← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 84

Sashe 14

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nima ina kewar ki Partner, ban ƙi na tafi dake yanzu ba, da bazan barki bacci ba sai na tabbatar kin samu abinda kike so fiye da yadda kika so a zuciyar ki." Ta ɗago kai ta kalle shi tace, "me nake so ɗin?."
"Au baki sani ba?." Ta ɗaga gira yayi dariya kaɗan ya matso da bakin sa kusa da kunnen ta ya mata magana a tare da cizon kunnen nata. Da sauri ta mayar da kanta jikin sa tace, "Allah ni ban ce ina so ba, kar kayi min sharrii."

"Ko baki faɗa ba idanun ki sun nuna haka, kar ki damu dole na samo miki mafita." Manal kamar zata yi kuka tace, "Allah ban ce ina so ba." Cikin nishaɗin da yake ji a zuciyar sa yace, "ni nasan kin ce." Ta yi masa dukan wasa a ƙirjin sa tace, "Allah ban ce ba."
"To laifi ne in kin ce ɗin Manal? In ke kina ganin laifi ne to ni ina buƙatar hakan Manal. Wallahi ina buƙatar ki a kusa dani sosai."

Hannun sa taji a kan cikin ta yana shafawa a hankali hakan ya saka ta lumshe idanu, ɗago fuskar ta yayi yana kallon ta fuskar yana ƙoƙarin kai bakin sa kusa da nata. Baya tayi da sauri tace, "Yaya zata iya shigowa." Ya girgiza kai yace, "baza ta zo ba" ya faɗa yana dawo da ita kusa dashi ya fara kissing ɗin ta a hankali itama tana taya shi.

Kusan mintina biyu suna a haka kafin ya janye bakin sa saboda kar ya canja mata yanayi daman abinda take so kenan kar ya zama ya tsokano ta. Goshin su ya haɗe waje guda hancin su na gugar juna, idanun ta a lumshe tana sauke numfashi a hankali. A hankali ta buɗe idon suka haɗa ido sai ya ɗaga mata gira tayi dariya ta rufe fuskar ta da hannun ta, murmushi yayi mai sauti yace, "Manal zaki bi ni muje gida mu dawo?."

Da sauri ta kalle shi ta janye fuskar ta yanayin ta ya canja tace, "Mama!."
"Baza ta sani ba. Partner kina buƙatar mijin ki nima ina buƙatar ki, rashin ki yana cutar dani kema rashi na yana cutar dake yana cutar da abinda yake cikin ki. Please Manal ki yarda mu tafiya bazan bar hanyar da Mama zata gane ba, I really missed you, ki taimake ni ki taimaki kanki da babyn mu."

Haɗa ido suka kuma yi da ita yace, "please Manal!." Ta sauke numfashi Allah ya sani tana son bin mijin ta amma baza ta iya yiwa Mama haka ba, ta kulle ido ta buɗe cikin sanyin jiki tace, "Yaya Mubeena tana nan me zance mata?."
"Zata fahimta, kar ki damu da Yaya Mubeena zata fahimce mu."

Manal tayi shiru tana ji yana cigaba da shafa jikin ta a hankali amma bata ce komai ba.
"Muje?." Maganar sa ta katse mata tunani ta kalle shi tace, "ina so naje amma kuma bazan iya yiwa Mama haka ba" ta faɗa hawaye yana sakko mata.

Numfashi ya sauke dan bashi da ta cewa tunda tace Mama bazai tilasta mata. Zare hannun sa yayi daga cikin rigar ta ya girgiza kai yana kallon ta yace, "shikenan, kin tabbatar hakan bazai cutar dake ba?." Ta kalli idon sa tana kuka tace, "uhum!." Ya sauke numfashi yace, "is okay, ki daina kuka."

"Kai fa?." Kallon ta yayi yace, "kar ki damu dani."
"Dole na damu da kai." Ya kawar da kai gefe yana shafa fuskar sa kafin yace, "yanzu in ku ka koma gida gobe shikenan bazan sake ganin ki ba?" Ya faɗa yana kawar da waccan maganar dan bayan son abinda zai tayar masa da hankali.

Ta fahimci hakan sai taji babu daɗi a zuciyar ta, Allah ya sani tana son abinda yake so ya wakana a tsakanin su, wataƙila ma ta fishi so ɗin amma ya zata yi?. Ganin tana kallon sa ta kasa magana yace, "Zan tafi" ya faɗa yana kallon agogon hannun sa.

Manal ta kalli agogon itama tace, "dare yayi sosai, ka kwana a nan." Ya kalle ta yace, "in na kwana zan samu abinda nake so ne a wajan ki?." Ta sunkuyar da kai yace, "hmm! gwara na tafi" ya faɗa yana tashi tsaye ta riƙon hannun sa tace, "fushi kayi?" Ta faɗa ido na sake cikowa da hawaye.

"Ba fushi nayi ba, dare yayi na bar Yaya a waje gwara na tafi."
"Allah fushi kayi, Gashi ka canja har fuskar ka ma ta canja" ta faɗa tama fashewa da kuka. Ya san daman tana da yawan kuka, amma samun cikin ta ya sake ƙara mata rigima da neman faɗa sosai, hakan ya saka shi ya koma ya zauna yace, "ba fushi nayi ba, akan me zanyi fushi ma?."

"Gashi nan ka canja" ta faɗa murya ba rawa sosai. Ya goge mata hawaye yace, "ni ban yi fushi ba, ke kin san in fushi nayi bazan kula ki ba tafiyata zan yi, tunda kika ga ina nan ban tafi ba ki yarda ban yi fushi ba kin ji partner?."

