankali, dan kaga an yi shiru da maganar ko?, To yanzu ka kawo kan ka, in naso sai na zama silar zuwan ka gidan yari."
Mujahid yayi murmushi yace, "wallahi Ina son Lubna so na tsakani da Allah, tun bayan abinda ya faru ban sake aikata abu makamancin wannan ba, zan iya cewa shiryu, tun daga kanta nake na daina aikata komai wallahi. Kayi haƙurj ka bani dama na same ta na bata haƙuri.
A fusace ya sake cewa, "babu ita babu kai, babu kai babu ita. Na rantse kaka da Allah na ganka da Lubna sai na saka anyi maka dukan da ranka zai iya barin jikin ka. Burin ka na ƙona min rai ya cika ka yiwa ƙanwata fyaɗen meye na dawowa rayuwar mu yanzu?, Ko kana tunanin wannan fuskar da ka sako zata iya yaudarata ne?, Ka tuna waye a gaban ka kafin ka fara tsara min labari."
Yayi murmushi yace, "ba labari bane. Wallahi da gaske nake. Ina son Lubna kuma inda za’a bani sama auren ta....."
"Kar ka sake ka ƙarasa, kar wannan kalmar ta fito daga bakin ka domin zaka iya tsintar haƙoran ka a tafin hannun ka wallahi. Ni zaka kalla ka faɗawa wannan maganar? Ni zaka zo har inda nake kana faɗa min wannan maganar banza da wofin?. Na sanka ciki da waje, baka isa ka raina min hankali na ɗauka ba, kuma wallahi in ka sake ka bibiyi Lubna wallahi sai na yi maka abinda zaka yi dana sanin sanin Adnan a rayuwar ka, sai kayi dana sanin sanin Lubna a rayuwar ka. A yanzu ma ka jira sammaci zan maka ka a kotu dan dawo da hannun agogo baya."
Mujahid zai yi magana Adnan cikin tsaya yace, "ka fita ka bani waje!." Mujahid yace, "zan fita, amma inda ace ba har zuciyata maganar nan take ba da baza ka ganni a nan ba wallahi, da gaske nake maka duk abinda na faɗa ba ƙarya nake ba." Huzaifa yace, "baka da kunya wallahi, baka san kara da mutunci ba. A zaman amanar da akayi da kai ƙanwar Adnan ƙanwar ka ce, ko wani ka gani zai yi mata kwatankwancin abinda ka yi mata kai mai iya kare ta ne, amma kai ne da kanka ka yaudare ta har ka aikata mata fyaɗe. Tirr da halin ka wallahi, za kuma kayi dana sani a lokacin da baza tayi maka amfani ba."
Ya kalli Huzaifa yace, "Nayi dana sani. A yanzu ina kan yin ta ma Huzaifa." Landline Bebi ya ɗauka yana kiran security na reception, ganin haka sai Mujahid yace, "zan fita Adnan, amma zan sake dawowa" ya faɗa yana fita daga office ɗin duk suka bishi da kallo cikin tsananin ɓacin rai.
BDƘB3P43
Yana fita Adnan ya kama ƙagu yana zagaye office ɗin Huzaifa yace, “tun farko naso ace an kama Mujahid Adnan, da yana prison yanzu da ba haka ba.” Adnan ya kalle shi yace, “bani da hujjar da zan kama Mujahid, Mujahid ba tilastawa Lubna yayi ba itace ta kai kanta har inda yake, bani da hujjar da zan kai shi kotu akan laifin fyaɗe ba.”
“Kana da hujja, ko iya hujjojin asibitin nan sun isa a kama Mujahid, kuma ita yarinyar da message ɗin da yayi maka duk hujja ce da zata saka a kama Mujahid.”
“Magana ake ta shekara ɗaya da wani abun da faruwar wannan abun fa Huzaifa.”
“Ko shekara goma ne akwai hujja da za’a kama Mujahid, barin Mujahid yanzu barazana ne ga Lubna, zai sake ƙoƙarin cusa mata kansa a zuciyar ta ƙarshe azo ana dana sani.” Adnan ya girgiza kai yana tunani kafin ya fita daga office ɗin. Sun jima a cikin asibitin kafin su fita su je su gaishe da Hamza daga nan Adnan ya wuce wajan Mama.
Sai da yayi sallar magriba a masallaci sannan ya shiga wajan Mama da sallama ya same ta ita da Farida suna hira. Zama yayi kafin ya sauka daga kan kujerar ya tsuguna yace, “Mummy ina kwana.” Mama tayi dariya tace, “kwana kuma?, Da alama yau baka fita ba.” Yace, “Au ina yini Mummy” ta amsa tana kallon sa ya koma ya zauna Farida tace, “Wallahi ƙiba ka ke yi yaron nan, ko da yake kana auren chef ai dole ka yi ƙiba.”
Ya ɗan saki fuska kaɗan yace, “nima na gani wallahi, kwana biyu bana traning ne.” Mama tace, “ɗazu Manal tazo ta gaishe ni har dambun kaza da wainar shinkafa ta kawo min mai daɗi, yanzun nan Kausar ta cinye wainar.”
“Ban sani bama.”
