← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 84

Sashe 45

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa aka karɓe ta, Bebi da Huzaifa sun ƙarasa asibitin da gaggawa Bebi ya fara auna zuciyar Mama aka saka mata abinda zai taimaka mata numfashi ta ya dawo daidai, aka saka mata ruwa da allurai a jijiya. Sun cika asibitin gabaɗaya hankalin su a tashe yake, gani suke kamar Mama zata mutu hankalin su yaƙi kwanciya. Manal da Mubeena sun ware a waje ɗaya har lokacin Ayaan yana wajan Surayya dan itama ita da Maman ta sun biyo su.

Bebi da ya fito wanda basu ana likitan Mama bane kallon sa suke yi kafin yayi murmushi yace, "Kar ku damu, zata dawo daidai nan da anjima in sha Allah. Firgice ne ya haifar da hakan kasancewar daman tana da ciwon zuciya." Alhaji Ahmad da yake cikin ruɗani da tashin hankali yace, "tana da ciwon zuciya?, Kaine Dr Adnan?."
"Eh ni ne, tana da ciwon zuciya kamar yadda nace. Na san condition ɗin ta kusan file ɗin ta a hannuna yake yanzu."

Alhaji Bello yace, "kuma kai ne mijin Manal ƴar ta?." Ya ɗaga masa kai alamun eh haka ne ya kalli inda Manal ɗin take dan kukan ta gabaɗaya ake ji a wajan. Ji yake kamar ya je ya ɗauke ta ya samu waje mai kyau ya rarrashe ta amma babu damar aikata hakan dan bata cikin hankalin ta.

Daddy ya kalle shi yace, "Adnan ka tabbatar zata samu lafiya?."
"İn sha Allah Daddy, zata warke da izinin Allah, ta firgita ne sosai." Daddy ya kalli Alhaji Ahmad da yake kallon sa shi ma, kafim Daddy yayi magana yace, "Ali ko?" Ya kalli Abba ma da yake zaune yace, "Ibrahim, ku ne wanda nake tunani ko?." Daddy ya ɗaga masa kai alamun eh yayi murmushi yace, "har abada fuskar ku baza ta ɓace min ba."

Bebi ya kalli agogo ganin lokacin sallah yayi sai ya wuce masallaci, suma duk suka wuce aka yi sallah aka sake dawowa aka zauna kowa ya kasa motsawa saboda gani ake kamar in aka tafi za'a ce Mama ta rasu ne, shiyasa suka kasa suka tsare a wajan ana jiran farkawar Mama.

BDƘB3P27

Suna nan a tsaye ana jiran tsammani Baba ya kalli Mubeena da Manal da suke tsaye yace, "ku samu waje ku zauna, tunda muka zo kuna tsaye, tsayuwar bata gaji daku bane?." Mubeena tana riƙe da hannun Manal Maman Surayya tace, "Manal ki karɓi yaron nan, tun ɗazu yake kuka har yanzu."

Surayya ta kawo mata shi dan itama kuka take yi, Baba ya kalli Adnan yace, "Adnan don Allah kaje dasu inda zasu zauna, kamar tsoron kowa suke yi a nan sai ɗari-ɗari suke." Bebi ya wuce zuwa inda suke Baba yace su bishi ya kai su wani falo ƙarami mai kyau, Surayya na riƙe da Ayaan suka zauna Surayya ta bata shi ta karɓa ta riƙe shi amma ta kasa yi masa komai. Suna zaune a tare ta bashi nono yana sha ita dai idon ta a rufe yake saboda tashin hankali yayi nata yawa. Ruwa Surayya ta miƙa mata kamar yadda Bebi ya bata yace ta bata ta sha, ta karɓa ta sha ta ajjiye ragowar tayi shiru hankalin ta na wajan Mama.

A nan Mubeena da Surayya suka yi sallah basu jima da idarwa ba sai suka fita a lokacin Ayaan yayi bacci tana riƙe dashi a hannun ta. Bebi ne ya shigo inda take bata ɗago ba ya ƙaraso kusa da ita ya ɗauƙe Ayaan daga jikin ta, a lokacin ta buɗe ido ta kalle shi ya kwantar dashi kan kujera mai zaman mutum ɗaya ya dawo ya zauna kusa da ita yana kallon ta idanun ta wanda ta sake rufe su, kafin yayi magana ta kwanta a jikin sa ta riƙe shi sosai tana kuka.

Shima riƙe ta yayi yana shafa bayan ta a hankali cikin sigar rarrashi da son kwantar mata da hankali. cikin kuka Manal tace, "Don Allah kar ka bari wani abun ya samu Mama, kar ka bari wani abun ya same ta, in Mama ta bar duniya nima mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa babu Mama ba. Bana buƙatar kowa Mama kawai nake buƙata, bazan yafewa musu ba tunda sune silar shigar Mama na wannan hali."

"shiii! Ki daina fadɗar haka Manal, Allah shi yake ɗorawa bawan sa ciwo duk lokacin ya so, wani ko wata basa sakawa wani ciwo sai Allah kawai. Ki mata addu'a Allah ya bata lafiya kuma na faɗa miki jikin nata akwai sauƙi sosai."

Bata ce komai ba tana jikin sa ya ɗago kanta ya riƙe kan nata yace, "ki yi haƙuri ki daina wannan kukan, kan ki ciwo yake yi sosai." Ko ido bata buɗe ba balle tayi magana, ya share mata hawayen da suke fuskar ta yace, "don Allah ki nutsu kinga ba wani lafiya ne dake ba har yanzu, ki dawo hankalin ki don Allah."
Zama tayi sosai akan kujerar tayi shiru ya kalle ta yace, "ina zuwa" ya faɗa yana fita daga ɗqkim ta bi bayan sa da kallo gabaɗaya hankalin ta baya jikin ta.