Ta girgiza kai ta kalle shi tace, "bana so ka tafi ka barni."
"Nima bana so na tafi ɗin, amma dole na tafi saboda na bawa Mubeena dama ta kwanta tayi bacci. Inda asibitin mu ne sai na canja mana room mu bata nata mu kwana tare, amma kin ga nan ban taɓa zuwa ba sai ta dalilin ki."

Manal tace, "haka ne."
"To ba fushi nayi ba ki yarda, sannan ki saka a zuciyar ki komai ya zo ƙarshe." Ta ɗaga kai alamun to ya sake tashi tsaye yace, "zan tafi." Sakkowa tayi daga kan gadon ta tsaya a tsaye tana kallon sa, kamar zatayi magana sai ta fasa ta sake shiga jikin sa ta rungume shi.

Dole ya riƙe ta ya sake matso da ita jikin sa sosai kirjin su ya haɗe waje ɗaya tace, "ina sonka partner."
"ina son ki sosai partner, Allah ya baki lafiya ya fito mana da babyn mu lafiya" ya faɗa yana ɗago ta ya manna mata kiss a goshi.

Itama a kumatu ta yi masa kiss tace, "Amin, Allah ya kiyaye hanya."
"Amin milky." Tayi murmushi shima yayi ya ɗauki wayar sa da ya ajjiye a gefe ta riƙe hannun sa suna tafiya har bakin ƙofa sannan ta tsaya tace, "in ka je ka kira ni."
"Okay ma'am" ya faɗa da girmamawa tayi dariya shima yayi kafin ya fita.

A zaune ya tarar da Mubeena a ƙofar ɗakin tana waya tana cewa, "kee bari kawai, ai Manal da mijin nan nata kan su rawa yake, soyayya suke ji da ita shiyasa na fito nan na bar musu ɗakin. Ke kuwa yayar ta ce ni fa" ta faɗa tana dariya sosai.

Bebi ya murmusa yana kallon ta daga gefen fuskar ta, tana yi masa kama sosai da wacce ya sani amma ya rasa wacece, amma tabbas ya san mai irin fuskar ta har maganar su kusan iri ɗaya. Ƙarasowa yayi yace, "Yaya Mubeena." Sai da ta firgita ta kalle shi tace, "Yaya kuma?."
"Eh, ba yayar bace?."
"Yayar Manal ba, amma ban da kai ban girme ka ba."

"Tunda ta Manal ce nima tawa ce." Mubeena ta girgiza kai tace, "da sake."
"Sai da safe, a kular min da ita don Allah. Anytime in akwai abinda ake so take so just call me please."

Mubeena tace, "in sha Allah." Ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata yace, "ki riƙe ko za'a nemi wani abu." Ta kalli kuɗin tace, "ka barshi kawai, ai gobe zamu bar nan."
"Ki karɓa." Ta karɓa kuwa yace, "goben in an yi discharging ɗin ku zan zo na kai ku gida."
"Allah ya kaimu" ya amsa da amin ya juya ya fita da sauri.

Da kallo ta bishi a bayyane tace, "Manal tayi sa'ar miji mai son ta, Allah yasa bai ɗauko halin bunsuraye irin na mahaifin sa ba, har tausayi yake bani in na tuna waye mahaifin sa" ta faɗa tana sauke numfashi a ranta tana ayyana da Mama zata ji labarin abinda mahaifin sa yayi mata da ko tana niyar mayar masa da Manal wallahi baza tayi ba shiyasa tayi shiru ta manta da batun.
Da wannan tunanin ta koma ciki ta tarar da Manal a zaune tana goge idanu, bata ce mata komai ba ta warware ƙaramin bargon ta ta shinfiɗa ta kwanta a ƙasa.

Washe gari kamar yadda yace ta kira shi bayan an sallame su ƙarfe takwas na safe ya shigo asibitin Mubeena ta gaishe shi ya amsa yana yi mata ya bangajiya, ya kalli Manal kafin tayi magana tace, "ina kwana."
"Kin tashi lafiya madam? Ya jikin?." Mubeena tace, "ina ta kwana ma balle ta tashi lafiya? Kwana tayi tana share hawaye cikin shegiyar shagwaɓar da take ji da ita, ayi mata magana ta fara harare harare. Baccin da ta samu ƙalilan ne, kuma na faɗa mata harda rashin bacci a matsalar ta amma taƙi ji."

Ya kalli Mubeena ganin tana hararar Manal ɗin ycae, "ayi haƙuri Yaya, yanayi ne ya kawo hakan." Kallon sa take yi, itafa haushi take ji in yana cewa yayar nan, bai san da ta amince da uban sa da yanzu Mama zai ce mata ba. Kallon Manal yayi yace, "bakya jin magana ko?."

Kallon sa ita dai kawai take yi yayi kyau cikin yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu hula, ganin tana kallon sa sai ya dungure mata kai yace, "Nawa zaki biya na kwalliyar?." Dariya tayi shima yayi murmushi yace, "tashi mu je." Riƙe ta yayi ta tashi tsaye a lokacin Mubeene ta fita daga ɗakin, tana jin rufewar ƙofar ta shiga jikin sa da hanzari ta kwanta tace, "kayi kyau partner, Allah ya isa duk wacce ta kallar min kai a tahowar ka, in kai kuma ka Allah akwai Allah."
Chapter 14 · 0% Book details