← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi Manal tayi da sauri ta shiga ɗaki tana kuka. Bebi ya kalle ta kafin ya sauke numfashi gabaɗaya bashi da nutsuwa ko kaɗan a haka yace, “shikenan Mama na gode, zan je na tambaye shi in sha Allah.”
“Yana da kyau.”
“Sai anjima” ya faɗa yana tashi ya tafi jiki babu ƙwari ko kaɗan.
Komawar sa gidan su ya tarar da wani tashin hankalin, domin kuwa Mamy ce a harabar gidan na su tana kuka tana dukan Maryam ta ko ina saboda abinda Maryam ta aikata.

Da hanzari ya faka motar ya fito ya ƙaraso wajan yana cewa, “Haba Mamy! Don Allah ki bari a gaban mutane ki duba kowa yana kallo na gidan nan” ya faɗa yana nuna mai gadi da drivern su Mamyn ga mai aikin Mamy. Mamy tace, “Adnan zuciyata zafi take min, Lubna na san fyaɗe aka mata ita kuma fa? Da hankalin ta da tunanin ta meye zata yi min haka Adnan?” Mamy ta faɗa tana hawaye cikin ɓakin ciki da ɓacin rai.

Adnan ya kalli Maryam da take kuka itama yace, “Na sani Mamy, amma ki yi haƙuri mu koma ciki wannan maganar ba ta nan bace.” Mamy bata ce komai ba ta cillar da madokin hannun ta ta juya ta koma gida. Ya kalli Maryam da take hawaye shima cikin ƙunar rai yace, “kin yi wasa da damar ki, kin ɓata wayon ki. Shekarun ki basu amfana miki da komai ba, girman da kike dashi na jiki ne kawai babu na hankali.”

Ita dai kuka take ya sauke ajiyar zuciya yace, “ki shiga ciki.” Jiki a sanyaye ta shiga wajan Mama dan baza ta iya shig wajan Mamy ba. Bebi ya sauke numfashi yana salati a bayyane yace, “Wannan tashin hankali da me yayi kama? Daga wannan Sai wannan da wanne zan ji?, da damuwar Manal ita da Maman ta ko kuma da wannan damuwar?.”

Wajan Mama ya shiga ya samu tana ta yiwa Maryam faɗa itama tana hawaye cikin ɓakin ciki da takaicin abinda ta aikata. Kasa zama yayi kawai ya fito a nan yayi karo da Daddy da kuma Uncle suka gaisa suka shiga wajan Abba shi kuma ya shiga mota kawai ya zauna ba tare da ya san abinda zai yi ba.

Babu jimawa yaga ana kiran sa waya a ya ɗauka ganin sunan Daddy bai jima yana magana ba ya kashe ya fito daga motar ya shiga cikin gidan wajan Abba.

BDƘB3P02

Bebi da ya shiga falon Abba a nan ya same su gabaɗaya har su Maryam da Yayyen sa maza da Mama da Mamy.

Yana shiga kafin ya zauna Abba yace, “Kai ka tabbatar da Maryam tayi ciki?.” Bebi ya samu waje ya zauna bai ce komai ba, Abba ya sake cewa, “tambayar ka nake, ka tabbatar tayi ciki?.” Ya ɗaga yace, “eh Abba, da ciki yanzu haka a jikin ta.” Abba ya zabura yayi tsalle ya dira a gaban Maryam, ya tsinke da mari mai zafi, ya sa ƙafa ya mangare ta ta faɗi ƙasa ta kwanta a wajan. Cikin wani irin yanayi yace, “Maryam ni zaki wulaƙanta? Ni zaki tozarta a idanun duniya Maryam?. Cikin uban waye a jikin ki?.”

Adnan yace, “Abba wannan fushin ba shi ya kamata ba a yanzu, abinda ya faru ya riga da ya faru sai dai a kiyaye gaba.” Abba bai kula shi ba yace, “zaki faɗa min uban da ya miki ciki ko san na tsine miki? Cikin uban waye a jikin ki?.” Maryam tana hawaye tace, “Na Kamal ne!.”

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!.” Shine abinda kowa ya faɗa suna tafa hannu Mamy ta ɗora da cewa, “Maryam mijin da yayi miki saki ɗaya, biyu, har uku shi kika komawa har ya miki ciki ba tare da aure ba Maryam? Maryam Kamal dai uban yaran ki guda biyu shi ne ya sake baki cikin na uku?.” Maryam bata amsa ba Sai kuka da take yi Mamy tace, “Maryam kin cuce ni, kin cuci kan ki, kin cuci rayuwar ki da ta ƴaƴan ki” Mamy ta faɗa tana kuka mai taɓa zuciya.

“Kamal!” Abba ya maimaita yana kallon ta cikin tsananin ɓacin rai da tashin hankali, ya sake maimaita sunan yana kallon ta kafin yace, “har gwara ace wani na waje ne daban ya aikata hakan akan ace Kamal ne, Maryam….!” Sai ya kasa magana ya zauna ya dafe kai yana jin wani irin ɓaci a zuciyar sa wanda ko a kan Lubna bai ji hakan ba.

Daddy da yake zaune bai yi magana ba sai lokacin yace, “Maryam meyasa kika biyewa zuciyar ki? Meyasa kika biyewa ruɗin shaiɗan har ya kai ki ya baro ki?. Tsohon mijin ki da yayi miki saki har uku shine kike ɗauke da cikin sa? Haba Maryam ina hankalin ki da ilimin ki yake?.”

