← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 84

Sashe 23

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal tace, "na san ai wajan wannan matar zaka yi order shiyasa nayi." Yayi dariya yana kallon ta yace, "kishi ki ke da ita dan tana siyar mana da abinci mai daɗi?."
"Kishi sosai ma kuwa, ta ya zaka dinga yabon abincin ta a gabana?."
Yayi murmushi yace, "yau Babyn mu ya motsa kuwa? Ban ji kin kira ni kina bani labari ba." Manal tace, "yau ai dambe yake da hanjin cikina, Allah yasa ba dan china zamu haifo ba dan wallahi dambe yake yi yau."

"Amma shine ko a bani labari?." Manal tayi dariya ta kalli Mubeena tace, "Yaya Mubeena ce ta ɗauke min hankali daga kiran na ka." Kallon inda take kallo yayi dan shi wallahi shi bai ganta ba sai yanzu, ya ce, "A'a Yaya Mubeena, Sannu da zuwa." Mubeena haushi take ji in yace Yayan nan, amma tunda yaga bata so yake faɗa shiyasa take amsawa kawai. Murmushi tayi tace, "Yauwa, ina wuni?."
"Lafiya lau, ya Mama?."
"Tana nan lafiya, tana gaishe ku."

"Muna amsawa." Manal tace, "kana ji, kuɗin auren Yaya Mubeena za'a kawo, Mun ksa shan shagalin biki." Mubeena ta kalle ta tace, "ke wai..." sai kuma tayi shiru bata faɗi abinda zata ce ba. Bebi yayi murmushi yace, "Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin."

Manal ta amsa da amin kafin Mubeena ta tashi tace, "ke ni zan wuce." Manal tace, "don Allah tsaya na baki saƙon Mama" ta faɗa tana shiga kitchen ba jimawa ta fito da flaks biyu na abinci tace, "Yaya don Allah ki kai mata."

Mubeena ta harare ta tace, "wai ke yar aiken kice ni?." Manal tace, "Allah nace, kuma Mama za'a bawa."
"Kawai sai na fita da flaks ɗin abinci, salon ace nazo gidan ɗanwata na tafi da abinci." Manal tace, "to meye? Ai ba gidan ƙanwar wani bace ƙanwar ki ce."

Mubeena ta karɓa tana cewa, "samun abin bawa ma a layin nan naku ko wahala." Bebi dai ya basu waje baya wajan, abinda Mubeena take faɗa yaji lokacim ya fito yace, "muje na kai ki" ya kalli Manal yace, "daman zan koma asibiti sai zuwa seven zan dawo, na zo naga ya kike ne kawai saboda baki yi min waya bw." Idon ta ya cikl da hawaye ganin hakan sai ya ƙarasa inda take yace, "don Allah kar ki min kuka, yanzu fa biyar da rabi zuwa nan da bakwai zan dawo ai bazan jima ba."

Ta kawar da kai tace, "a dawo lafiya." Ya girgiza kai ya wuce Mubeena ta harare ta tace, "banza shagwaɓaɓɓiya" ta faɗa tana fita.

A mota ta samu Bebi ta shiga gaba ya ja motar suka fita. Babu mai magana a cikin su sai sautin radio da yake tashi a motar kaɗan-kaɗan, bai ce komai ba itama bata ce komai ba.

Wayar Mubeena ce tayi ƙara ganin sunan Manal sai ta ɗauka tace, "ya akayi?." Manal tace, "kinga na manta da man shanun miyar tuwon, don Allah ki dawo ki karɓa."
"Kan bala'i! Ni zan dawo ma na karɓar miki man shanu? Lallai Manal wallahi kin jima da gama raina ni."
"Kin san Mama tana san man shanu a tuwo, don Allah ku zo ki karɓar mata na san partner zai dawo."
"Baki ma da aikin yi ne, shagwaɓaɓɓiyar banza kawai. Gwara dama Allah ya raba mu da kullum bakin ki a fashe yake" ta faɗa tana kashe wayar tana cewa, "gabaɗaya Mama ce ta sangarta ki, komai kuka kamar wata yarinya ƙarama."

Bebi yana jin ta yayi murmushi kawai ya kalli Mubeena sai tayi shiru tunawa fa da mijin Manal ɗin take tare sai tace, "ina ta yiwa matar ka faɗa ko? Naga kana kallona." Baice mata komai itama tayi shiru har suka zo ƙofar gida ya faka motar tace, "to na gode sosai." Bebi yace, "in babu damuwa zan iya tambayar ki?."
"Ina jin ka."

Bebi yace, "kin taɓa sanin mahaifina? Ina nufin kun taɓa haɗuwa dashi kafin ki san shine ya haife ni?." Gaban ta ya faɗi sosai ta danne bata nuna ba ta kalli Bebi tace, "meyasa ka ke tambayata?." Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, "yanayin fuskar ki na yanzu kawai ya nuna min kamar abinda na tambaya amsa ta itace eh."

Mubeena ta girgiza kai tace, "mamaki abinda kace ya bani ne, ban taɓa ganin sa sai a asibiti lokacin da muka je da Mama amma kafin nan ban san shi ba, Sai dai in shi Abban ne ya sanni wani wajan amma ni ban san shi ba." Kallon fuskar ta Bebi yake yi yana karantar yanayin ta sai dai bata bashi damar da zai gano wani abun ba a tare da ita.

Bebi yace, "to shikenan na gode sosai." Mubeena tace, "babu komai, a gaishe da mutanen gidan" ta faɗa tana fita daga motar ta wuce gida shi kuma yana motar yana tunani. Wacece Mubeenan da abokin Abban sa yaji yana cewa itace silar damuwar sa?, Abinda ya saka ya zata wannan Mubeena ce saboda kallon da tayi masa a asibiti yayi tunanin akwai wani abun, amma gashi tace ba ita bace, to in ba ita bace wacece? In kuma ita ɗin ce fa?.

