← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 84

Sashe 4

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kansa babban tashin hankalin sa kenan, wannan tunanin yana daga cikin abinda yake ɗaga masa hankali yaji zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri. In akace Manal ƙanwar sace ya zanyi? Ina zai saka ransa yaji daɗi?, Da wanne ido zai kalle ta!?. A wanne matsayi ɗan cikin ta yake?, ɗan sa ko kuma ɗan kanwar sa...?. Fita yayi daga ɗakin ya koma ɓangaren Abba ya shiga da sallama ya samu Abban a zaune yayi shiru alamun tunani yake yi, ya dauƙi wayar sa baice komai ba ya fita daga falon.

Gidan sa ya wuce ya shiga falon ya tarar dashi kamar ko yaushe a share sai ƙhamshi air freshener yake. Zama yayi a falon ya dafe kai da hannun sa biyu ya rasa inda zai saka zuciyar sa yaji daɗi. Wayar ya jawo ya shiga sunan Manal ya kira amma bata ɗauka ba, ya sake kira bata ɗauka ba ya riƙe wayar a hannun sa ba tare da ya kuma kira ba yana ji zuciyar sa na harbawa sosai.

Kiran ta ne  ya shigo wayar hannu yana rawa ya ɗauka bai jira tayi magana ba yace, "Ina cikin damuwa Manal, ina buƙatar ki a kusa dani, zuciyata gab take da daina aiki saboda abubuwa sun yi min yawa. A wajan ki zan samu sassauci gashi yanzu kin yi nisa dani, ban san me na yiwa Mama ta yanke wannan hukuncin ba, na lura ba laifina bane laifin Abba ne ya shafe ni, abin tambayar a nan me ya faru Manal?. Tsoro na da tashin hankalina kar ace ni da ke jini ɗaya ne, kar ace ni dake yaya da ƙanwa ne.
Bana so hakan ta kasance ko a mafarki, ban san ya zanyi da raina ba in hakan ya faru." Kuka Manal take a banɗakin da ta shiga don bata so Mama taji tana waya murya a ƙasa tace, "Hakan bazai tabbata ba in sha Allah, in hakan ya faru mutuwa zanyi."

"Baza ki mutu ba Manal, baza ki mutu ba, in mutuwar ne ni zan mutu ba ke ba, saboda zuciyata tafi taki yin nauyi Manal. Ina cikin tashin hankali, na dawo gida bakya nan duniyar tayi min zafi Manal. Kece maganin damuwa ta amma kin yi min nisa."

Manal kuka take yi sosai ya rantse ido yace, "ki daina kuka, jin kukan ki sabon tashin hankali ne a wajena. Ki yi mana addu'a Allah kar ya kawo rabuwar mu nan kusa, Allah yasa mutuwa ce zata raba mu dake ba wani dalili ba." Numfashi yaji ta sauke a hankali yace, "ki kula da kan ki, kar ki dinga shan sugar kin ji?." Kukan ta ke yi sosai kafin ya sake magana ta yanke wayar ya kulle ido yana ji kamar yayi kukan shima.

Manal sai da ta sha kukan ta a banɗaki sannan ta fito, ta dawo falon ta zauna tana jan numfashi na wacce tayi kuka ta ƙoshi. Mama tana kallon ta duk da dare yayi ba gani take sosai ba amma tana lura da duk wani motsin ta. Mama tace, "haka zaki kwanta baki ci komai ba?." Manal murya na rawa tace, "na ƙoshi." Mama tace, "kin huta, yunwa ba ƙanwar uwa bace balle taji tausayin ki."

Kwanciya tayi a gefen Mama ta kalli Mubeena da take zaune ta kulle ido kamar mai bacci amma ba baccin yake ji ba. A haka ta kwana babu baccin kirki sai ruwan hawaye, ga yunwa da ta addabe ta gabaɗaya ta kasa samun baccin kirki da ta fara baccin zata farka tayi kuka ta koma. Sai da tayi sallar asuba sannan ta samu tayi bacci shima zuwa tara na safe ta tashi.

Sai da tayi wanka a banɗakin Mama tayi sallar walha sannan ta fito tsakar gidan ta samu Mama ce kawai a zaune a inda ta saba zama da safe tana shan tea da biredin alkamar ta a gefe. Tsayawa tayi daga inda take tsaye Mama ta kalle ta tace, "ki ƙaraso kici abinci." Manal ta ƙarasa ta zauna kusa da ita Mama ta kalle ta tace, "wannan damuwar da wannan rashin cin abincin ba kowa zai cuta ba sai ke, aure ne babu shi a tsakanin ki dashi in zaki sake ki dawo kamar da yafi miki."

Manal ta jawo flask tea ta zuba a kofin da Maman ta gama sha ta kai bakin ta sai dai salam babu komai a ciki sai lipton da kayan ƙhamshi. Riƙe take da kofin bata ce komai ba kuma bata sha ba sai kallon wani waje da daban da take yi. Sallamar Maman su Surayya ce ta saka ta kalli mai shigowa Mama ta amsa sallamar da fara'a ta ƙaraso ta zauna suka gaisa Manal ma ta gaishe ta ta amsa kafin ta kalli Mama tace, "Lafiya dai ko Maman Manal? Surayya tace min a gida Manal ta kwana, ina fatan lafiya dai."

Mama ta kalli Manal da take juya cokali a cikin shayi tace, "Eh to lafiya amma lau ba, auren ta da Adnan ne ya ƙare."

Manal ta kalli Mama da take kallon Maman su Surayya ta kulle ido da buɗe taji Maman Surayya na cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raj'iun, Maman Manal me yayi zafi haka? Yaushe akayi auren Manal ɗin da za'a ce auren ya ƙare?."

