← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 84

Sashe 1

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BDƘB3P001

Manal ta buɗe idanu tana kallon Mama gaban ta na faɗuwa sosai tsoron ta ya bayyana a fili ƙarara, ƙirjin ta har ɗagawa yake saboda tashin hankalin abinda Mama tace wanda ko a mafarki bata shiryawa jin sa ba. Abinda bata yi zato ba shine ya fito daga bakin Mama, shiyasa hankalin ta ya taji har ta rasa abinda zata ce sai kallon amma da take yi idanu a waje.

Daƙyar ta iya buɗe baki tace, “Mama ban gane abinda kika ce ba, kaina ya kulle ki yi min bayani yadda zan fahimta.” Mama ta kalle ta tace, “baza ki gane ba Manal, Daman bana so ki gane ɗin ki cigaba da zama da kai a kullen kai zai fi miki amfani, koda na so ki gane hakan ba ganewar zaki ba. Ki cigaba da zama cikin rashin sani. abu ɗaya na sani kin gama auren Adnan, babu ke babu shi har abada.”

Manal ta tsorata sosai ta kalli Mubeena da take tsaye itama cikin tashin hankali ta sake kallon Mama tace, “Mama kin saka ni a ruɗani, ki cire ni daga cikin wanna ruɗanin don Allah. Zuciyata bugawa take kamar zata fito, ki taimaka ki sanar dani Mama.” Mama ta kulle ido ta buɗe tace, “baza ki taɓa fita ba Manal, baza ki fita daga cikin ruɗanin da kike ciki ba, gwara ki yi ƙoƙarin daidai ta hankalin ki tun kafin shima ya gushe.

Mubeena tace, “Kenan Mama mahaifin Adnan mijin Manal shine mahaifin mu ko me kike nufi? Bamu gane ba ki ganar damu don Allah.”
“İn zuciyar ku haka ta ɗauka ki ɗauka haka ne, in zuciyar ku ba haka ta ɗauka ba ku ɗauka ba haka bane. Abu ɗaya na sani kawai, auren Adnan da Manal tamkar rubutu ne a kan ruwa.”
“Mama don Allah ki fahimtar damu” Mubeena ta faɗa cikin nata tashin hankalin.

Mama ta daka mata tsaya tace, “baza ku fahimta ba, na faɗa muku baza ku gane ba meyasa ku ka cika naci ne? A bar maganar a wajan nan bana so a sake tayar da ita, bana so wata ta sake yi min maganar nan yanzu ko nan gaba. Ko waye shi a wajan ku a bar maganar nace” ta kalli Manal tace, “ki rubuta a zuciyar ki babu ke babu Adnan indai ina da rai” tana gama faɗar hakan ta bar tsakar gidan duk suna tsaye ko wacce da kalar nata ruɗanin.

Mubeena tunanin ta kenan mahaifin Adnan mahaifin su ne, a yadda Mama tayi maganar Manal da Yayan ta take zaune matsayin matar sa ko me? Kenan mahaifin tane ya nemi yin lalata da ita?. To in ba mahaifin su bane waye shi? Ga Mama tace auren Manal da Bebi babu meyasa tace hakan?. Numfashi ta sauke babu mai bata amsa sai Mama, Amma zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi, tsoro ya cika mata zuciya bata so tunanin ta ya zama gaskiya.

Manal ma tunanin da take yi kenan, waye mahaifin Adnan a wajan ta? Uba ko kuwa uban miji?. Waje ta samu ta zauna a tsakar gidan ta rasa ma wanne tunani zata yi a lokacin, kawai ta dafe kai tayi shiru ta rasa abinda yake mata daɗi, Mama ce kawai zata fitar dasu daga wannan tashin hankalin gashi Mamn taƙi bada damar hakan.

Tun fitar su Mama Bebi ya daskare a wajan tana kallon Abba da ya kasa motsi ya zubawa ƙofar da su Manal suka fita ido, Mummy ta kalli Bebi da yake tsaye suke haɗa ido ta sake kallon Abba da ya kasa motsin kirki tace, “Wacece ita? Ka san tane?.”

A lokacin ya dawo daga tunanin sa ya kalli Bebi yace, “itace mahifiyar matar ka da gaske ko wasa?.” Bebi zuciyar sa bugawa take yi sosai saboda tsoro da tashin hankali yace, “itace Abba, Akwai abinda ya faru ne?.”
“İnnalillahi wa’inna ilaihir raji’un!, kuma wannan yarinyar ma da suka zo tare ƴar ta ce?.” Bebi yace, “eh, yayar matar tawa ce sunan ta Mubeena. Abba me yake faruwa ne haka?.”

Tissue ɗin da take gefe a ajjiye Abba ya zara ya goge gumin da yake yi tsatstsafo masa, ya kasa cewa komai tashin hankali ya gama dabaibaye shi. Kenan Mubeena da yake so da aure ƴar Zahra ce? Kenan Mubeena da ya nema a baya dan yayi lalata da ita ƴar Zahra ce?. A bayyane yace, “Ya rasulillahi! Ina zan kai wannan lamari?.” Kallon sa su Bebi suka yi Bebi ya matso kusa dashi yace, “Abba don Allah ka yi min bayani, Wacece ita a wajan ka?.”

Bai iya cewa komai ba ya juya kawai ya fita da sauri, Bebi ya kalli Mama yace, “Mummy me yake faruwa ne haka? Meyasa tace Manal tazo su tafi? Meyasa tunda taga Abba ta canja?. Meye alaƙar su dashi har haka?.” Mummy tace, “nima tambayar da zan maka kenan, Wacece ita a wajan sa?.” Da sauri Bebi ya fita hankalin sa a tashe yake sosai so yake yaji abinda yake faruwa kawai ko hankalin sa zai kwanta.

