Sashe 12
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A wannan lokacin muka sake komawa Jalingo kamar yadda muka saba gidan ne masaukin mu, a wannan zuwan mun tarar da tashin hankalin da ya fi na zuwan baya, domin mun tarar da Allah ya yiwa Alhaji rasuwa. Mutuwar sa ta jijjiga mu ta taɓa zuciyar mu sosai, muka zauma muka yiwa iyalan gidan gaisuwa suka amsa dan mun saba dasu sosai." Abba ya kalle su ya sake gyara zama yace, "mun kwashe kwanaki sosai kafin mu sake komawa garin dan albarkar da muke samowa a garin ya saka muke komawa akai akai. Lokacin da muka goma bayan rasuwar Alhaji nace baza mu je gidan sa ba saboda babu ransa wajan wa zamu je?. Ali sai yace ko dan kyautatawar sa gare mu yana da kyau mu je mu gaisa da mutanen gidan, jin abinda yace sai na gamsu muka je gidan."
"A cikin kwanakin sun raba gado sun bata nata duk da lokacin bata mallaki hankalin kanta ba, dan baza wuce shekaru sha uku zuwa sha huɗu ba. Wannan labari da Ali yaji sai yazo ya same ni yace shi dai yana son auren ta." Abba ya sake cewa, "da farko naƙi bashi goyan baya amma da ya dinga tsara ni, yana faɗa min maganar da zan tausaya mata a zuciyata saboda rashin iyayen da bata dashi da yadda basa sonta sai na amince. Muka je aka karɓo auren Zahra a ranar da muka je a ranar aka bamu auren ta ba tare da bincike ba, ana ɗaura aure suka tattarawa Ali dukiyar ta suka ce ya tafi da ita."
"A washe garin ranar ya dawo Zaria ya bar ni a can saboda na taho da kayan da muka siya shi kuma ya taho tare da matar sa. Sai da na gama komai sannan na wuce Kano kai tsaye ban shiga Zaria ba dan ina so nazo gida dan a kai abinda aka siyo kasuwa. Bayan na dawo yake sanar dani ya samu gidan haya ya saka ta a ciki nazo na ganta mu gaisa."
"Nima kuwa washe gari na taso zuwa Zaria ya tare ni a tasha muka je gidan ya saka ta a ciki. Gidan haya ne mai mutum biyu ma'ana bashi kaɗai bane a gidan akwai wasu ƴan hayar, muka gaisa da ita a wannan lokaci ta amsa da fara'a dan ta shaida ni mijin ta ya faɗa mata waye ni a wajan sa da sauran bayanai. A gidan na kwana a wani shago da yake wajan gidan gari na dawo Kano a zuciya Ina jin kamar bamu kyauta mata ba."
Abba ya kulle ido ya buɗe kafin ya ce, "daga wannan lokacin sai Ali ya daina sana'ar da muje yi, in na same shi da maganar sai ya fara yi min hanya-hanya, yau yace bashi da lafiya gobe yace min ya gaji da sauran su. Daga nan sai na watsar dashi indai akan business ne amma nuna waya dashi ta landline sosai har nace yaushe zai zo gidana don a lokacin an yi haihuwar Adnan. Bai zo ba nima ban je ba, na cigaba da harkokina har Allah ya kaini Zaria lokacin kusan shekara ɗaya da rabi da auren su. A nan naje na tarar da Zahra tana da cikin ƴar ta fari."
"Bayan ta haihu aka saka mata sunan Maman ta ya cigaba da rainon ta cikin so da ƙauna har aka sake samun cikin matar ka Adnan!" Ya faɗa yana nuna Adnan da yatsan sa. Bebi ya kalle shi Abba ya kuma cewa, "lokacin ina yawan zuwa Abuja a kai a kai, to na kan tsaya a Zaria har na kwana a wajan sa, a haka na san matar sa ta farko duk da mun taɓa gaisawa da ita sau ɗaya, abinda na sani na san bashi da yara dan ya faɗa min ƴaƴa uku ya haifa duk sun rasu. Muna gaisawa da matar sa in naje sosai duk da bata san da matar sa biyu ba. Na yi masa magana me yasa bai faɗa mata ba yace haka yake so baya zo ko wacce ta san da ƴar uwar ta, na dinga faɗa akan me zai yi haka so yake yaran sa su taso basu san juna ba yace eh haka yake so. A lokacin yana da ɗa namiji guda ɗaya, sannan ya faɗa min ya taɓa yin aure a Kano amma basu jima da matar ba suka rabu, itama matar sa ta farko bata san da ita ba. Nayi fushi na tafi bai sake nemana ba nima ban kuma neman sa ba a wannan lokacin."
"Sai da ya gaji da kansa ya neme ni muka shirya, yace min kuma ai ya faɗawa matar tasa har ta amince ashe ƙarya yake yi bai faɗa ba. A wannan lokacin aka haifi ƴar sa ta biyu matar Adnan kenwn, aka saka mata sunan babar ta wacce yake kiran ta da Fatima. Daga wannan lokacin Ali ya fars bayyanar da ƙudurin sa akan auren Zahra."
