Sashe 66
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar da Abba ya kwana biyar a a asibiti a ranar ya buɗe ido, a lokacin Bebi yana tsaye a kusa dashi ganin ya buɗe ido sai yayi hamdala ga Allah ya kalle shi yace, "Abba sannu, ya jikin naka?."
Kallon sa Abba yake yi ya mayar da ido ya kulle ya sake buɗewa ya kalle shi amma bai ce komai ba. Jinin sa Bebi yake dubawa ganin har lokacin bai sauka ya sake ɗauko ruwa ya sakawa Abban ba jimawa ya sake yin bacci.
Awa ɗaya ya samu yana bacci ya farka a lokacin ma Bebin ne kawai a zaune a ɗaƙin, ciwon kai an damun Abba amma a haka ya riƙo hannun Bebi yaji zafi sosai ya kalli Bebi idanun sa da suka yi yarrrrr sun juye sun kuma yi ja yace, "kar ka taɓa kuskuren aikata zina a rayuwar ka, in ba haka ba ta zata dinga bibiyar ka har yaran ka da jikokin ka. Ita nake ganina yanzu shiyasa nake baka shawarar ka faɗawa ƴan uwan ka” Abba ya faɗa murya na shaƙewa numfashin sa na ƙoƙarin barin jikin sa.
Gaban sa ya faɗi sosai, ya riƙe hannun Abban yace, "Abba ka daina magana don Allah, ka kwantar da hankalin ka a samu jinin ka ya sauka. Wannan tunanin da ka ke yi shine ya saka jinin ka yaƙi yayi ƙasa, ka yi haƙuri." Abba ya girgiza kai yana runtse idanun sa yace, "illar zina nake gani, kar ka yi wannan kurkuren Adnan. Ka bawa Lubna haƙuri, ka basa Maryam haƙuri duk ni na jawo musu" tarin da yake yi ne yayi yawa harda jini, cikin ihuuu Adnan yayi magana wanda yasa ƴan gidan su da suke waje sun ji, suna zaunen dai ga likitoci biyu sun shiga a guje sai hankalin su ya sake tashi.
Duk yadda aka so ayi wajan ceto ran Abba abin yaci tura, Abba dai rai yayi halin sa a daidai wannan lokacin Alalh ya karɓi kayan sa. Dr da yake duba shi bayan ya tabbatar da rasuwar sa ya kalli Adnan ya sauke ajiyar zuciya yace, "i’m sorry Dr, Allah ya karɓi kayan sa."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!" Ya furta cikin gigicewa tare da zama a kan kuskure ya kulle idanun sa kawai ya fara hawaye. Dr ganin haka sai ya zauna a gefen sa yace, "kayi haƙuri ka daure, in kana hawaye su kuma uwan ka ƴan kenan?, ka yi haƙuri ka yi masa addu’a Allah ya bashi ikon amsa tambayar kabri.” Ya kasa koda motsin kallon Abba yake daga kwance an kulle masa fuska ya tashi ya ƙarasa inda yake ya riƙe hannun sa ya ɗora a fuskar sa yana kuka sosai.
Duk yadda likitan yaso rarrashin Adnan abin yaci tura, yafi mintina ashirin yana kuka kafin ya iya daurewa ya goge idanun sa ya kalli tagar ɗakin ya hamgo ƴan uwan sa dukkan su suna tsaye alamun jiran fitowar su suke. Ya kulle idon sa cikin zafi da raɗaɗin mutuwa ya jingina da bango yana kallon Abba, gani yake kamar wasa ake masa Abba bai rasu ba yana nan da ran sa. Daurewa yayi ya ɗauki waya ya kira Yayan sa yana ɗauka yace, "Yaya Abba ya rasu." Abinda yace kenan ya kashe wayar dan bazai iya fita ba. Yaya yayi ta maza ya daure ya kalle su da kowa shi yake kallo yace, "hayaniya tayi yawa, Bebi yace ku koma gida dukkan ku yanzu ba'a son hayaniya."
Mamy da take kallon yanayin sa tace, "kar ka yi mana ƙarya, ka faɗa mana abinda ya faru fuskar ka ba haka ta nuna ba. Abba ya rasu ne?." Ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe ido a kansu yace, "Allah ya karɓi rayuwar Abba."
Gabaɗaya su suka haɗa baki akayi salati ana fara koke-koke a wajan daƙyar aka lallaɓa su suka tafi gida sunkuma suka taso da gawar Abba.
Bayan anyi sallar la'asar aka yiwa Abban suttura aka tafi kai shi gidan sa na gajiya gaskiya. Gidan da yake jira kowa, gidan da babu mai shigar maka sai dai ka shiga, gidan da abinda ka aikata yake jiran zuwan ka, gidan da mala'ikun Allah ke jiran zuwan ka, gidan da tun kafin kaje masu tarbar ka suna jiran ka, gidan da za'a saka maka ƙasa a saman kanka ta rufe ka, gidan da babu hasken fitili sai hasken aikin ka, gidan da za’a yi maka tambaya akan ubangijin ka, gidan da sai ka amsa wannan tambayar zaka samu haske a cikin sa, gidan da babu fanka balle ac a cikin sa, gidan da babu taga balle kaji iska, gidan da bashi da faɗi balle kayi kwanciyar yadda ka ke so, gidan da alkur'ani ne zai kawo maka ziyara ku yi hirar ka in kana karanta shi, gidan da sallolin ka zasu kawo maka ziyara in aka aikata au da kyau. Ya Allah ka sa mu dace, ka sa mu yi kyakykyawan ƙarshe amin.
