← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 84

Sashe 26

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya murmusa kaɗan ya ce, "to Bebi." Daga nan bai kuma cewa komai ba, Bebi ya tashi ya ɗauko abin gwada jiki ya auna jinin Abban yaga ya sauka amma dai ba yadda ake so ba, a lokacin su Mama suka shigo ganin ta da abinci Bebi ya saka aka zubawa Abban abinci yaci sannan ya sake saka masa ruwa bacci ya sake ɗauke shi.

Yana fitowar daga ɗakin da Yaya Isma'il ya haɗu yaja Bebi gefe suka ɗan yi tafiya kaɗan kafin ya ce, "faɗa min gaskiya abinda yake damun Abba Adnan." Bebi ya ce, "wallahi Yaya damuwa ce da rashin bacci dama rashin abinci shine yake damun sa, amma yanzu jikin nasa ya ɗan sauka kaɗan na sake saka masa ruwa in sha Allah in ya farka daga baccin jinin zai sake yin ƙasa, saboda akwai rashin bacci a lamarin sa in yayi bacci sosai wani abun zai ragu sosai."

Yaya ya ce, "bayan nan babu komai?."
"Babu komai, in akwai bazan ɓoye maka ba."
"To Allah ya bashi lafiya."
"Amin ya Allah. Ya maganar company? Yaya Bilal  yaje?."
"Yaje, yana can ma zai yi waya zai sanar damu halin da ake ciki in sha Allah." Bebi ya amsa kafin ya bar wajan ya cigaba da aikin sa.

Sai sha ɗaya na safe ya kira Manal ta ɗauka kafin yayi magana tace, "Partner ina kwana."
"Kin tashi lafiya? Ya kike?, ya kuma Baby?."
"Sai kace ya me sunan ka." Yayi murmushi ya ce, "to ya me sunana?."
"Yana nan sai naushi na yake a ciki."
"Lafiya lau yake kenan, kin ci abinci?."

Manal tace, "uhum na sha tea sannan kuma na ci salad ɗin da na haɗa jiya."
"Kin tabbatar kin ƙoshi?."
"Sosai ma, ya jikin Abba?."
"Jikin sa da sauƙi sosai."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin. yanzu babu wani abun ko?." Manal tace, "babu komai, sai dai ina so zan zo asibitin na duba Abba."

Bebi yace, "to babu damuwa, sai dai bana son ki ce zaki yi driving. Abinda zai faru zan turo azo a ɗauke ki kawai, kin gama abinda zaki yi?." Manal tace, "na kusa, nan da kamar minti talatin."
"Okay, in kin gama sai ki faɗa min" ta amsa da to ya kashe wayar ya cigaba da abinda yake yi.

Manal bata zo ba sai da tayi abinci shinkafa da miyar kaji da lafiyayyen salad, ta saka a basket mai kyau tayi masa waya tace a zo a ɗauke ta sannan ta shiga wanka ta shirya cikin doguwar riga waacce zata sake a ciki suka tafi.

Lokacin da taje asibitin duk ƴan gidan suna nan  har sirikai matar Yaya Bilal da Yaya Isma'il suna nan. Itama da ta je ta shiga cikin su aka zauna bayan taje ta ga yanayin jikin Abban. Hira suke yi da Mimi sama-sama dan zaman ma ya fara isar ta ita kar ta bar wajen aga kamar tayi rashin kunya.

Mamy ce ta lura da gaji da zaman  tace, "Manal kin gaji da zaman nan, ina Bebi kije office ɗin sa ki huta." Maryam tace, "gaskiya ki je ki samu ki zauna ki miƙe ƙafar ki ko ki kwanta, kin gaji da zaman naga alama. Mimi ki raka ta ai kun san office ɗin."

Tashi suka yi suka tafi ita da Mimi, lokacin da suka shiga office ɗin babu kowa a ciki.Manal ta zauna akan doguwar kujera ta kwanta tana yatsine fuska tace, "wallahi Mimi Mamy ta taimake ni, badan tace ba bazan iya tashi ba." Mimi tace, "sai ki cuci kan ki kuma?."
"Kunyar su nake ji fa ni, ko Mummy ban so ta ganni ba wallahi."
"Lallai kina da aiki, haka Mama tace min ai tunda cikin ki ya fito kika daina zuwa gaishe ta sai dai a waya."
"Baza ki gane bane."  Mimi tayi dariya kawai dan ita kam sha'awar Manal ɗin take ita ko cikin ma bata dashi.

Zama tayi tace, "bara na taya ki na matsa ƙafar nasan ta yi miki tsami" ta faɗa tana zama a gefen ta tana matsa mata ƙafar ta suna hira. Bebi ne ya shigo yana amsa waya ya kalle su sai ya tsaya ba tare da ya zauna ba, bayan ya gama wayar ya ƙaraso yana kallon Manal da Mimin ya ce, "lafiya take?." Mimi tace, "lafiya lau take, ta gaji da zama ne shine Mamy tace tazo nan ta huta." Kallon sa tayi ta tashi zaune ya ce, "ko zaki koma gida?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "to in kin zauna a nan ɗin me zaki yi? Ko zaki je gidan Mama to?." Ta noƙe kafaɗa alamun a'a tana shagwaɓe fuska harda turo masa baki tace, "ni a nan zan zauna, kawai sai naje wajan Mama bayan ga Abba baya da lafiya?."

"To zaman ki shine zai bashi lafiya?."
"Indai a'a zan zauna a nan." Ya zuba nata ido na wani lokaci bai ce komai ba, itama kallon sa take kafin ya janye idon sa ya kalli Mimi da take kallon su tana murmushi ya sake kallon Manal ɗin da take kallon sa kafin yayi magana tace, "Yunwa nake ji."