Mama ta sauke numfashi tace, "Zan fahimtar dake in lokacin hakan yayi, Amma a yanzu ki ɗauka Manal bata da aure Balaraba." Jin hakan sai Maman su Surraya tace, "to Allah ya shiga lamarin." Mama ta amsa da amin suka ɗan yi hira kafin tayi sallama ta fita. Tana fita Manal ta tashi zata shiga ɗaki Mama tace, "har kin gama cin abincin?." Manal tace, "na kasa ci, kwanciya nake so nayi" ta faɗa tana shiga da sauri dan kukan da yazo mata baza ta iya riƙe shi ba.

*******
Mubeena suna zaune da Bilkisu a falo suna tattaunawa, Mubeena ta kalli Bily tace, "Bily ina cikin tashin hankali, na rasa abinda yake min daɗi na kuma rasa abinda yake shirin faruwa a cikin rayuwa ta." Bily tace, "nima tunda kika min waya hankalina yake a tashe wallahi, me ya faru?."

Mubeena tace, "jiya na raka Mama asibiti duba Yayar mijin Manal, da muka shiga Mama suka gaisa da da Maman su Adnan ɗin da fara'a da komai, har Maman su Adnan ta bawa Mama wajan da take zaune fa, aka gaisa da mutunci da girmama juna. Amma tana ganin mahaifin sa nan da nan sai yanayin ta ya canja, ta koma wani iri tana yi masa kallon so take ta gane shi, yana faɗar sunan ta ta gane kawai tayo murmushi ta miƙe tsaye. Shima kuma kallon ta yake da irin nata mamakin har yana cewa Zahra da gaske kece, kin ga kenan ya san Mama."

Bily tace, "ƙwarai ya san ta."
"Daga nan sai Mama ta riƙo hannun Manal tace mu taho gida, muka dawo gida Manal ta takura akan Mama ta faɗa mata abinda yake faruwa, Mama sai tace wanda take kallo matsayin mahaifin mijin ta itama shine mahaifin ta."

Bily ta wara ido tare da dafe ƙirji tace, "Mun shiga uku! Kenan mahaifin Adnan shine mahaifin ku? Kenan auren ya da ƙanwa akayi ko me?." Mubeena tace, "Mun kasa samun wannan amsar daga wajan Mama, Adnan ɗin da kansa yazo gidan cikin yanayin damuwa amma Mama tace ya tafi babu aure tsakanin sa da Manal, tana kuma bashi shawara daga wannan lokaci ya cire Manal daga ransa."

"Innalillahi! Mubeena wannan abun fa ba ƙaramin abu bane." Mubeena ta sauke numfashi tace, "akwai wani abun da yafi wannan Bily." Ta kalle ta tace, "ina jin ki." Ta sauke numfashi tace, "Mahaifin Adnan wanda bamu da tabbacin a yanzu ba shine mahaifin mu, shine wannan Alhaji nawa da muka rabu."

Bily ta ɗora hannu a kai tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mubeena da gaske kike wai ko wasa?." Mubeena tace, "wallahi da gaske nake shine, abinda yake ɗaga min hankali kenan Bily, in ya kasance shine mahaifin mu kenan shine ya nemi yayi lalata ƴar cikin sa?. A tarihin rayuwa ta dole na rubuta mahaifina yaso yin zina dani kenan Bily...." Ta faɗa cikin rauni mai nuni da damuwar da take ciki har zuciyar ta.

Bily tayi hanzari ta tarar numfashin ta tace, "Ki daina wannan ƙazamin tunanin Mubeena, wannan ba abinda zaki tunani a kai bane. Taya zai kasance mahaifin ki Mubeena?." Mubeena tace, "meyasa Mama take cewa uban Manal ne? Indai har ya kasance mahaifin Manal nima mahaifina ne."

Bily cikin tashin hankali da son ta kwantar mata da hankali ta kalle ta tace, "wataƙila Maman ta faɗa ne kawai amma ba hakan bane ba."
"Meyasa tace auren Manal da Adnan ya ƙare to? Meyasa ta dage a kan Manal babu ita babu Adnan duk da son da take yiwa auren su?. Bily Mama tana son auren Manal da Adnan kema kin sani, amma yau itace take hana Manal ko waya dashi, in ba mahaifin mu bane waye shi?."

Bily tayi shiru tana tunani ta kasa cewa komai saboda itama abin ya ɗaure mata kai sosai. Ganin hakan sai Mubeena tace, "indai har ya kasnace mahaifin Manal nima mahaifina ne, sai dai in nida Manal ɗin kowa mahaifin sa daban:" Bily ta kalli Mubeena kafin tayi magana Mubeena tace, "babu wanda muka sani da dangin mu na uwa da uba, dole zamu iya mu'amala da dangin mahaifin mu ko mahaifin na mu ba tare da mun sani ba, jikina yana bani tabbas wannan mahaifin Adnan ɗin kuma tsohon saurayina wani ne a cikin dangin mu, in ba mahaifin mu ya shafi ahlin mu."

Bily ta sauke numfashi bata ce komai dan ta kasa magana ba dan bata san abinda zata ce ba. Mubeena tace, "Amma waye shi..? Meyasa Mama bata son wanda ya raɓe shi ne?, Meyasa take cewa babu aure a tsakanin Manal da Adnan?."

BDƘB3P04

Mubeena ta sake kallon Bily da jajayen idanun ta tace, "babu mai bani amsar nan sai Mama, ita kuma Mama taƙi maganar gabaɗaya." Bily ta jinjina kai tace, "gaskiya wannan babban lamari ne ba ƙarami ba, ina Baba to?."
"Baba baya nan, sai zuwa gobe ina jin zai dawo nasan da ya dawo wataƙila maganar tazo ƙarshe."
Chapter 4 · 0% Book details