“Haka tace, daman tace min baka san ma zata zo ba gida taje sai ta biyo ta nan. Sai iv bikin Yayar ta da ta kawo min.” Farida tace, “ai gaskiya tana da kirki, ni da farko na ɗauka kirkin nata na farkon zuwa ne, gashi tafiya tayi nisa bata canja ba. Ba wai dan kaji daɗi nake faɗa ba,wallahi in bata dashi a gaban ka zan faɗa dan baza ka dake ni ba” ta faɗa tana kallon sa.
Taɓe baki yayi kafin yace, “Ya maganar Mimi kuwa? Taga likitan?.”
“Wanne ganin likita ana zancen Allah ya kawo rabo” Farida ta faɗa tana kallon sa. Ya kalle ta ya ce, “daman ai ke ki zugawa akan taje asibiti, haka kawai shekara ɗaya kacal ku fara zancen infertility kamar wacce ta shekara goma.”
Farida tace, “dole fa mu damu, dangin miji basu da daɗi yanzu sai a fara tunanin wani zance ana cewa bata haihuwa ko wani abun.” Ya kalle ta yace, “kawai dai mata bakwa rasa abin magana ne kawai. Amma Allah na tuba shekara ɗaya tal a fara zancen wani infertility ana zaune lafiya?” ya faɗa yana kallon Mama.
Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe tsaye ya kalli Mama ya p
ce, “Mummy na wuce gida, tun safe ina asibiti sai yanzu na dawo na gaji sosai.”
“Allah ya kiyaye, ka yi min godiya wajan Manal na gode.” Ya sauke ajiyar zuciya baice komai ba. Farida tace, “lafiya dai ka ke ko?.” Ya ɗan motsa hannun sa yace, “to lafiyar dai zan ce.
Sai da safe” ya faɗa yana fita daga falon.
Yana shiga cikin gidan sa ya samu Manal a tsaye a falon Ayan sai kuka yake tana ta zagaye da alama ya jima yana kukan. Ya kalle ta yace, “ya dai? Lafiya yake kuwa?” Ya faɗa yana karɓar sa daga hannun ta. Manal tace, “tunda na dawo yake kuka wallahi, na rasa abinda zan yi masa yayi shiru.”
“Kuma ba yunwa yake ji ba?.”
“To ya ƙi karɓa ma, na rasa ya zanyi duk ya ruɗa ni.”
Har lokacin kuka yake yi yana hannun sa yana jijjiga shi amma yaƙi shiru, sake karɓar sa tayi ta zauna ta sake bashi nonon yaƙi karɓa sai kuka kawai yake yi. A hankali kukan nasa kuma sai ya fara raguwa tana jijjiga shi a jikin ta sai yayi bacci.
Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi yana kallon ta tace, “ni na san lafiya lau yake wallahi, kawai rigima ce wacce ya saba” ta faɗa tana kwantar dashi a hankali tana tsoron kar ya tashi. Ɗaki ya shiga yayi wanka ya fito ya samu bata falon ya ƙwala mata kira ta shigo falon ya ce, “bani abinci yunwa nake ji.”
Manal tace, “yanzu zan ɗora.” ya juyo yana kallon ta ya ce, “yanzu zaki ɗora fa kika ce?.”
“Tunda na dawo yake kuka ban samu na ɗara daga falon nan bama balle na shiga kitchen, girkin nake taso nayi maka amma na rasa ya zanyi.” Tsaki yayi yace, “yanzu har sai na jira an dafa abinci sannan zan ci?.”
Manal tace, “to ya zanyi?.” Tsaki ya sake yi alamun bai ji daɗi ba ya ce, “ki barshi kawai, bazan iya jira har a dafa ba gaskiya.” Manal tace, “ina da waffles in zaka fara ci kafin na dafa maka abincin, akwai dambun kaza ma kafin na fita na yi.” Ya ɗan kalle ta kafin ya amsa ta wuce kitchen ta kawo masa ta ajjiye a gaban sa. Ganin sai ɓata rai yake yi sai taji babu daɗi tasan baya so ya dawo bata gama abinci ba tace, “kayi haƙuri, yanzu zan dafa maka couscous tunda yafi sauƙi.”
Ya fara cin waffles ɗin da ta shafe shi da chocolate sai ƙhamshi yake yi ya ce, “ko barshi ma, in naci wannan ya ishe ni.” Ta kalle shi tace, “ni ma baka ci abincin ba dole na dafa yunwa nake ji sosai.”
“Na taho da fura ki buɗe mota ki ɗauko sai ki dama ki sha ko?.” Manal tayi ajiyar zuciya tace, “na huta” ta faɗa tana ɗaukar key ɗin motar sa ta fita harabar gidan. Ba jimawa ta dawo ta ajjiye makullin ta shiga ciki ta dama fitar ta dawo tana sha duk da babu zaƙi amma taji daɗin ta ta kuma ƙoshi sosai.
“Mummy tace min kin je.” Ta ɗaga kai tace, “eh na biya da na dawo, na kai nata iv bikin Yaya. kaima ga naka can a jakata.” Ya kalle ta yace, “tace min kin kai mata dambun kaza harda wainar masa, an gode.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba.
Tashi tsaye yayi ya ce, “Partner kwanciya zanyi, na gaji yau sosa bacci nake ji.” Manal tayi murmushi tace, “A huta lafiya.”
“Sai kin shigo” ya faɗa yana wucewa ya shige ɗaki ba tare da ya kalle ta ba. Itama sai da ta gama abinda yake yi sannan ta shiga ɗakin nasa a lokacin ma har yayi bacci.