← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 84

Sashe 31

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal ta kalli yaron tace, "Ayan." Ya haɗa goshin su waje ɗaya da nata ya ce, "Allah ya raya mana shi, Allah ya yi masa albarka."
"Amin Partner."
"Kamar wasa wai ɗan mu ne nida ke ko?." Manal tayi murmushi tace, "abun kamar a mafarki." Ya yiwa bakin ta kiss ya ce, "ba mafarki bane, da gaske ni da ke iyaye ne yanzu" ya faɗa yana riƙe hannun ta yana kallon ta.

Ta kwanta a kafaɗarsa ya sake cwwa, "na gode da kika mayar dani uba Manal." Tayi murmushi tace, "nima na gode da ka mayar dani uwa, yanzu na tashi daga Manal na dawo Ammin Ayan." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne wannan Partner, bakya jin yunwa?."
"Bana ji ai naci abinci, amma nasan kai kana ji ko?."
"Ina ji, amma bazan ci ba sai na tashi daga bacci." Ya sake cewa, "zan kulle babbar ƙofar farko da ta tsakiya, zan bɗe ta falon tsakiya a dinga shigowa ta nan. In ina can babu wanda ya san ina nan."

Manal tace, "yadda ka yi Daddyn Ayan." Ya girgiza kai yace, "A'a kar mu zo nan, kira ni da partner bana son wannan Daddy ko Abban wane ɗin nan." Tayi dariya sai kuma ta tsaya da dariyar tana yatsine fuksa tace, "Wayyo, daman in aka yi dariya sosai zafi ake ji?."
"Ayya sorry, ai ba'a dariya mai yawa, tari ko attishawa duk sai kin ji a jikin ki. Amma da ya fara warkewa shikenan, kedai ki lallaɓa ya warke in ba haka ba sabon stitches yafi haihuwar wahala."

Manal tace, "Allah ya tsare ni." Yayi murmushi ya amsa. Wayar ta aka jira ganin Maman Surayya ce
sai ya fita ya same su a babban falo ya raka ta har ɗakin Manal ɗin shi kuma ya shiga ɗakin sa ya kwanta dan ya huta.

Ana ta zuwa barkar haihuwa Manal suna tare da Mama duk abinda bata sani ba tana faɗa mata
cikin kwana uku ta fara jin sauƙin ciwon ɗinkin dan Mama na kula da ita sosai. Duk yan gidan su babu wanda bai zo ba da matan yayyen sa kowa yazo har da kaya aka dinga kawo mata na barkar samun Ayan. Har daga gidan su Bebi sai da aka kawo kayan haihuwa ita dai nata ido sai bayan an tafi Mama sai tace ai haka ake yi.

Matar Huzaifa da matar Hamza ranar da suka zo wuni suka yi har dare kafin su tafi gida, ai kam taji daɗi sosai sun yi hira kuma sun sake sabawaa da juna kamar mazajen su.

Ranar suna da yake ba'a yi taro Manal tace bata so kai baza nace ma ranar suna ba, sai na gida kawai ƙannen sa da kuma sunMubeena kawai. Manal tayi kwalliya har lalle anyi mata, suka ɗauko mai hoto yazo gidan ya yi musu hotuna ita dashi masu kyau sosai. Ranar saurayi Mubeena ma yazo barka har da kayan barkar sa bayan ya tafi Manal ta dinga tsokanar Mubeena kamar ba yayar ta ba.

Manal na samun kula a wajan Mama sosai ta ko wanne ɓangare, gashi jegon ya karɓe ta tayi kiɓa duk da ba sosai ba amma da ka ganta ka san ta canja, Ayan ɗin ma yayi kiɓa abin sa kowa ya ganshi sai ya yaba saboda kyau. Kamar sa ta fito soaai kama ɗaya sak da Manal har hasken irin nata ne dogon hancin ne kawai na baban sa da tsaho.

Ranar da suka cika sati biyu Manal tana zaune ita kaɗai a ɗakin ta da yamma Bebi ya shigo da sallama ta amsa tana kallon sa ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya ce, "Partner nayi kewar ki, rabon da mu zauna haka ni dake ma na manta." Ya ɗauki Ayan a gadom sa ya dawo ya zauna ya ce, "Sai kallona ki ke yi, ke ba tani ma kike ba, kyau kawai kike yi abin ki."

Manal tayi dariya tace, "ni na isa nace bana ta kai? Allah nayi kewar ka nima sosai." Ya Harare ta yace, "ba wani nan, inda kin yi kewata bazan gan ki haka ba." Ta shagwaɓe fuska tace, "Allah nayi kewar ka sosai." Ya ajjiye Ayan ɗin a kan gadon ya kalle ta sosai yace, "to nuna min na gani."

Ta saka hannu biyu ta riƙe fuskar sa sai ya ɗaga mata gira tayi dariya ta rufe fuskar ta da hannun ta, Bebi ya ce, "My Partner, kunyar nan tana miki kyau." Ta matso sosai kusa dashi ta shiga jikin sa ya rungume ta harda sauke ajiyar zuciya ya ce, "yaushe rabon da na jiki a jikina? Gaskiya nayi kewar ki my love" ya faɗa yana sake riƙe ta sosai itama ta riƙe shi dan tayi kewar sa tunda ta riga da ta saba ko yaushe tana jikin sa.

Ya mata kiss a goshi ya ce, "Yaushe zamu kwana nida ke a haka? Ina kunyar Maman Surayya ne da Allah yau tare zamu kwana."  Manal tana ɗago daga jikin sa tace, "na fahimci kana kunyar ta sosai, ko zama baka iyawa in tana nan. Itama kuma kunyar taka take ji."

