Sashe 35
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama tace, "A'a bazai yu ba, Surayya maza ɗora koda couscous ne tunda yana da sauƙi kafin a gama gaisawa ma ya yi koda sun zo, akwai miya a fridge sai ki ƙara naman ciki a soya ta, akwai salad ɗin Manal shima a gyara shi a haɗa musu dashi." Surayya ya amsa ta fara ƙoƙarin ɗorawa ita dai Manal tana tzaune kawai a gefe. Fitar Mama ya saka Surayya ta kalle ta tace, "wai lafiya ki ke? Gabaɗaya kin canja me ya same ki?."
Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, "ban sani ba, amma akwai abinda yake damun partner yaƙi sanar dani." Surayya jin hakan sai ta cigaba da abinda yake gaban ta kawai bata ce komai ba dan bata shafe ta ba maganar.
Lokacin da motar su ta tsaya lokacin Surayya tw zuba couscous a ruwan da ta ɗora, shigowar mutane falon suka ji hakan ya saka Manal tashi ta fito falon da ta saba zama ta tarar mata guda huɗu, ƴan mata biyu da yarinya wacce bata wuce shekara goma ba, Sai babbar mace wacce ta kasance mahaifiyar su, dan kana kallon ta zaka ga kama da Huzaifa sosai. Manal tayi murmushi ta ƙaraso tana cewa, "Sannun ku da zuwa." Ƙaramar yarinyar cikin su tace, "woww! I thoroug you can't speak hausa."
Wacce take zaune kusa da ita ta doke ta tace, "kin cika magana ko gaishe ta baki ba." Manal da murmushi ta ƙarasa ta gaisa da Maman su Huzaifa ta amsa da murmushi tace, "an samu ƙaruwa ko." Manal ta amsa Maman ta sake cewa, "Allah ya raya mana shi, Gashi kuwa sak ke" ta faɗa tana kallon yarpn da yake hannun ta.
Manal tayi murmushi ta kalli ƴan matan tace, "Sannun ku." Babbar cikin su tace, "Sannu Sis Manal, yau dai gashi min gan ki ido da ido, bikin ku duk waya muka gani." Manal tace, "gaskiya dai kam, ya sunan ki?."
"Sunana Fatima amma ana kirana da Baby." Manal ta buɗe ido tace, "sunan Mamana ne dake."
Baby tace, "kice na gyara zama gidan ƴata nazo." Manal tace, "ki yi abinda ki ke so Mamana."
Ɗayar da take zaune tace, "duk da baki tambaya ba sunana Aisha." Ƙaramar tace, "ni kuma Ayra." Aka yi dariya harda Maman su Manal tace, "your welcome Ayra, sunan ki mai daɗi."
"Bai kai naki ba Anty Manal."
Surayya ce ta fito da flaks ɗin abinci dana fan cake ɗim ta ajjiye musu suka gaisa, aka kawo ruwa da lemo da kofuna da kuma kayan marmari. Mama tace, "mu da zamu tafi ina mu ina cin abinci?." Maman su Surayya tace, "ai kam ko yaya ya kamata ku taɓa." Manal kallon Aisha take yi ganin tana yatsina kana ganin ta kaga mai iyayi tayi murmushi tace, "Aisha iyayin ki irin na Yayata." Aisha tayi dariya tace, "wai iyayi, don Allah da gaske? Tana ina?."
Manal tace, "Tana gida."
Buɗe ƙofar akayi ya saka Manal ta kalli wajan Bebi ya kalle ta yace, "ki zo ku gaisa da Daddy." Manal ta amsa ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi Ayra ta tashi tace, "ni zan ɗauki mai irin sunana na kaiwa Daddy." Maman su tace, "sai kin yar dashi?." Manal tayi dariya tace, "ƙyale ta Mama, daman sunan su iri ɗaya ita Ayra shi Ayan" Manal ta faɗa tana bata shi suka nufi falon Abban.