Maryam tana kuka sosai muryar ta na rawa tace, “Wallahi Daddy ba da son raina bane, wallahi Daddy ba a son raina hakan ya faru ba.” A fusace Yaya Isma’il ya kai mata mari a fuska ya ce, “kema fyaɗen yayi miki kenan? Sau nawa Adnan yana hana ki magana dashi?, Akan maganar nan har hisba Bebi yaje aka yi muku iyaka dashi, ya kai ƙarar sa har wajan iyayen sa duk dan saboda yana guje miki wannan ranar, amma kika saka ƙafa kika ɓarar ki sake bawa Kamal damar da tafi baya. Da kin ji abinda yake faɗa miki da yanzu hakan bata faru ba, sai da kika zubawa Adnan ƙasa a ido kika yi ciki Maryam.”

Maryam ta sake fashewa da kuka cikin dana sani mara amfani ta kalli Bebi da shima ita yake kallo murya na rawa tace, “na san nayi kuskure babba, amma amfani yayi da wani abu nawa yana tilasta min aikatawa ba dan ina so ba.”

Mamy tace, “ƙarya kike Maryam! Ƙarya kike daman kina niyar aikata hakan, kin kasa rabuwa dashi shiyasa ya samu wannan damar.” Maryam tana kuka sosai ta kasa cewa komai. Abba ya kalle ta cikin wata murya mai nuni da tsantsar ɓacin ran da yake ciki yace, “kin cuce ni Maryam kin gama cutar dani, amma zan ɗauki mataki a kan ki dashi kansa Kamal ɗin.” Mamy tayi caraf tace, “Me Kamal yayi? Me ya aikata…? Ga babbar mai laifi nan ai, shi dama ya samu kuma yayi amfani da damar sa.”

Abba ji yake kamar yayi ta dukan Maryam har sai ta mutu saboda baƙin, ji yake kawai ya shaƙo wuyan ta ya riƙe har sai ya ga ta daina numfashi. Yace, “Cikin shege a gidana, a cikin gıdana aka samo min cikin shege?. Cikin shegen ma mai muni, cikin da aka samar dashi bayan anyi saki har guda uku. Maryam kin cuce ni, kin gama cutar dani.”

Daddy yace, “abinda ya faru dai ya faru, tayi nadama ta gane kuskuren ta na tabbatar baza ta sake aikata abinda tayi ba sai ayi haƙuri kawai komai ya wuce a rungumi ƙaddara wacce ta riga fata.” Abba ya kalli Yayan nasa yace, “kenan ta haifi ɗan shege a gidan nan? Wallahi bazai yu ba sai dai ta bar min gidana taje ta cigaba da zama da Kamal ɗin ta ya haife shi a can, baza’a haifar min cikin shege a gidan nan ba wallahi.”

Ƙanin Abba wanda suke kira da Uncle yace, “haka zaka yi haƙuri ka karɓi ƙaddara. Maryam bata da inda yafi nan, in kace ta tafi sake lalata lamarin ka yi.” Abba yace, “bazai yu ba, ji nake kamar na kashe ta wallahi.” Mama dai kallon Abba kawai take yi zuciyar ta wani tunani kawai take yi daban shiyasa bata ce komai ba.

Shiru kowa yayi sai kukan Maryam da take yi Mamy ma kuka take yi, Mamy ta kalli Maryam tace, “Maryam Allah ya isa ban yafe ba.” Da sauri aka tari numfashin ta Daddy yace, “Haba Jamila! Meye na furta wannan maganar?, Meyasa baza ki karɓi ƙaddara ba?.” Mamy ta miƙe tace, “na fahimci baza ku gane irin abinda nake ji a zuciyata bane shiyasa, amma kar na sake ganin Maryam a inda nake, taje ta koma gidan Kamal su ɗora daga inda suka tsaya, bana son ganin ta daga nan har a tashi duniya” tana faɗar hakan ta fita Maryam ta sake rushewa da kuka.

Abba ya kalli cikin baƙin ciki Maryam yace, “zaki min shiru ko sai na faɗi irin abinda uwar ki ta faɗa? Shegiyar yarinya mai zubin mutanen kirki ashe ta banza ce. A cikin gidana ace an samu wacce tayi cikin shege, kin cuce ni wallahi, kin gama dani, kin zubar min da mutunci a idon duniya.” Maryama ta rufe bakin ta tana jin tashin hankalin da bata taɓa jin irin sa ba a duniya.

Kowa yayi shiru an rasa mai magana a cikin su sai Daddy yace, “ayi haƙuri a karɓi ƙaddara babu wanda ya wuce hakan ta faru a kansa, Allah ya bamu ikon cinyewa. Tabbas Maryam tayi rashin hankali ta kuma biyewa son zuciya, a zahiri mun san duk wanda ya biyewa son zuciya ƙarshen sa yana zama irin na Maryam ko yafi na Maryam muni. Amma tayi nadama a yanzu hakan bazai sake faruwa ba, ko wata ta gani na aikata irin abinda tayi Maryam mai yi mata faɗa ce. Shi kuma Kamal inda bai samu fuska daga wajan ta ba bazai sake koda yi mata magana ba koda a akan yaran su ne. Kamal fuska da dama ya samu shiyasa har aka zo ga wannan gaɓar, da ta riƙe mutuncin ta matsayin ta na ɗiya mace da kallon ta ma wahala zai dinga yi masa balle yayi mata magana. Mace itace take bada ƙofar aikata ɓarna, ko a akan Lubna in ku ka duba in da bata bawa Mujahid dama ba da hakan bazai faru ba. Biyewa Kamal da Maryan tayi shine babban kuskuren da ta tafka a rayuwar ta.”

Yaya Isma’il yace, “abinda Bebi yake guje mata kenan amma ta kasa ganewa” ya kalle ta yace, “sai da lokaci ya ƙure mata ta sannan ta gane kuskuren da tayi wanda bazai gogu ba har abada.”
Chapter 2 · 0% Book details