Yayi murmushi ya ɗago ta daga jikin sa ya ce, "nima na kula hakan, tsoran tsoro muke yi ni da ita." Ta girgiza masa kai alamun eh yace, "Allah sarki! Ai tayi ƙoƙari soaai, ta baro gidan ta da yaran ta ta taho nan kawai saboda ta kular min dake, gashi kin yi kyau har ƙiba ma kin yi kamar baki da ciwon sugar, Me ya kamata mu yi mata in lokacin tafiyar ta ya kusa?."

Manal tace, "Ai Mama tana sona tun ina yarinya in ji Mama, da yake ni age mate ɗim Surayya ce komai a gidan su nake yi har makaranta tare muke zuwa."
"Faɗi abinda kike so mu yi mata."
"Abinda kace shine daidai." Ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru kafin yace, "kafin lokacin zamu san abinda zamu yi in sha Allah. In anjima da daddare zamu je asibiti akwai likitan da zata duba min ɗinkin jikin ki."

Manal tace, "to Allah ya kai mu, ai na warke ma fa gabaɗaya na daina jin sa." Ya amsa da amin yana Kallon bakin ta. Sai ta rufe bakin ta da hannun ta ganin hakan sai ya mayar da fuska kalar tausayi yace, "ni ko? Ni ko? Shikenan na gode." Manal tayi dariya ta ɗauki Ayan a cinyar sa ta kwantar dashi a gefe, ta juyo da fuskar sa ta ɗora bakin ta akan nasa, abinda yake jira kenan nan da nan yayi accepting.

Sun fara mantawa da inda suke kissing ɗin ta romantically itama kum haka, dukkan su sun yi kewar junan su yanayin su zai gwada haka saboda yadda suka riƙe juna kamar za'a ƙwance ɗaya a cikin su. Buɗe ƙofar kawai suka ji anyi a tare suka kalli wajan suka haɗa ido da Rumana da take tsaye kamar zata haɗɗiye zuciya ta mutu, ganin Rumana ce sai kawai yayi tsaki ya sake juyo da fuskar Manal ya sake mayar da bakin sa cikin nata.

Da sauri Manal tayi baya ta ta raba kanta daga gare shi ta  sake kallon Rumana da har lokacin tana kallon su cikin kallon da yake nuna zallan kishin da yake addabar zuciyar ta. Muryar Mummy suka ji tana cewa, "tsayuwar me kike yi? Manal ɗin bata nan ne?." Jin kamar tawowar Mama sai Bebi ya miƙe tsaye Manal ɗin ma haka ta ɗauki ɗankwalin ta ta ɗaura. A  lokacin Mama ta shigo ganin suna tsaye cirko-cirko ta kalli Rumana ta sake kallon su sai tace, "Manal ki fito mu gaisa" ta faɗa tana barin wajan dan bata san Bebi yana ciki ba da baza ta kai kanta wajan ba, ganin motar sa bata nan bata ɗauka yana gidan ba.

Manal ta dauƙo Ayan tazo ta wuce Rumana da take tsaye har lokacin kamar an dasa ta, Sai da Bebi ya fito ya wuce ta sannan ta iya takowa ta zauna akan kujera ta dafe kanta.

Ganin Ammi sai ya ɗan yi murmushi Ammi tace, "ashe kana nan, mu da muka ga motar ka bata nan mun ɗauka kana asibiti ai." Bebi shi kansa kunyar su yake ji duk da basu suka gan shi ba amma ba daɗi. yace, "motar na bayar a kai Maman Surayya gida shiyasa. Mummy barka da rana." Mummy ta amsa tana sake kallon yaron tace, "Sumayya na faɗa miki yaron kamar Ɓaman sa, ma sha Allah akwai haske."
"Ammi barka da rana."
"Barka dai Bebi, ga Ayan ma sha Allah yayi kyau." Manal ma ta gaishe su suka gaisa da fara'a kafin ta kalli Mummy tace, "Mummy ban san zaki zo ba ai da na shiryawa zuwan ku, zuwan ki gidan nan na biyu kenan."

Mama tayi dariya tace, "To Manal ai zuwan sai ya kama ake yin sa." Tayi murmushi ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo da apple wacce bata rabuwa da ita. Ammi tace, "ki zaman ki Manal hakan ma mun gode." Tayi murmushi tana zaune cikin jin nauyin su.

Bebi fita yayi daga falon Rumana tunda ta dafe kai bata ɗago ba, daman hanya ce ta biyo dasu Ammi tace su shigo suga yaro dan haka basu jima ba suka tafi Manal har bakin motar ta raka su driver yaja suka tafi har lokacin Rumana babu abinda tace yanayin ta gabaɗaya ya canja.

Rumana suna komawa gidan Mummy ta shiga ɗakin Mummy a guje Ammi ta bita da kallo ta kalli Mama tace, "Wai ke yarinyar nan take nufi ne?." Mama tace, "na fahimci akwai wani abun tun zuwan mu gidan."
"To Mama kishi take da matar sa kenan?." Mama ta  ɗaga mata hannu ta bi bayan sa ta samu tana wani irin kukan da ya bawa Mama tsoro, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tace, "Rumana lafiya kike? Me ya faru?" ta faɗa tana riƙe kafaɗun ta amma kuka take yi bata daina ba.

Hankalin Mama ya tashi tace, "kin faɗa min meye ya faru? Ki daina kuka ki faɗa min lafiya kike? me ya same ki?."
"Mama Bebi baya sona, Mama zan mutu ji nake kamar ƙirjina kamar zai fita Mama. Matar sa yake ao ba ni ba, baya ƙaunar ganina ko kaɗaan!" Ta ƙarasa faɗa tana kuka.
Chapter 31 · 0% Book details