A zaune ta same su da Daddy da Huzaifa da wani ɗan saurayi da alama shima ƙanin Huzaifa ne a zaune sai Bebi da yake tsaye ya ajjiye musu abin sha. Ayra ta ƙarasa wajan Daddy tana cewa, "Daddy kaga Ayan mai kyau, kuma sunan mu iri ɗaya ne dashi, Anty Manal ɗin ma tana da kyau sosai" ta faɗa tana bawa Daddyn shi ya karɓa yana cewa, "Sarkin magana, aka baki jariri sai kun faɗi ke da shi?."
"Daddy gashi na kawo maka shi bai faɗi ba."
Manal ta zauna a ƙasa suka gaisa da Daddy ya yi mata barkar samun ƙaruwa tare da addu'a kafin yace, "ku yi haƙuri fa, ana ta saka rana zamu zo zamu zo Allah bai yi ba sai yau." Manal tayi murmushi tace, "daman komai sai Allah yayi." Daddy yace, "gaskiya ne." Manal tace, "hakan ma mun gode Allah ya ƙara girma." Daddy ya amsa da fara'a kafin ta miƙe tana cewa, "bara a kawo abinci."
Daddy yace, "A'a, ki barshi ba sai mun ci komai ba."
A lokacin Manal ɗago kai ta kalli fuskar sa a lokacin shima ya kalle ta sai tayi murmushi tace, "A'a Daddy, gwara dai ku ci ko ya yake, bara na kawo." Sak Daddy yayi ya kasa magana yana kallon ta fuskar har ta ɓace daga falon, gaban sa ne yake faɗuwa tunawa da wani abu da ya faru a shekarun baya, zuciyar sa lokaci ɗaya ta harba cikin tunanin da yazo kansa lokaci ɗaya. Suna zaune aka kawo abinci suka ɗan ci kaɗan kafin su gama yace a kita yaran suka fito gabaɗaya har Manal ɗin, Daddy ya bawa Manal kayan da aka kawowa Ayan da nata kayan har da kuɗi. Har bakin mota suka raka su suna godiya kafin su shiga mota su tafi gidan su Bebi.
Komawa ciki su Manal suka yi Mama tace, "to gashi sun ci, da kuna baza'a ayi girki ba. Ai in aka sanar da kai zuwan mutane da wuri ana nufin ayi musu tarba mai kyau." Manal ta zauna tana cin abincin tana cewa, "Wallahi kuwa Mama, ba dan ke ba da mun ji kunya." Surayya tace, "tun farko ai nace miki ayi kika ƙi." Manal tana cin abincin tace, "to ba gashi an yi ɗin ba, kin cika mitar tsiya." Surayya tayi dariya itama ta zuba abincin ta fara ci.
Su Daddy kai tsaye gidan su Bebi aka wuce dan a gaishe da Abba, suka faka motocin a harabar gidan Bebi yayi musu iso zuwa wajan Abba kai tsaye tunda ya san da zuwan nasu.
A falon Abban suka samu Mamy da Mummy a zaune suna magana da Abban, suka shiga da sallama. Abba yana kashingiɗe akan kujera, Mummy tana daga gefe ganin su sai tayi murmushi tace, "Sannun ku da zuwa, Yauwa Bebi yi sauri kazo jikin sa yayi zafi" ta faɗa tana kallon ew. Bebi ya ƙarasa kusa da Abba da sauri Abba ya tashi zaune yace, "Zazzaɓi ne kawai ba wani abun ba, ƙyale ni Adnan ga baƙi sun zo in mun gaisa sai ka duba ni ɗin."
Ganin Abban ya tashi si ya bashi waje suka ƙaraso aka zauna. Abba ya kalli Daddy tare da miƙa masa hannu yace, "Barka da zuwa mutanen Qatar, sai yau Allah yayi zamu gana, ana ta saka lokaci ana saɓun saɓani, sai yau da Allah ya nufa gani ga ka." Daddy ya kalli Abba da murmushi yana miƙa masa hannu alamun su yi musabaha.