BDƘB3P13

Mubeena kuwa tana tsaye ya wuce a mota dan a soron ta tsaya tana kallon sa, ta sauke numfashi bayan ya wuce tace, "meyasa ya tambaye ni? Ya taɓa ganina da mahaifin sa kenan ko kuma hasashe yake?. To me zai saka ya hasaso ni haka kawai ina matsayin Yayar matar sa?."

Mubeena ta sauke ajiyar zuciya tace, "Tabbas yaji wani abu game dani shiyasa yake so ya tabbatar, amma me yaji a kaina? Me aka faɗa masa?." Ya dafe kanta tace, "ya Allah kasa kar ya san gaskiyar lamarin nan, sanin gaskiyar tonuwar asiri na ce da ma mahaifin sa gabaɗaya. Allah yasa maganar ta tsaya iya haka." Sai da ta daidai ta nutsuwar ta sannan ta shiga ciki wajan Mama.

Shi kuwa asibitin ya wuce kamar yadda ya cewa Manal sai da akayi sallar i'sha sannan ya fito ya tafi gidan su. Wajan Abba ya shiga ya same shi a zaune yana kallon labarai ya zauna a ƙasa yace, "Abba barka da dare." Abba ya kalle shi yace, "har an dawo ko za'a tafi?."
"Na dawo yau bazan fita da daddare ba."
"To Allah ya sa albarka."

Bebi ya amsa da amin kafin ya kalli mahaifin nasa da ya rame ya koma wani iri kamar ba shi ba ya ce, "Abba jiya naji Alhaji Magaji yana yi maka wata magana, duk da bata shafe ni ba amma indai itace silar damuwar ka sai mu yi maganin ta." Gaban Abba ya faɗi sosai ya tashi zaune sosai yana kallon sa ya ce, "ne kaji yace?." Bebi ya ce, "Naji yana cewa yanzu akan ka rasa Mubeena ka koma haka? Me zai hana baza ka nemi auren ta ba ai zata amince. Abinda naji ya ce kenan, shine nake so na tabbatar da hakan in da dama, in har da gaske Abba itace silar damuwar ka babu laifi in ka aure ta ɗim."

Abba kawai kallon sa yake yi amma zuciyar sa rawa take saboda tashin hankali da fargaba, shirun da Bebi ya ji ne ya saka shi ya kalli Abba suka haɗa ido sai Abba ya ce, "to wacece Mubeenan? A ina take?." Bebi ya ce, "shine ban sani ba nazo na tambaye ka, in dai itace silar komawar ka haka Abba gwara ka aure ta yafi." Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Abba yayi cikin jin daɗi ya ce, "wannan tsohon labari ne Bebi, tsokana ce kawai dake tsakanina dashi amma ba maganar yanzu bace ba. Wannan maganar zata kai shekara goma da suka wuce, a wancan lokacin na ɗan yi ciwo ne akan yarinyar, wannan dalilin ya saka ko ya ya nace bani da lafiya sai ya dinga tsokana ta da sunan ta."

Bebi yace, "to Abba meye yake damun ka? Ka rasa nutuswar ka gabaɗaya ka koma kamar ba kai ba, ko fita baka yi ko yaushe kana gida. Kuma naga maganar Maman su Manal ta wuce, komai ya warware kowa ya cigaba da harokin sa. Abba me yake faruwa wanda mu bamu san da shi ba?."

Abba yayi murmushi ya ce, "A baya in ina fita ai bakwa so Bebi."
"Abba ka tafi kayi kwanaki ba tare da iyayen mu ba shine abinda ya saka muke magana bawai fitar taka ce bama so ba. Zaman gida ai ba na ka bane sai dai lalura, wancan lokacin ma kwanakin da kake yi baka gida ne yake saka mu mgana." Abba ya sauke numfashi ya ce, "Bebi fitar tawa bata da amfani, kunyar kaina nake ji da kuma kunyar mutanen gari har daku kan ku."

Bebi ya kalli mahaifin nasa yaga ya kulle ido ya buɗe ya ce, "ni kaɗai na san abinda yake zuciyata, baza ka fahimci abinda yake damuna ba kawai ka cigaba da yi min addu'a, Allah ya yafe min laifukan da na aikata ya bani lafiya ya kuma sanya min nutsuwa a zuciyata, in kuma babu rabon samu ya sa mu cika da imani." Bebi ya ce, "Amin Abba, amma wannan damuwar zata iya saka maka babban ciwo, ya kamata ka rage ta ko ka sanar damu damuwar ka."

Abba ya girgiza kai ya ce, "zan rage saka damuwar Bebi, zan rage in sha Allah" ya faɗa yana kulle idon sa Allah kaɗai ya san abinda yake damun sa. Bebi dole ya taso jiki a sanyaye ya fito ya shiga wajan Mama.

Yadda Mama ta gan shi jiki a snayaye sai ta bishi da kallo tace, "ya akayi?." Yace, "Mummy Abba ne, me yake damun Abba ne har haka? Ya rame sosai ko yaushe cikin tunani yake. Tunda maganar nan da mahaifiyar su Manal ta bayyana shikenan ya koma haka, meye kuma yake faruwa bayan abinda ya faɗa mana?." Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "Nima ban sani ba, nayi-nayi ya faɗa min amma ya ƙi."
"Don Allah Mummy ki je yanzu ko zai faɗa miki, na shiga damuwa a akan yanayin nan na Abba."
Chapter 23 · 0% Book details