← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 84

Sashe 16

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zaune a falo da alama sun ji komai a yanayin jikin su da taga yayi sanyi ta gane hakan, ta kalle su bayan ta zauna  tace, "zan faɗa muku asalin waccee ni da mahaifin ku." Ta kalle su ta fara basu labari kamar yadda Abba ya bawa su Adnan labari kafin dalla-dalla kafin tace, "A zamana da mahaifin ku da farko zamana ne na farin ciki, zama ne wanda naji daɗin sa nake murna addu'a mahaifiyata ta karɓu da take yawan cewa Allah kar ya kai ni inda zan wulaƙanta. Duk da yarinya ce ni a lokacin amma na san jin daɗin aure, yana bani lokacin sa sosai yana kuma biye min ya mayar da kansa mai shekaru irin nawa. Sai bayan na haifi Manal na fahimci me mahaifin ku yake nufi dani, kuɗin da na gada na mahaifina da mahaifiyata shine silar karɓar aurena da yayi a wajan ƴan uwana da basa ƙaunata, da ya gama tattara dukiyar ya tafi ya barni ba tare da yayi tunanin ban san kowa ba sai shi."

"Haka na fara rayuwa ni kaɗai sai ku sai matar da nake zaune a gida ɗaya da iya, bani komai ya kwashe ban iya komai ba saboda na tashi da gata ban iya wani abu na sana'a ba balle na fara. Ina zaune ni kaɗai a Zaria aka zo aka kore ni akace kuɗin haya ya ƙare, na koma zaman titi kamar almajira. Rana ta fito ta koma a kaina nida ku, ruwan sama yazo ya dake ni amma ƙoƙari nake na ɓoye ku musamman Manal da ta kasance ƙarama kar ta cutu. A wannan yanayin na kasance har kwana biyar a lokacin Allah ya kawo min baban ku, da yake a lokacin baya taimako bai yi ƙaranci kamar yanzu ba ya kai ni asibiti saboda ciwon da nake yi nida ke Manal, aka mana magani daga nan yace ya tambaye ni inda zanje nace masa bani da kowa, na bashi labarina ya tausaya min sosai sai yace zai kaini Kano wajan mahaifiyar sa, na amince saboda bani da zaɓi a wannan lokacin, in na ƙi ina zan je? Wa nake dashi da zai sake kawo min ɗauki? Wannan dalilin ya saka na amince muka taho Kano."

Mama ta sauke numfashi tace, "mahaifiyar sa ta riƙe ni tamkar wacce ta haifa tana rainon ku kamar jikokin ta, tare da take haɗa ku da ƴaƴan Baban ku tayi muku ko mai tare har kuka fara tasawa. Daga nan ta bashi shawarar aurena bai musa ba ya amince ya aure ni matsayin matar sa ta uku ya cigaba da riƙe ku matsayin ƴaƴan sa."

"Duk wani abu da ya shafi mahaifin ku da abokin sa da kuma ƴan uwana bana so, ko kusa bana so ayi min maganar shiyasa ban taɓa faɗa muku ba, Shima kuma na roƙe shi nace don Allah kar ya faɗa muku yace bazai faɗa ba. Wannan dalilin ya saka da naga Mu'azzam duk da ya girma amma na iya shaida shi saboda ba'a mantawa da alkhairi haka sharri ma ba'a manta shi. A gani na sune suka raba ni da farin cikina, da ace sun barni a gidan mu na tabbatar ƴan uwana dole zasu haƙura da ƙiyayyar da suke min su zauna dani saboda ni jinin su ce, duk da na kasnace ƴar ƙwarƙwara amma mahaifina ya mayar da mahaifiyata matar aure, kuma koda ace ni ƴar ƙwarƙwarar ce dole ace ni ƴar Muhammad Jalingo ce ko basa so. Suka raba ni da garin mu suka kai ni inda ban taɓa zuwa ba kuma suka barni, shiyasa nace kizo mu tafi saboda tuna hakan ya saka naji bazan iya haɗa alaƙa da Mu'azzam ba."

Manal da Mubeena dai kuka suke yi sosai jin labarin mahaifiyar su da irin wahalar da ta sha kamar ba ƴar babban attajirin da har yanzu sunan sa bai ɓace daga doron duniya ba. Mama tace, "Tunda kina son Adnan bazan raba ku ba Manal, kamar yadda Baban ku yace na bar ki da abinda ki ke so zan yi, ki koma Manal har zuciyata na amince da ki koma gidan sa."

Ta girgiza kai tana kuka tace, "Mama ashe haka kika sha wahala? Meyasa ƴan uwana ki basa son ki? Meyasa suka wulaƙanta ki?." Mama tayi murmushi tace, "A baya ban fahimci dalili na saboda ƙuruciya, amma da girma ya cimmin na gane dalilin hakan. Allah ya ɗorawa mahaifina son mahaifiyata fiye matan sa na aure, Allah ya yiwa mahaifiyata baiwar kyau wanda ake kira da kyau, duk kyauna da ake gani da kyaun Mubeena bamu ɗauko rabi da kwata a cikin kyaun da take dashi ba. Gabaɗaya hasken ta kika ɗauko Manal, haka tajr fara kamar tana shafa madara, inda da ace har kyaun gabaɗaya nata kika ɗauko da ban san wanne irin kyau zaki ba Manal."