"Kaiii!" Daddy ya faɗa yana zare glasses ɗin idon sa yana kallon kamar yadda Abban ma shi yake kallo da matuƙar mamaki a kwance a kan fuskar sa. Sun ƙamar da hannun basu gaisa ba kuma basu janye hannun ba sai kallon juna da suke yi cikin mamaki da kuma al'jabi. Abba ne ya miƙa hannun sa sosai suka gaisa ya ce, "wai idona ne suke gane min abinda nake gani ko kuwa gaskiya ne?, fuska nake gani kamar ta wanda taɓa sani a baya. Sai dai wannam fuskar cike take da girma da kuma farin gashi."
Daddy yayi dariya mai sauti wacce take nuni da tunanin sa ya zama gaskiya ya riƙe hannun Abba yana jijjigawa yace, "nima irin hakan nake gani, kar kace min Mu'azaam ne." Abba yayi murmushi ya ce, "Aliyu dollar." Jin sunan da ya faɗa Sai Daddy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Wallahi kai ne, wallahi wannna abokina ne Mu'azzam."
"Ali ashe rai zai sake ganin rai?."
"Gashi kuwa mai haɗawa ta haɗa mu. Mu'azzam daman kai ne mahaifin Adnan? Ikon Allah kuma ya aka yi ban yi saurin fahimta a kan fuskar Adnan ba?, Ko da yake shekaran da yawa, maganar shekara sama da ashirin ake yi."
Abba ya girgiza kai ya kalli iyalan Ali yace, "kowa ya tara iyalai ma sha Allah, amma babu wanda ya san wani, an rabu kamar ba a taɓa haɗuwa ba." A lokacin iyalan Daddy suka gaishe da Abba ya amsa da fara'a kafin ya kalli Huzaifa yace, "Huzaifa ashe daman wannan shine ya haife ka?, Ai na jima da sanin mahaifin ka shekaru da yawa da suka wuce, wani dalilin ne ya raba mu amma da na tabbatar har yanzu muna tare. Da yake Allah yayi dai yau zamu sai aka dinga samun saɓanin haɗuwar tamu."
Daddy yace, "bari kawai, kuma na neme ka daga baya, Allah dai bai yi za'a sake haɗuwa ba sai yanzu ta silar Adnan da Huzaifa." Abba yace, "Huzaifa shine yaron da na sani yana yaro?, shine wanda dai nake gani?."
"Shine wallahi, Allah ya raya min shi gashi har ya girma ya ajjiye iyali. Da yake kamannin sa gabaɗaya sun canja baza ka iya gane shi ba" ya kalli Manan su Huzaifa yace, "Mu'azzam ne fa abokina a Zaria, kin gane shi?."
Mama tayi murmushi tace, "na gane shi mana, ai ganewa ba ma ɗaya ba, ba shine wanda yake zuwa daga nan Kano ba ku ke barin garin tare?." Daddy ya girgiza kai alamun shine yana murmushi. Abba ya kalli Mamy kafin yayi magana tace, "na gane shi yanzu." Abba ya kalli Mama yace, "daman dake ne baku taɓa haɗuwa ba, amma ya taɓa ganin Adnan ne ko Farida na dai manta waye a cikin su. A'a Muhammad ne Yayan Adnan da ya rasu." Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba.
Daddy ya kalli Abba yace, "Alhaji Mu'azzam na iyayen kowa." Abba shi kaɗai yasan me sunan yake nuri hakan ya saka yace, "wannan suna ai ya zama tarihi." Suka yi dariya gabaɗayan su da alama dai sun ji daɗin sake ganin juna.
Abba ya kalli matan sa yace, "Hauwa ku je da baƙin su ci abinci dan tafiya ba yanzu ba sai dare." Daddy yace, "ko ma gobe ba, aje dai ayi hira dan munci abinci a gidan Adnan." Abba yayi murmushi ya girgiza kai duk suka fita aka bar Abba da Daddy kawai.