← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 84

Sashe 65

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wani nan, kema dangin mijin ce ai." Farida tace, "maganar gaskiya ko Manal ɗin ce aka zo yanzu bata haihu ba da muna nan muna cewa anya lafiya." Yayi dariya yace, "to dan an yiwa Mimi ashe babu laifi."Ita dai Manal tana zaune murmushi kawai take yadda suka mayar da ita tamkar ƴar gida yana yi mata daɗi sosai.

Kallon Manal yayi suka haɗa ido sai ta ɗauke kanta Farida na kallon sa tace, "wallahi baza ta bika ba, yau tana gidan nan har sai mun kai Maryam." Dariya yayi mai sauti yace, "in nace zamu tafi zaki hana ne?." Mama tayi dariya tace, "ka raina Farida wallahi, kuma har goya ka tayi." Da sauri ya kalli Mama yace, "Haba Mummy, kwata-kwata nawa take da zata goya ni?. To ko Maryam ai bata goya ni ba balle wannan." Farida tace, "duk bala'in ka dai ni Yayar ka ce." Baice komai ba ya fita daga falon yana dariya.

Abba dashi da Alhaji Magaji suna zaune yanayin fuskar Abba zaka kalla ka tabbatar yana cikin farin ciki saboda yadda yake murmushi yace, "ai da naji Sani ɗan kane nayi farin ciki sosai, ko babu komai na san inda Lubna zata shiga."

Alhaji Magaji yayi murmushi yace, "da yake bana ƙasat aka yi komai, sai bayan komai ya faru nake jin labari ashe Lubnan wajan ka ce." Abba yayi murmushi yace, "itace wallahi."
Alhaji Magaji yace, "Wai Lubna ba itace wacce aka yiwa fyaɗe ba?." Abba ya kalle shi yace, "eh itace."
"Shi Sanin ya sannan an yi mata fyaɗe ko kuma akuya kuka bashi da farar kura?." Abba yace, "ya sani mana, ai ba a bayar da aure a ɓoye ko?."

Alhaji Magaji yace, "kuma sai ya amince?." Abba bai bashi amsa ba ya bishi da kallo yace, "to maganar gaskiya ko shi ya amince ni bazan amince ya aure ta ba, saboda ni da kai kar ta san kar ne, babu abinda baka sani nawa ba babu abinda ban sani naka ba. Ba dan Allah ya kiyaye mu daga aikata luwaɗi ba da baka da abokin aikin ka sai ni. Dan haka auren Lubna da Sani ka mata dashi kawai, domin bazan iya bari ya aure ta ba."

Abba a firgice ya kalle shi yace, "me hakan yake nufi?."
"Alhaji Mu'azzam Sani bazai auri Lubna ba saboda bazan iya haɗa haɗa zuri'a da kai ba. Bazan iya kallon ka matsayin siriki ba, haka ƴar ka bazan taɓa kallon ta matsayin sirika ba, sannan baza ta iya samun kwanciyar hankali a gidan ɗana ba. Gwara a ƙyale ta in wanda yayi mata fyaɗen ya dawo da niyar auren ta sai ya aure ta kawai a rufawa juna asiri, amma gaskiya ni bazan bawa Sani ita ba."

Abba ya kasa magana sai kallo Alhaji Magaji da yake yi ya kasa cewa komai. Alhaji Magaji yace, "Yayar matar Adnan kuma ƴar abokin ka Mubeena ka neme ta, ita kanta matat Adnan ɗin itace yarinyar da na kawo maka nace itace daidai kai ka tuna?, ka tuna yarinyar da muka yi amfani da rashin lafiyar babar ta da dan mu same ta?." Abba ya wara ido waje ƙirjin sa yana up and down Alhaji magani yace, "eh itace, nasan babu lallai ka gane ta saboda matan sun yi maka yawa. To itace, itace yarinyar da ta gudu a lokacin baka yi mata komai ba, kai baka ganr ta ba amma na san ita ta gane ka. Da irin wannan mummunar ɗabi'ar zan haɗa zuri'a da kai?. Inaa...!kawai a cigaba da zama a abokai aamma babu zancen zama sirikai ni da kai."

Kallon Abba yayi yaga ya kasa magana yace, "dole ka kasa magana ai, daman abinda nazo na faɗa maka kenan wannan aure bazai yu ba, Allah ya bata wani dan wannan baikon an soke shi" ya faɗa yana miƙewa tsaye ya fito harabar gidan.

BDƘB3P40

       A can falon Mamy kuwa Maryam ce da angon ta a zaune fuskar sa a ɗaure sosai ita kuma gaban ta sqi faɗuwa yake yi saboda yanayin da ta ganshi a ciki ya bata tsoro. Maryam tace, "kace min zaka zo gida mu yi magana kazo kuma baka ce komai ba." Mahmud ya kalle ta yace, "Meyasa kika ɓoye min kin yi ciki shege na tsohon mijin ki?."

Gaban Maryam ya faɗi ta kalle shi tace, "a ina kaji wannan maganar?."
"Saboda kina tunanin ba zan sani ba kika ɓoye min? Ashe ke ƴar iska ce mai bin tsohon miji?."
Maryam ta yi Shiru ta sauke kai ƙasa tace, "ba yadda ka ke tunani bane wallahi, blackmailing ɗina yayi."  yayi tsaki yace, "koma meye da haɗin kan ki aka yi, iskanci sunan sa iskanci ko mai ƙarancin sa. Kin cuce ni wallahi, kin  cuce ni da har aurena ya hau kan ki. Ban san da cewa ke ɗin karuwa bace ba sai yanzu, ban san da cewa baki da daraja ta mace ba sai yanzu. Nayi dana sanin auren ki, nayi dana sanin haɗa jikina dake."