"Tatttara dukiyar ta kawai yake yi yana siyar da na Jalingo yana siya a wani wajan a hankali ba tare da ya sani ba. Jasancewar ta mai ƙarancin shekara dan har ta haifi Manal bana tunanin tayi shekara ashirin ba, ta yarda dashi sosai ɗari bisa ɗari ta tamƙa masa duk abinda ta gada wajan iyayen ta a hannun sa, dukiya ce mai yawa sosai dan na faɗa muku waye mahaifin ta. Samun wannan dama a hannu sai Ali yayi amfani da ita wajan tattara duk wata dukiyar ta yana sakawa a aljihun sa. "
"A haka ya gama siyar da komai bai barta da komai ba ya tattara komai ya gama siyarwa a hankali yana cigaba da haɗa plan ɗin yadda zai ɗauki uwar gidan sa su gudu. A lokacin muka haɗu dashi yake faɗa min shi zai kwashe kuɗin ta ya gudu ne in ina so zamu raba. Wallahil azim na ji tausayin ta sosai saboda bata da kowa sai shi, ina zata je in ya rabu da ita ga yara guda biyu..?. Amma ban nuna masa ba shaiɗan ya shiga raina nima naji ina da sha'awar cin wani abu a cikin kuɗin nata, tunawa da irin dukiyar da aka bar mata naji nima zan zo na samu kasona. Ya dinga dariya muka tafa muka gama tsara yadda komai zai faru, a nan yake faɗar daman shi dan kuɗin ta ya aure ta."
Abba yayi shiru yana jin ɗacin abinda ya aikata a zuciyar sa, dana sani yake yi sosai dan da bai bashi goyan baya ba da wataƙila hakan bai faru ba.
Abba yace, "ina ta jiran sa yace min ga kuɗi shiru, sai gashi a Kano yazo ya same ni da wani kuɗin da basu taka kara sun karya ba nace ai ni bazan karɓa ba. A taƙaice a nan muka yi rabuwar babu daɗi dashi ya kama gaban sa na kama gabana saboda bai bani adadin abinda muka yi dashi zai bani ba."
"Haka kawai naji a zuciyata ina so naje gidan sa na faɗa masa gaskiya akan kar ya yi mata abinda yace in ba haka ba za'a cutar da ita. Ban tashi zuwa ba sai bayan sati uku da wannan tunanin nawa, ban kuma sake neman sa ba naje kai tsaye ne. Ina zuwa na tarar da ita ana korar ta daga gidan haya ga yara guda biyu tana kuka saboda bata da kuɗi, ashe ya ɗauke matar sa da kuɗin ya bar garin. Da hanzari naje nayi magana dasu na biya kuɗin take suka barta naje zan yi magana da ita a nan ta nuna min bakin mu ɗaya da abokina dan haka baza ta saurare ni ba naje duk abinda muka yi Allah ya isa. Ni kuma wannan haushin nunawa da tayi bakin mu ɗaya har tana faɗa min duk abinda yazo bakin ta sai raina ya ɓaci, na dinga faɗa mata magana sosai tana kuka na tafi na barta a wannan yanayi ba tare da na duba yaran da suke tare da ita ba, haushin mijin ta da ita kanta ya saka ban saurare ta ba."
Abba ya kalle su yace, "tun daga wannan lokaci ban sake ganin ta bata sake ganina ba ba sai asibiti, nayi mamaki da ta gane ni dan shekarun da yawa sosai, girma ya cimmana furfura ta zagaye mana fuska, amma da yake ba'a mantawa da sharri ko alkhairi tana ganina ta gane ni nima na gane ta. Abinda nayi na san nayi kuskure na biyewa son zuciya, kuma har ga Allah ban ci ko naira biyar a dukiyar ta ba, ban kuma sake ganin Ali ba, dan bayan rabuwar mu na watsar da waccan sana'ar dan a lokacin shuganan ƙasa ya bani appointment na zama minister. Ban san ya akayi ta dawo Kano har tayi aure ta raini yaran ta ba."
Mama da take jin sa har ya kai ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya tace, "Yanzu dai mun tabbatar da ba kai ne mahaifin Manal ba abokin kane wanda ku ka so kwashe dukiyar ta tare dashi ashe cuta ce ta ɗau cuta, yanzu Ina abokin naka ya ke?."
Abba yace, "baki ji me nace bane?." Mama ta ɗan taɓe baki tace, "ban ga laifin ta da tace baza ta bawa jinin ka auren ƴarta ba, bata sani ba ko wataƙila shima irin halin ku ne dashi da ya aure ta ya kwashe abinda ta tara." Bebi ne ya kalle ta yace, "Haba Mama!." Mama ta sauke kai dan wallahi ita labarin ma bai wani shige ta ba, gani take yi akwai abinda ya ɓoye a cikin labarin.
Bebi yace, "yanzu Abba ina mahaifin nasu yake?." Abba yace, "wallahi ban sani ba. Yana da rai ko bashi da rai Allah ne kawai ya sani. Asalin sa dai ɗan garin katsina ne.” Yaya Isma'il ya girgiza kai cikin girmama labarin da aka bashi yace, "Kenan babar su Manal ƴar Muhammad Jalingo ce?." Abba ya ɗaga kai yace, "ƙwarai kuwa, ta gaji dukiya wacce ake kira duniya tun a wancan lokacin. In Ali yana da rai duk kuɗin da yayi a yanzu da dukiyar ta ya yi shi wallahi, Tabbas da naci wani abu a ciki nima da dukiyar da nake da ita a yanzu ta ta ce ba tawa ba."