Yayi ƙaramin tsaki ya ce, "Manal kina da damuwa, damuwar ki yawa ce da ita. Shiyasa nace kije gidan ai  kika ce ke a'a, yanzu ina zan samu abincin da zaki ci?." Jin ya fara magana cikin faɗa sai tayi shiru bata ce komai ba. Yayi ƙaramin tsaki ya fita.

Mimi tayi dariya tace, "Yaya Bebi masifa, ashe har ke bai bari ba."
"Yana nan yana yi, wani lokacin in yana faɗa kamar ni da shi abokan gaba ne. Ni har tunani nake ya akayi ma na aure shi" Manal ta faɗa tana taɓe baki. Suka yi dariya a tare tace, "ai wallahi duk masifar babu inda zanje, kawai naje gida na zauna ni kaɗai ba gwara nan ɗin ba."

Bai jima ba ya dawo ya kalle ta ya ce, "kina ji? Dole ma kije gida ni ban san wanne irin abinci zan kawo miki da ya dace dake a nan ba, ke kin san a wannan yanayin ba a so blood sugar ɗin ki ya hau." Manal ta sauke numfashi tace, "to shikenan ba sai na ci ba" ta faɗa cikin kalar tausayi.
"Ke wai gidan ne baza ki tafi ba? Biki ake yi a nan ɗin da ki ke son zama?" Ya faɗa yana kallon ta. Manal ta turo baki tace, "to in naje ni kaɗai fa zan zauna."

Mimi tayi dariya tace, "bara naje a cikin wanda ta kawo naga ai basmati ce shinkafar kuma akwai salad sai taci" ta faɗa tana tashi ta fita. Ya harari Manal ta murgaɗa masa baki tare da juya idanun ta, ya girgiza kai ya wuce inda yake zama yana duba abinda ya kawo shi office ɗim tun farko. Sai da yaga Mimi ta kawo abincin ya tabbatar yayi daidai da Manal sannan ya fita.
Har yamma Manal tana nan tunda ya fita ma shi bata sake ganin sa ba, har ta gaji da zaman ta fito cikin mutane duk da ba hira ake yi ba.

Abba ko da ya tashi daga baccin Bebi ya ce a kira masa a lokacin ne taga ya wuce ta ya shiga inda Abban yake. Bayan ya shiga Abba ya kalle shi ya ce, "Adnan na samu lafiya a gida nake so na kwana yau." Bebi ya ce, "Abba a nan zaka fi samun hutu sama da gida, nan ya kamata ka zauna na kwana uku zaka fi warwarewa in sha Allah."
"A'a Adnan, gida nake so na koma kuma zan koma ɗin."

Bebi ya kalli Yayan su da yake tsaye yac e, "Yaya ka saka baki ko gobe Abba ya bari sai ya tafi, a nan zai fi nustuwa saboda zai fi samun kulawa." Yaya ya ce, "don Allah Abba kayi haƙuri zuwa goben." Jin abinda yace sai  kawai yayi shiru bai ce komai ba.  A ranar an karɓi baƙuncin baƙi maza dan zuwa duba Bbba, har dare zuwa ake wannan yazo ya tafi wannan yazo ya tafi wasu sun san su wasu kuma basu san su ba.

Ƙarfe tara na dare Mama ta kira Adanan gefe tace, "kai wai wanne iri ne, kana da mai tsohon ciki ka zaunar da ita har dare baza ka kai ta gida ba?." Ya kalli Manal da take zaune alamun gajiya ya gama bayyana a tare da ita ya ce, "wallahi Mummy tun azahar nace zan saka a mayar da ita amma taƙi ji."
"Yanzu sai kazo ka wuce ku tafi dare yayi, Isma'il yace yau a nan zai kwana." Da to kawai ya amsa ya kira Manal yace mata zasu tafi, sai da ya shiga wajan Abba kafin ya fito su tafi gida.

Kwanan Abba biyu a asibitin ya matsa sai ya tafi, a cikin kwanaki biyu labarin gobarar company sa ta baza ko ina kowa yaji labari, anyi asarar dukiya ba kaɗan ba, dan kayan amfani na ciki duk sun ƙone wasu an samu ragowa wasu kuma babu ma ragowar sun zama toka. Ana ta taya shi da addu'a Allah ya mayar da alkhairi shi kuma a ɓangaren sa a wani abun daban yake kallon lamarin.

Manal na gida a zaune da yamma tana waya da Mama tana cewa, "Amma Mama ya kamata ace kun zo kun duba Abban, har a asibiti fa ya kwanta kuma kince komai ya wuce." Daga can ɓangaren Mama tace, "Manal ai baki fini sanin ya kamata ba ko?."
"Eh Mama" ta faɗa a hankali dan kar Maman tayi mata faɗa.

Mama tace, "zamu zo in sha Allah, in kin je kice ina yi masa Allah yaƙara lafiya, shima Adnan ɗin kice ina yi masa ya mai jiki." A lokacin ya shigo falonsai ta kalle shi tace, "Shikenan ma gashi ya shigo" ta faɗa tana bashi wayar tace, "Ga mama."

Karɓa yayi suka gaisa bayan sun gama ya bawa Manal wayar ya ce, "Ashe Maman babu lafiya baki faɗa min ba?." Manal tace, "cewa tayi basai mun zo ba tunda Abba ma babu lafiya."
"Rashin lafiya ai rashin lafiya ce, da kin sani kin faɗa min sai muje mu duba ta."
Chapter 26 · 0% Book details