Office ya shiga ya kira wayar Manal ba jimawa ta ɗauka yace, “Me yake faruwa Manal? Daman Mamaa ta san Abba ne?. Ko kuma ta san fuskar sa a lokacin da abin nan ya faru a tsakanin ku?, ki yi min bayani Manal zuciyata ta gaza ɗauka.” Manal murya a raunane tace, “ta san labarin amma bata san shi ba, kuma ban faɗa mata ba, hankalina a tashe yake domin Mama ta ƙi yi mana bayanin abinda yake faruwa, daga ƙarshe tace kar wanda ya sake yi mata maganar.”

Bebi yace, “kuma bata faɗa miki komai ba?.” Manal tace, “tace min indai ita ta haife ni aure na dakai ya ƙare, Mama tana cemin wanda nake kallo matsayin uba a wajan ka nima ubana ne.”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Kin san abinda kike faɗa kuwa? Kin ji yadda zuciya ta buga da jin wannan kalaman naki?.”

Manal tace, “nima a yanayin da nake ciki kenan.”
“Wanda kike kallo matsayin uba a wajana kema uba ne a wajan ki, me Mama take nufi da wannan kalaman nata? Manal don Allah ki faɗin min kafin zuciyata ta buga.”

Manal a raaunane tace, “nima ban sani ba, iya abinda tace min kenan bayan shi tace kar na sake yi mata maganar. Mama tace min babu ni babu kai har abada, na tambayi dalili taƙi faɗa min.” Bebi salati kawai yake yi a zuciyar sa tsoro ya gama mamaye masa zuciyar sa jin abinda Manal take faɗa. Manal tace, “ka tambayi Abban ko zai maka bayani.” Bebi yace, “Manal shima Abba yaƙi cewa komai, ƙarshe yayi tafiyar sa ya bar ni a tsaye ina tunani. Manal me yake faruwa?.”

Bata bashi amsa ba taji Mama tana magana daga bayan ta tana cewa, “Malama ki kashe wayar nan babu ke babu shi kamar yadda na faɗa miki.” Muryar Mubeena taji tana cewa, “Mama mijin ta ne fa.” A fusace taji Maman tace, “na fiki sanin mijin ta ne, daga yau ki fara saka ta a layin wanda basu da aure, domin auren ta dashi dole ya ƙare ko suna so ko basa so.” Daga nan yaji Manal ta yanke kiran.

Tashin hankali ya taru ya yi masa yawa sai maimaita salati yake yi hannu yana rawa ya sake kiran ta amma bata ɗauka ba ya ajjiye wayar yana tunanin lamarin mai kama da shirin film.

A haka suka koma gida dashi da Mummy da Maryam baya iya cewa komai, duk yadda yaso daurewa akan lamarin Manal da Maman ta kasawa ya yi, hakan ya sa yana ajjiye su Mama a gida ko ciki bai shiga ba ya ɗauki hanyar gidan su Manal.

A ƙofar gidan ya ajjiye motar yana kallon gidan dan bai taɓa shiga kai tsaye ba, a ko yaushe itace take yi masa iso ko kuma Baba ko Yayan su Haruna. Fitowa tayi daga motar ya ƙaraso ƙofar gidan ya rasa abinda zai yi.

Surayya ƙawar Manal ya ganj ta nufi gidan ganin sa ta tsaya tana murmushi na sanayya ta gaishe shi ya amsa tare da faɗin, “Yauwa don Allah ki faɗawa Mama zuwana.” Surayya ta amsa tana shiga cikin gidan. Ba jimawa sai gata ta dawo tace, “ka shigo.”

Sai da yayi ajiyar zuciya ya shiga cikin gidan har cikin falon da aka saka masa sababbin kujeru ya tarar da Mama a zaune ita da Manal da Mubeena. Yayi sallama Mama ta amsa ya sake gaishe ta ta amsa ba yabo babu fallasa. Ya sauke nunfashi ya ce, “Mama don Allah zan iya sanin abinda yake faruwa?.”

Mama ta kalle shi tace, “nace ka shigo ne daman saboda na yi maka iyaka da Manal, ka daina lissafa Manal matsayin matar ka daga rana irin ta yau, domin Manal baza ta sake zama dakai matsayin matar ka ba. ka ɗauka baka san wata mai suna Manal aba a duniya, ka ɗauka rayuwar da ku ka yi da ita tamkar a mafarki ne.”

Adnan hankali a tashe, “Mama me yayi zafi haka?.”
“Kaje ka tambayi mahaifin ka shine zai faɗa maka abinda yayi zafi bani ba, Abinda na faɗa shi za a yi koda bana raye, domin auren ka da ita babu shi!.” Mamaki yake yi jin yadda Mama take magana kamar ba ita ba ya kalli Manal da take gefe tana shafe hawaye yace, “Mama don Allah ki sanar dani abinda yake faruwa har kika ce haka, dukkan mu a ruɗani muke muna so mu san amsar tambayar da take zuciyoyin mu, don Allah ki sanar damu ko zamu fita daga cikin tashin hankalin da muke ciki.”

Mama tace, “ai nace kaje ka tambayi mahaifin ka ko? Kaima kawai saboda girma mutuncin ka da nake gani ne ma ya saka nake sauraren ka wallahi, da yanzu ka tashi da ƙafar ka ka bar gidan nan saboda irin kalamam da zasu fito daga bakina. Kaje ka tambayi mahaifin ka kaji wacece Manal a wajan sa, in bai faɗa maka ba kar kayi tunanin zaka fita daga wannan ruɗanin da ka ke ciki har abada.”
Chapter 1 · 0% Book details