Mubeena tana kuka tace, "kuma basu sake neman inda kike ba? Basu sake waiwaiyar ki ba kema baki neme su ba?." Mama tace, "har abada wallahi bazan neme su ba, kuma kar wacce tace zata neme su yadda suka barni nima na barsu, yadda suka aurar dani ga wanda basu san shi ba suka bar ni a wajan sa aboda basu damu dani ba shikenan aje a haka kawai. Mu haɗu a lahira a lokacin da Allah zai tambaye su haƙƙina."

Mubeena tace, "Mama to ina dangin Maman ki?."Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "Ban sani ba Mubeena, a lokacin baya da yawan wanda suke zama ƙwarƙwarori bayi ne, wataƙila Mamana tazo a baiwa ne har aka bawa mahaifina ita a matsayin baiwar sa. Mamana ta taɓa cemin dangin ta sun rasu kuma asalin ta ba ƴar nigeria bace, wannan dalilin ya saka na saka a zuciyata mahaifiyata bata da dangi."

Mubeena tace, "mahaifin mu bai...." Kallon da tayi mata ya saka ta yin shiru tace, "kul kar na sake jin maganar mahaifin ku a bakin ki, dan na yafewa Mu'azzam har na barwa ɗan sa Manal ba hakan yana nufin na manta da abokin sa bane, Shima Mu'azzam ɗin in wani ne ba Adnan ba wallahi bazan bashi Manal ba. Kar ki sake maganar mahaifin ku, ko yana da rai ko bashi da rai wannan bai dame ki ba, ya neme ni bai neme ki ba babu ruwan ki, tunda ya kwashe dukiya ta wacce daman ita ta kawo shi ya tafi ya barni daku na shafe babin tarihin sa a duniya. Kwanciyar hankalin sa ya zama ya bar duniya, in ma yana duniyar kar ya zama yana tunanin inda nake ko kuma inda ku ke, domin shine kawai kwanciyar hankalin sa."

Mubeena tace, "ki yi haƙuri."
"Cikin dukiyata da suka kwashe abu biyu ne ya rage basu ɗauka ba, wata babbar gona da na gada a can Jalingo da kuma wani shago na kasuwa wanda aka siyar dashi baban ku yake juya kuɗin. Gonar kuma ita aka siyar da rabi aka yiwa Manal dake kayan ɗaki."

Manal dai kuka take ta matso kusa da Mama ta riƙe ta tace, "Mama ki yi haƙuri" Mama ta riƙe ta itama tace, "baki min komai ba Manal, ni zan baki haƙuri da nake ƙoƙarin katse miki farin ciki."
"Wallahi Mama zan iya yin komai a kan ki ciki harda rabuwa da Adnan."
"Baza ki rabu dashi ba Manal, na amince da zaman ki dashi komai ya wuce kar ki masa zancen mahaifin sa domin mahaifi mahaifi ne, duk lalacewar sa shine ya a haife shi."

Mubeena ma ta ƙarasa kusa da Maman tana kuka tace, "abubuwa dana aikata a baya Mama ki yafe min." Mama tayi dariya tace, "Mubeena kar ki damu komai ai ya wuce, na yafe miki na kuma tabbatar da kin yi hankali tun ba yanzu ba. Allah yayi muku albarka ya baki miji na gari, ke kuma da Allah ya baki na garin Allah yasa kar yayi halin mahaifin sa sannan kuma ya baku zaman lafiya har abada."

Manal ta amsa da amin suka rungume Maman suna kuka, Mama tayi murmushi tace, "komai ya wuce, ku ne farin cikina a duniyar nan, burina na saka ku farin ciki ko yaushe a kuma ko ina. Ku jikokin Muhammad Jalingo ne, kuna da asali ba a bola aka haife ku ba."

Ɗago su tayi daga jikin ta kalle su ta riƙe fuskar su tace, "yadda ku ke da kyawawan fuskoki ina so zuciyar ku ta kassance fiye da haka, don Allah kar ku ɗauko munin halin mahaifin ku, ku kasnace masu zumunci a ko yaushe, ku ƙaunaci junan ku, baku da kowa sai ni kawai, ni kuma na girma zaku iya rasa ni a ko wanne lokaci, da zarar ƙasa ta kulle idona baku da wani wanda zamu kalla matsayin dangin ku sai junan ku. Duk da nasan Baba kamar mahaifi ne a wajan ku yaran sa kamar ƴan uwan ku suke amma ba jini ɗaya ku ke ba, in kuka riƙe kan ku kuka mayar da Balaraba uwa, kuka mayar da Baban ku uban shikenan zaku zauna lafiya koda bani da rai."

"Balaraba tayi min komai a rayuwa, lokacin da Baban ku ya aure ni bashi da wani hali sosai, itace take kawo min abinci a ko yaushe bata taɓa gajiya ba kuma bata taɓa yi min gori ba. Balaraba ƴar uwata nake kallon ta wallahi, a yanzu in akace na nuna dangina itace ta farko wacce zan nuna saboda ta zama kamar jinina duk abinda yake damuna ita nake faɗawa. Ban amince ku nemo ahlin jalingo ba, ban amince ku ce musu ku jinina bane. Haka zalika ko da zaku ga mahaifin ku kuma kun tabbatar shine ban amince ku nuna masa kan ku ba, yadda aka bar ku kuma ku bar su."

Mubeena ta riƙe Mama sosai tana kuka tace, "in sha Allah Mama, baza ki tafi ma ki bar mu ba." Ta riƙe su  a jikin ta sosai tana kukan farin ciki suka kuma haka. Ƙaunar ƴaƴan ta take ji tana shiga ko ina na jikin ta, soyayyar su ta gama mamaye mata zuciya da gangar jikin ta, bata jin kowa a ranta sai ƴaƴan ta kawai.
Chapter 16 · 0% Book details