Haka suka wuni a asibitin kowa ya kasa tafiya kar ace Mama ta rasu, har bayan i'sha Mama bata farfaɗo ba har goma na dare ana zaune ana jiran tsammani. Manal ta fito suna tare da Mubeena waje ɗaya, kallon kowa suke kamar bare ita da ita ne kawai suke zaune basa yiwa kowa magana indai ba Baba ba.

Baba ya kalli Manal da take zaune ya kalli Bebi yace, "Adnan ba yanzu zaku tafi gida bane?." Adnan ya kalli shi yace, "yanzu zan tafi."
"Yanzu za ku tafi dai, me Manal ɗin zata yi a nan?." Manal ta girgiza kai tace, "Baba don Allah kar kace na tafi."
"Na ce Manal, haƙuri zaki yi ku tafi zaman ki bazai bata lafiya ba. Allah ya kaimu gobe sai ki dawo." Jin abinda yace sai tayi shiru kawai bata ce komai ba. Manal ba dan ta so ba haka suka tafi gida ita dashi ko Maman Surayya ma bata biyo su ba dan bata cikin wannan nustuwar itama ta manta ma shaf da batun a gidan Manal take.

Kwanan Mama biyu a asibitin Bebi ya hana a ganta dan ta farfaɗo a kwana na farko yana sane ya hana kowa ganin ta sai da aka kwana biyu saboda a samu ta huta sosai, Manal da Mubeena kawai ya iya bari suka ganta su ma basu san ta fardaɗo ba lokacin da suka shiga bacci take yi.

Ranar kwana na biyun da rana yake sanar dasu farkawar ta kowa yayi farin ciki da hakan, aka shiga ana yi mata sannu tana amasawa amma bata cewa komai sai dai ta ɗaga kai kawai. A ranar suka koma gida dan tace ta gaji da zaman asibiti babu wanda ya bita daga Manal dai Sai Mubeena saboda kowa tsoro yake yi kar ta sake faɗawa wani yanayin.

Sai washe gari ta kama ranar juma'a bayan sallar juma'a Mama tana zaune da Manal da Mubeena duk da ba magana suke yi ba amma duk kallon ta suke yi dan tunda tayi rashin lafiya bata sani warware sosai ba.

Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya kalli Mama yace, "Fatima ki shirya akwai babban baƙo da zai shigo yanzu." Mama ta saka hijjabi Manal ma daman da mayafi a jikin ta suka gyara sai ga Baba ya shigo da babban Malami wanda aka san fuskar sa a ko ina wato Malam Habib Usman.
Ganin Malam sai mamaki ya kama Mama ta gyara zama tace, "Malam barka da zuwa" ta faɗa da girmamawa tana mamakin abinda ya kawo shi gare ta.

Aka ɗaukowa Malam farar kujera ya zauna kowa ya gaishe shi ya amsa da fara'a ya kalli Mama yace, "Ya ƙarfin jikin naki?." Mama tace, "da sauƙi, jiki yayi sauƙi."

Malam yace, "Allah ya ƙara lafiya." Aka amsa da amin kafin Malam yace, "na san kin yi mamakin ganina a gidan nan ko?."
"Gaskiya dai nayi mamaki, ni da a radio ko a waya nake ganin ka yau ace ga Malam har gidana?, abin ya ɗaure min kai." Malam yace, "ni na san hakan, amma ba wani abun bane gyara zumunci nazo nayi."

Malam ya sake cewa, "ƴan uwan ki maza da mata sun je har gida sun same ni akan abinda ya faru, sun faɗa min komai sun kuma nuna min nadamar su a bayyane, sannan suna kuma buƙatar ki dawo ciki ahlin su, sannan suna so ki yafe musu ki shiga cikin su a cigaba da rayuwa cikin farin ciki da zumunci. Faɗa min hakan da suka yi sai nace bara na taso da kaina nazo na taya su baki haƙuri da kuma neman afuwa, dukkan su suna shakkar zuwa saboda kar ciwon ki ya sake tashi. Shiyasa nazo ni kaɗai ba tare da rakiyar kowa a cikin su ba."

Mama ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba Malam yace, "Zahra'u a labarin da aka bani a kanki tabbas ba a kyauta miki ba, sun watsar da zumunci babu kuma sun yi watsi da wasiyyar mahaifin su a kan ki. Sun ɗauki tsana sun ɗora miki akan abinda ba laifin ki ba, itama mahaifiyar ki ba laifin ta ba amma saboda wata baiwa da Allah ya baki keda ita suka kasance basa zumunci dake. Duk da dai yanzu ba a tuna baya, ina faɗe ne dan ki san na san komai an faɗa min har aurar dake da suka yi ga wanda basu sani ba duk na sani, duk abinda na faɗa miki anyi ko?."

Mama ta ɗaga kai tace, "anyi Malam." Malam ya sake cewa, " yanzu da suka dawo suna neman afuwar ki meyasa baza ki yi haƙuri ki karɓi ƴan uwan ki ba?." Mama ta girgiza kai tace, "bana ji a zuciyata zan iya hakan Malam, saboda in na tuna abubuwa da suka faru sai naga gwara ma nayi rayuwata ba tare da su ba, gwara ace na cigaba da rayuwa har mutuwa matsayin wacce ƴan uwan ta suka wulaƙanta ta suka barta. Bani buƙatar su gabaɗaya, bana buƙatar su shiyasa kawai nace ni ba zan iya magana da kowa ba."
Chapter 45 · 0% Book details