Duk wani masoyin su ya tauaysawa iyalan gidan saboda rasa bangon gidan da akayi, mutuwar ta zamar musu tamkar ba a taɓa yi ba duk da Yayan Farida ya taɓa rasuwa amma gidan ya zama kamar ba'a taɓa yi musu mutuwa ba. Har akayi kwana uku da rasuwar Abba kuka suke yi, Daddy ya dawo dashi ake karɓar gaisuwa, mayan mutane suna ta kawo ziyara ba zaka ce gidan rasuwa bane saboda yadda ake cika shi.
Sai da akayi kwana bakwai sannan kowa ya watse babu kowa sai iyalan gidan kawai. Maryam tafi kowa shiga tashin hankalina bayyane saboda tana ganin ta silar ta abba ya bar duniya, kullum a kuka take da tashin hankali ko fitowa bata yi.
A ranar da ya kwana takwas da rasuwa ta suka tara ƴan uwan şu mata da maza aka fara zancen raba gado dan a sauke masa nauyi da wuri, a nan Adnaan yake sanar dasu wasiyyar da yace ya faɗa musu nan da nan waje ya sake dawo ɗanye, mutuwa ta dawo zabuwa fil kamar a lokacin aka yi ta.
A hankali mutuwar ta fara bin jikin su kowa ya fara warewa ana cigaba da harkoki tunda wanda ya rasu dai bazai dawo ba ya tafi kenan. A ranar lahadi da yamma wanda a lokacin satin Abba uku da barin duniya Bebi ya fito daga wajan Mama yaji Lubna tana kiran sunan sa ya tsaya yana kallon ta ta ƙaraso kusa dashi tace, "Yaya daman akwai abinda nake so na faɗa maka."
Ya gyara tsayuwar sa yace, "ina jin ki." Ta sauke ajiyar zuciya tace, "tun kafin rasuwar Abba ake yi min message da wata number amm bana bayar da amsa, shine yay aka kira ni da na ɗauka sai naji wanda yake min wayar na san shi." Bebi ya kalle ta yace, "waye?."
"Yaya Mujahid ne!."
BDƘB3P41
Da mamaki yake kallon Lubna yace, "Mujahid fa kika ce? Shine yake yi miki waya?." Lubna ta ɗaga kai tace, "shine Yaya, da ake yi min messages ban san shi bane zai da ya kira ni sannan na gane muryar sa." Bebi ya girgiza kai ya kalli wani wajan daban ya sake kallon ta yace, "kin tabbatar shine yake yi miki waya?."
"Shine wallahi" ta kalli wayar ta sannan tace, "kaga ma number ce take kirana."
"Ɗauki ki saka naji" ya faɗa yana kallon ta. Ta ɗauki wayar ta saka a speaker daga can ɓangaren yace, "Lubna don Allah ki saurare ni, magana nake so mu yi dake ta fahimta, Wallahi nayi nadamar abinda na yi..." Kit ya datse wayar ya miƙa mata wayar ya ce, "Kar ki sake ɗauka in ya kira ki, sannan duk inda zaki je ki tabbatar na dani dan zai fara bibiyar ki ne, in kika ganshi a wani waje ki sanar dani."
Lubna ta amsa da to ta juya ta koma ciki shi kuma ya shiga mota ya tafi gida.
Yana shiga ya tarar da Manal ta yi girki mai kyau tana yiwa abincin hoto kamar yadda ta saba yi. Ganin sa sai tace, "Partner barka da zuwa." Ya kalle ta ya ce, "barkan ki my chef." Tayi dariya ta rufe abincin tana kallon ta ƙaraso inda yake tace, "wai meye sirrin ne?, naga kana yin kyau kwana biyu.” Yayi ƴar dariya ya ce, "wanda ya rasa mahaifin sa ina shi ina yin kyau Manal?, kar ki manta Abba bai yi wata ɗaya da rasuwa ba.”
“Na sani, kuma in sha Allah Abba yana aljanna.” Ya sauke numfashi yace, “Allah ya tabbatar da hakan.”
Amin. Amma ni dai naga kayi kyau sosai." Ya zauna yana ɗaukar Ayan da yake cikin gadon sa yace, "kema kin yi kyau din ai."
Ta zauna a kusa dashi tace, "na kawo maka abinci yanzu?." Ya girgiza kai yace, "bara mu yi magriba naci, yanzu bana jin yunwa." Kallon Ayan yake yi yana wasa da kumatun sa ta kalle shi cikin tausayawa.
Rasuwar Abba ta taɓa shi sosai, tun a farkon rasuwar zaka tabbatar da rashin Abba ya shige shi, haka zai shiga ɗaki ya kulle kansa yayi kuka ya gode Allah sannan ya fito. Addu’a da sadaka kullum cikin yiwa Abba yake yi, daga rasuwar Abba zuwa yanzu bohol biyar ya saka aka haƙa a ƙauyukan da basu da ruwa da niyar Allah ya kai ladan kabarin Abba. Dukkan su ƴan gidan sun yi haɗin guiwa ana gina babbar islamiyya da za’a dinga yin karatu da komai kyauta da niyar Allah ya kaiwa Abba ladan kabarin sa. Adnan yana jin ɗacin rasa mahaifin sa a ko yaushe, daga baya ne abin ya lafa har ma yake iya dannewa.
A tausashe tace, "Partner na so da kai Ayan yake kama ba dani ba." Ya kalle ta ya ce, "da yayi kama dake baki ga yadda yake da farin jini ba? da dani yake kama baza’a dinga ɗaukar sa ba.” Ta turo baki tace, "ni kai nake so yayi kama dashi."