Bebi ne ya shigo falon da sallama da niyar su gaisa da Mamy ganin Mayam da mijin ta sai yayi murmushi ya ƙaraso ya miƙa masa hannu alamun su gaisa  yace, "A'a Mahmud, barka da wannan lokaci Ango, ba dai kazo ɗauke matar ka ba."
Musabaha suka yi ya kalli Maryam da take kuka ya kalle shi kamar zai magana sai yaga ba hurumin sa bane. Ya juya da niyar fita Mahmud yace, "na saki maryam saki biyu, na sake ta saki ɗaya, saki uku kenan. Aurena da aka ɗaura da ita ranar juma'a na warware shi a yanzu."

Gaban Bebi ya faɗi sosai ya juyo da sauri yana kallon sa Mahmud yace, "eh na sake ta, bazan iya zama da karuwa wacce tayi ciki tare da tsoron mijin ta ba, zan nemana yarana uwa ta gari ba irin ta ba. Shiyasa na sake ta a gaban ka domin ka zaka shaida, ni ba irin mijin da zai aure ta bane, domin ko na aure ta baza ta fasa bin tsohon mijin ta ba, dan haka taje ta cigaba da mu'alama da mijin ta ni na sake ta saki uku!."

Bebi kallon sa yake yi rai a ɓace matuƙa zai yi magana Mahmud ya miƙe tsaye yace, "ba sai nace komai ba, har labarin yadda ka hanata sauraren sa naji, amma da yake bata da hankali bata mutunci bata san mutunci ba, da yake ta saka neman maza a gaba..." Bebi ban san ya ɗauke shi da mari ba sai hannun sa da ya gani ya chakume wuyan sa yace, "ka sake ta kece ko? To ka fita ka bani waje kar na sake jin wata magana mara daɗi a kanta, in kuma ba haka ba wallahi sai na fasa maka baki."

Mahmud yace, "kut ni ka mara Adnan?." Bebi yace, "na mare ka, in kana ganin zaka rama gani gaka, kuma in ka sake faɗar wata magana a kanta wallahi sai na cire maka haƙori." Sakin sa Bebi yayi Mahmud yayi hanyar fita yace, "ko me zaka yi dai kayi, ni ba zan zauna da karuwa ba mai neman tsohon mijin ta." Da zafin nama ya biyo bayan sa lokacin yaje harabar gidan ya riƙe kwalar sa ya sake tsinke shi da mari. Mahmud shima bai ƙyale shi ba ya kai masa duka ya same shi a gefen fuskar sa.

A lokacin Alhaji Magaji yana niyar shiga mota yaga abinda yake faruwa, kafin kace wani abu duk mutanen gidan sun fito har Abba ya fito wajan ana riƙe Bebi.  Mahmud ya kalle shi yace, "in ka sake ɗaga hannu ka taɓa jikina  zaka yi dana sani Adnan." Bebi ya tankaɗa shi ya nuna amsa gaye yace, "fita ka bani waje, kar na sake ganin fuskar ka har abada."

"Bazan fita ba, gwara da kowa ya fito ku shaida na saki Maryam saki uku, domin bazan zauna da karuwa wacce ta gama lalacewa da tsoron mijin ta ba, nj ba lusarin namiji bane domin uwa ta gari nake son nemana yarana, matata da ta rasu ta kirki ce bazan ɗauko ta banza na kai gidana ba. Na sake ta na sake maimaitawa kowa yana ji, bazan iya haɗa zuri'a da mutanen gidan nan ba domin dukkan ku a lalace ku ke. Hakan kuma ya samo asali ne daga shi shugaban gidan, duk a wajan sa kuka yi gado."

Bebi ya zabura zai yi wajan sa Alhaji Magaji ya riƙe shi yace, "ƙyale shi Adnan, ai gaskiya yake faɗa ba ƙarya yayi ba, kuma an rufe shi da tun farko sai a faɗa masa wacece wacce za'a wanke a kai masa da duk hakan bata faru ba. Nima yanzu na waraware baikon da aka yiwa Sani da Lubna, domin ba zai auri wacce aka lalata ba, kuma bazai iya haɗa zuri'a da mahaifin ku ba."

Bebi kallon sa yake yi da matuƙar mamaki kafin yace wani abu Alhaji Magaji yace, "kai Mahmud ka hau motar ka kayi tafiyar ka, dan ka sake ta ai ba komai bane nima na warware baikon ƴar sa da ɗa na" ya faɗa yana ƙarasawa ya shiga mota Shima Mahmud ya shiga motar sa suka fita daga gidan.

"Abbaaaaa!" Mimi ta faɗa da ƙarfin hakan ya saka suka juya suka ga Abba a kwance a wajan a sume.
Hankalin mutanen gidan ya tashi da taimakon mai gadi a saka Abba a mota Bebi ya ja motar da ƙarfi ya fita zuwa asibiti hankalin sa a tashe sosai.

Taimakon na musamman aka bawa Abba sai dai an tabbatar da jinin sa ya hau sosai har lokacin kuma baya hankalin sa. An samu ya farfaɗo daga suman da yayi a lokaci. Amma bai buɗe ido ba ba kuma ba’a tunanin zai buɗe ido a kurkusa.

Hankalin iyalan gidan ya kai ƙarshe wajan tashi, ga fasa auren Lubna da akayi ga sakin da aka yiwa Maryam gabaɗaya hankalin su baya jikin su duk sun ruɗe gabaɗayan su. Haka suka kwana a wannan a cikin ruɗani washe gari da safe asibitin ya cika da iyalan gidan amma Abba bai farka ba a haka aka kwash kwana uku.
Chapter 65 · 0% Book details